← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 88

Sashe 62

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na cewa Jalilah class mate dina, “ki wuce hostel kawai, akwai inda zan je" tace toh sai kin dawo. Har ta fara tafiya sai kuma ta juyo tace “naji wani rumor yana yawo a cikin class dinmu, wai zaki yi aure?" na dan jijjiga mata kai ina murmushi, tace “amma gaskiya ban ji dadi da baki fada min ba" nace “sorry, auren ne kawai za a daura kin gane? Shi yasa ma ban wani yi shela ba saboda ina makaranta ma za a daura" ta matso da bakinta saitin kunnena cikin rada, “amma naji ana cewa wai wani lecturer ne anan zaki aura, da gaske ne??" na zaro ido cike da mamakin yadda aka yi zancen ya isa garesu, koda yake dama an ce zancen duniya baya buya. Nace mata “rumors ne kawai amma ba haka bane" tace “idan ma hakan ne meye na wa ko na mutane a ciki? Allah ya baku zaman lafiya mai daurewa" na mata murmushi ina kokarin boye dariyar data ciwo ni don nasan magana ce ta fada min, nace Ameen. Ta juya ta tafi abinta. Na duba agogon hannuna naga karfe sha daya ne da rabi lokacin, da sauri na dauki hanyar da zata kaini ofishin Abbu don nasan yana can yana jira na, ranar juma'ah ce ga masallaci ga kuma cinkoson ababen hawa. Na tura kofar office din na shiga fuskana dauke da murmushi, duk lokacin da zan ga Abbu sai in dinga jin wani irin doki da farin ciki a cikin raina kamar wadda ta shekara bata ganshi ba, alhalin duka duka jiya alhamis har karfe tara na dare muna tare dashi, ranar ta Jumma'ah da safe wayar shi ta tashe ni daga barci, muka gaisa ya maimaita min how eager he was to have me as his, farin cikin da yake ciki saboda samuna da yayi a cikin rayuwar shi. A gare shi wadannan kalmomin kamar wasu routine words ne da ya saba fada min a duk sanda muke tare, a gare ni kam they were far more than golden and diamond words, suna saka ni cikin tsananin farin ciki da jin dadi, suna hana duk wata damuwa da bacin rai samun matsuguni a cikin raina, they were my remedies. Ya juyo daga gaban book shelves din dake kusa da desk din computer dinshi, wani tattausan murmushi ya sakar min da suka sa naji alamun butterflies na yawo a cikina, sanye yake da wandon jeans blue da knit shirt mai kama da sweater, irin shigar da naga samarin zamanin nan nayi kenan a wannan lokacin, shima sai ta maida shi kamar wani saurayin bayan kyawun data mishi, Abbu yasan kan fashion kamar wani fashionista shi yasa ko wane irin kaya ya sanya suke haska shi. Ya maida littafin dake hannunshi cikin jerin littafan dake cikin shelves din, ya juyo gareni gaba daya yana murmushin nan nashi dai, kallona yake kamar wanda zai tsuke ni ta cikin idanuwanshi, it was so intense and disconcerting sai dana ajiye idanuwa kasa ina jin kamar kasa zata tsage in shige, yace “tun dazu nake jiran ki yanzu nake shirin biyawa ta library din in duba ki" nace “ban kula da cewa lokaci yaja bane, sorry!" ya dauki wata jaka mai kama da box dinnan akan tebur ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, ya dan jingina jikinshi da teburin yace “akwai reception da aka hada mana ranar Sunday, kayan da zaki saka ne" na bude jakar na kalli kayan ciki, shadda ce bugaggiya ruwan kasa mai haske sai jaka, takalmi, da gyale su kuma dark brown kalar zaren da aka yi amfani dashi wajen yin surfani, na kara kallon shi nace “ranar Monday fa zamu fara exams dinmu" yace “ba zai taba karatunki ko jarabawar ki ba I promise, ni kaina ban san da zancen ba sai da suka riga suka shirya komi sannan suka sanar dani. I don't want to disappoint them, please help Nafeesah kinji?" yadda ya wani rausayar da kai yana kallona pleadingly, who m I to say no to him a yadda yayi dinnan taking my breath away?? Sai kawai na girgiza kai ina murmushi, nace “Allah ya kaimu ranar" yayi murmushi “Ameen Amour.... Mine" na sunke kai a cikin hijabina, ya wani kuta, “just wait till