← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 88

Sashe 66

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ranar Talata bamu yi exams ba sai ranar Laraba. Misalin karfe tara muna cikin exam hall muna jiran invigilators su shigo, sanye nake da doguwar riga dinkin Stella sai mayafi dana yafa mai yalwar fadi, fuskata daga hoda sai kwalli ko janbaki ban shafa ba saboda a sukwane na fita ranar don na kusa makara. Much to my surprise na tsinci Abbu cikin invigilators din, idanunshi suka zagaye ajin har sai da suka lalubo ni ya sakar min kyakkyawan murmushin shi da sai da yasa naji gwiwoyina sun sage, a dan kunyace na maida mishi martani tare da sadda kaina kasa ina tuno yadda muka rabu dashi a jiya da yamma da yazo wajena, yana insisting lallai sai munje ya nuna min gidan da zan zauna ni kuma nace mishi ba sai na gani ba, da yaga alamun ba zan bishi ba sai ya fara min abubuwan nashi da har lokacin kwakwalwata ta kasa daukar su ko sabawa dasu, da kyar na samu na zame na tsere.
Lokacin dana sake kallon inda yake hararata yake yi kasa-kasa fuskar shi na nuna bacin rai, gabana ya fadi, crap! Me nayi? Ko dai tun laifin jiya ne har yanzu yake fushi dani don naga tun daga lokacin bamu sake waya ba kamar yadda bai turon text ba duk da cewa dai na tura mishi wani yau da safe amma bai turo min da reply ba. Aka fara raba mana answer booklet ya dauki wasu yayi row din dake gefenmu na dama, yadda na bishi da ido haka na tsinci idanun yawancin ‘yanmatan ajin suna bin shi da kallo, naji wani takaici da bacin rai yana lullube ni, meye nasu na Kalle min miji? Sai naji kamar in tashi in fidda shi daga cikin ajin, na dai daure ban yi anything silly ba har ya juyo ta bangarenmu. Yazo saitina ya tsaya yana kokarin ciro booklet din, kamshin turaren Armani Code ya mamaye wajen naja na shaka har da lumshe ido, a hankali nace mishi “Abbu good morning!" lokacin daya danyi leaning akan desk din da nake ya ajiye mun takardar, “me yasa kika fito da wadannan kayan a jikin ki?" ya fada muryar shi na nuna bacin rai da distaste, na kalleshi tare da kallon kayan jikina, saboda Allah meye aibun su? Gyalena mai fadi ne ya rufe duk inda ake bukatar ya rufe, kafin in samu ince wani abu ya kara gaba zuwa ga desk din bayana, na danyi shrugging slightly na fara rubuta sunana akan takardar.
Ana bamu question paper na fara rubutu, Abbu ya jingina da window din gefenmu na hagu saitina, duk da ban daga kai na kalleshi ba amma nasan da cewa idanuwanshi a kaina suke don kuwa naji su, don haka zan iya cewa jarabawar ranar cikin takatsantsan nayi ta, ko motsin kirki ban yi ba. Ranar ni na fara submitting, ban tsaya jiran komi ba na bar hall din a tunani na zan iya tsere mishi kafin ya fito, sai ganin shi nayi ya wuce ta gabana, “follow me!" kawai yace yayi wajen parking lot, na sadda kaina kasa in surrender, nabi bayan shi na bude motar daya riga ya mata key na shiga, ina zama ya juyo glaring at me, “na tambaye ki baki bani amsa ba, nace me yasa kike yawo da wadannan kayan?" na daga gyalen jikina ina kallonshi, “naga fa gyalen bashi da matsala babba ne, kuma ya rufe min jiki meye marabar su da hijabi?" yaja motar muka tafi, “it's transparent for Goodness sake, ki duba kiga dazu da muka shigo, hannu da wuyanki duk a waje suke. Maza nawa na gani suna kallonki kina a matsayin mata ta?" juyawa nayi na kalleshi, ashe muna taya daya, “daga yau na hana ki saka gyale ko wani iri ne, be it mai kauri ko transparent I don't care, wear hijab wadda zata dinga rufe miki dunduniya!" na zaro ido, “to ai ni hijabai na gabadayansu ma basu kai biyar ba kuma da guda biyu kadai nazo makaranta" ya daga baki cikin mamaki kamar zai yi magana sai kuma ya rufe bakin, ya sake budewa yace “akwai hijabai a cikin kayan lefenki, idan kin tare ma zan dinka miki wasu for now sai kiyi amfani da wadanda kike dasu kafin ki koma" nace “Abbu....?" ya juyo ya kalleni fuskarshi na nuna rashin jin dadi, “r u arguing with me Nafeesah?" nayi saurin girgiza kaina, “to meye?" sai kawai na sake girgiza mishi kai, muka cigaba da tafiya ba tare da munyi magana ba, wani tunani ya darsu a raina. Na hade fuska tare da turo baki nace “to in dai haka ne sai dai kaima ka daina sa irin kayan daka sa yau, Allah kadai yasan iya adadin matan da suka dinga kallonka yau, kai duka ‘yanmatan ajinmu were looking at you with interest in their eyes" daidai lokacin yayi pulling motar zuwa cikin lot din dake gaban hostel dinmu yayi parking, ya kwashe da dariya cikin farinciki da wani abu mai kama da humor, na kura mishi ido ina kallonshi relieved and amazed, at last! Yayi more than murmushi.
Sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya kalleni, “ni kuma meye aibun tawa shigar?" Armani pants ne a jikinshi da open neck top, ire-iren kayan da suke boye shekaru da girman da yayi su fito da xallan yarinta da kyawun shi. Na turo baki ban amsa ba, hannuna ya kamo ya rike a cikin nashi yana caressing, “girl, Ashe kema kin iya kishi? Ni indai nine baki da matsala dani, ki fadi duk irin kayan da kike so in dinga sawa zan sanya babu musu, m all urs Amour" na sadda kaina kasa ina blushing, na duba naga duk cikin irin kayan da yake sawa babu wanda basu mishi kyau, sai na kauda hirar na fara kokarin janye hannuna daga nashi wanda ya fara sa min tashin tsigar jiki. Ya kalleni fuskar shi a dan hade, “na kula baki son ina rabar ki kwana biyun nan Nafeesah, mai yasa?" duk da maganar da yayi sai dana janye hannuna daga nashi na saka su cikin gyalena, shiru nayi kawai, to in ce masa me? Ina jin kaina kamar wata traitor ko mai laifi idan ya taba ni, I'm feeling awkward idan ya taba ni, feelings ne da ban saba jinsu a cikin rayuwata ba hakan yasa na fara having second thoughts, ko dai don yana abokin Dad ne na kasa sakewa da Al'amuran shi? Ya kuta kawai, “zaki gama kewaye-kewayen ki ne ma ki dawo hanya Nafeesah, ina so zan wuce gida yanzu, me kike so in kawo miki anjima?" nayi saurin girgiza kaina, “babu komi" frankly speaking zan fi so ace ba ma sai ya dawo ba, ya tabe baki “sai wani guduna kike yi fa, kin manta cewa komi wayon amarya sai an sha man ta?" na kalle shi, wani murmushin mugunta ne akan fuskar shi da yasa naji wani tsoron shi yana shiga ta, ya kamo hannuna duk nokewar da nake yi sai da ya kai bayan hannuna saitin bakin shi ya sumbata, nayi saurin bude motar na janye hannuna na fita, sai dana fitan sannan na leka ta tagar motar nace “Abbu a gaida su Hafsy, sai anjima" yayi murmushi kawai yana gyada kai, na juya da sauri na wuce.
Chapter 66 · 0% Book details