tomorrow, war haka kin zama tawa, mallakina ta har abada, wannan kunyar taki sai nasa kin neme ta kin rasa" ya saki murmushi mai sauti, “Allah ya kaimu goben nan dai, I really can't wait baby" na kara kanannade fuskata a hijabin, jin abin nake yi kamar a mafarki, mafarkin ma wanda ba zai zama da gaskiya ba, wai goben ne daurin Auren mu? Oh, zan zama matar Abbu, Abbu na wanda so da qaunar sa suka mamaye jini da jijiyoyin jikina, na kauda tunanin daga cikin raina bana so in fara fayyace matsayin da gobe take a gare ni don nasan ba zan gama da wuri ba. Ya dauki key din motar shi muka fita, na jira ya rufe office din kafin muka fara tafiya a hankali zuwa inda ya ajiye motar shi. Ya bude motar ya shiga ciki ya juyo ya kalleni, “sorry, bazan iya maidaki hostel ba saboda sai na biya na dauki su Abdullahi sannan mu wuce masallaci" nace “babu komi, a gaida su" ya gyada kai, “zan kira ki anjima" na maida mishi murfin motar na rufe, ya mata key ya tafi ina daga mishi hannu, sai dana ga fitar shi sannan na daga kafa da niyar tafiya. Kamar daga sama naga tsayuwar mutum a gabana, naja baya a dan tsorace har ina dafe kirji ina jan salati, Matar nan da muka hadu da ita a ofishin Abbu ranar nan ta bayyana a gabana, da alamu shigar rashin mutunci da na ganta da ita ranar a jininta take don kuwa lokacin ma irinta ce a jikinta, zan iya cewa ta ranar tafi ta waccan lokacin bayyana surar jiki ma. Hararata take yi tun karfinta da gwala-gwalan idanuwanta da suka sha uban eye shadow da girar kanti in ka ganta kamar wata doll. Nima na mayar mata da kwatankwacin hararar da take jifana dashi, “Malama lafiya zaki tare min hanya?" ta kama kugu tana wani jijjiga jiki, “ina so ne in fada miki ki rabu da Ibrahim" nayi fuskar alamun tambaya “me yasa?" ta dan daga murya, “saboda nawa ne! Na sha alwashin babu wadda ta isa ta aure shi muddin ina raye" nace “da alamu baki samu labarin cewa gobe ne daurin auren mu dashi ba, na tabbata da kin sani kam da ba zaki tare ni a hanya kina barking kamar tsohuwar karya ba" a girmame matar ta girme ni nesa ba kadan ba, sai dai ni a rayuwa na sau daya zaka zubda daraja da kimarka a idona, abin na matar yayi yawa, ko a lokacin da nayi shirmen son Muneer ban taba tunanin zan yi kwatankwacin abinda take yi yanzu ba, bin kan namiji yana wulakanta ni kamar karya amma in ki in hakura har ta Kai ni ga bibiyar wadda zai aura ina threatening dinta. Fuskar ta tayi looking so pale saboda maganar da nayi, “ni kika kira da karya? just wait, in har ina raye sai na mayar dake abin kwatance, sai na muzanta ki fiye da kare, I'm warning u, ki fita daga rayuwar Ibrahim kafin in mayar dake abin kwatance!!" na daga kafada, “I'm not stopping you from doing whatever you will do, kawai abinda nake so yanzu shine ki matsa ki bani hanya in wuce" ta hasala iya hasala, hannu ta daga kamar zata mare ni, kallonta nake yi kamar wata kayan kashi a yatsine, ita da kanta ta janye hannunta ta maida shi kasa, nayi murmushin mugunta nace “kece kike ta shirme kina bin namijin da yake kin ki, tunda yace baya yi let him be, ana so dole ne malama?" ta wani zare ido tare da buga tsawa “ke...!!" nayi saurin katseta kafin ma ta gama fadin abinda tayi niyar cewa ta hanyar zare ido nima, nace “malama kin ganni nan ban yi kama da matan da threats dinki zasu yi tasiri a kan su ba, kiyi duk abinda zaki yi wanda kike ikirarin mallaka ba zaki taba mallakar shi ba saboda ba don ke aka yi shi ba, a shawarce zan gaya miki ki fita daga rayuwar shi, Idan kuma kin ki ji sai dai kiyi mutuwar da kike ikirarin yi! Abbu ne kamar na aure shi na gama" naja tsaki tare da zagayawa ta gefenta ta wuce abuna ina muttering kalmomin dani kaina bansan me nake fada ba duk don in yi provoking dinta, na kuwa yi nasara. Ina bada baya naji sautin karan data saki cike da takaici, na kuwa saki murmushi kamar zan sheke da dariya.
Chapter 62 · 0% Book details