Sashe 63
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washegari da misalin karfe daya aka daura auren a babban masallacin juma'ah dake garin Malumfashi. Muna zaune a dakinmu Ni'imah ta kawo wata yarinya tana min kunshi wanda hakan umarnin Abbu ne, text dinshi ya shigo wayata. Na mika hannu na da nake jin shi kamar ba a jikina yake ba na dauki wayar, kai gabadaya ma sauran sassan jikina haka suke tunda garin ranar ya waye, ina ji Niimah da Firdausi suna ta hira amma na kasa saka musu baki duk da cewa rabin hirar a wajen tsokanata ne. Text din cewa yayi, “Alhamdulillah. Yanzun nan aka shafa fatiha, kin zamo tawa ta har abada. Ina taya junanmu murna da farin cikin mallakar junanmu, Allah ya bani ikon rike ki cikin amana da kulawa Nafeesah" sai kuma wani da yace, “Wannan ranar rana ce da ban taba tunanin zata Riske ni ba, ranar dana mallaki abinda ban taba kawowa raina zan mallake shi ba. Jina nake kamar wani sabon halitta saboda tsananin farin cikin da nake ciki wanda na kasa misalta shi, Nafeesah kina da gurbi mai matukar girma da fadi a cikin zuciyata, na roki Allah mai Girma akan ya bamu zaman lafiya mai dorewa. You've Completed My Puzzled and Shattered Life, I really Cherish You Nafeesah" naji hawaye sun cika min idanu, nayi saurin runtse idanun ina kokarin maida hawayen, Allah abin godiya da Girmamawa, wai ni ce yau na zama matar Abbu?? Naji ina narkewa kamar wata jelly akan kujerar da nake zaune, na tabbata da ace ina tsaye ne da sai na fadi. Rangadediyar gudar da Ni'imah ta rangada ce ta dawo dani cikin tunani na, guda take tun karfinta da waya a hannunta ta hau kiran waya tana bada albishir din an daura aure. Wayana ya shiga kara na daga, Daddy ne. Cikin rawar hannu na daga, “Uwata! Amarya!!" abinda na fara dokar kunnena kenan, na kasa magana sai kai dana jijjiga, yace “Nagode Allah da yasa naga wannan rana, ranar dana damka amanar ki a hannun wanda na tabbatar zai rike ki dari bisa dari, dama babu burin duk wani uba na kwarai daya wuce wannan. Yau dai kin zama matar Ibrahim, kin fita daga karkashin kulawar mu kin koma karkashin shi, yanzu shi zai yi sanadiyar ki zuwa gidan Aljannah wadda nasan babu haufi zaki sameta da yardar Allah uwata, Allah ya miki Albarka, Ya Albarkaci Rayuwar Auren ki, Allah ya baku zuriya Dayyiba!" muryar shi tayi kasa can kamar wanda yake so yayi kuka, ni kam kasa daurewa nayi kawai na fashe da kuka, gabadaya wani iri nake jina a tunanina idan nayi kukan zan samu sanyin zuciya. Ya shiga lallashina har na samu nayi shiru kafin ya min sallama. Yana kashe wayar kiran Mommy ya shigo, itama dai Addu'ah ta min kamar yadda Daddy yayi, zuciyar Mace mai rauni, sai tasa kuka, nima kukan nake yanzu sosai su Ni'imah na aikin bani hakuri, ina ji daga wayar Anty Uwani da muryar wasu mata suna ba Mommy hakuri, Anty Uwani cikin fada tace “sai kisa hankalinta ya tashi ai, gashi nan itama kin sata kuka, ina amfanin haka?" tace “kukan farin ciki ne" tace “ai godiyar Allah ya kamata kiyi ba wai kuka ba, shima Abban nata yanzu na baro shi a waje yana share kwallah Allah yasa ba ita ya kira yana kukan ba.... Wannan ai sai ku sanyayar mata da gwiwa...." daga haka dai suka kashe wayar. A hankali nima nawa kukan ya fara yin kasa har ya dawo shessheka kafin nayi shiru ina ajiyar rai. A ranar dai har ba zan iya lissafa iyaka mutanen da suka kira ni suna taya ni murnar yin aure ba, tun daga kan abokaina da yan uwa har wasu daga cikin abokan Mom. Da yamma sai ga Ramlah ta dira a Kanon kamar daga sama, muka yi tsalle muka rungume juna ni da ita muna ihun murna, watanni biyar ciff tunda muka rabu da ita bamu sake haduwa face to face ba sai dai a Video call. Muka zube akan gado muna maida numfashi daya bayan daya, kallona take tun daga sama har kasa ta kyalkyale da dariya, “kaga Amarya a gidan Ibrahim Galadanchi, kin ga wani kyau da kika yi kuwa??" na kai mata duka ina dariya, “meye haka zuwa babu sanarwa?" tace “surprise, dazu na dawo har mun yi hutu abinmu" nace “kun huta ku kam" nan muka shiga hirar yaushe gamo, tana nan tare dani har aka kira sallar magriba, ganinta ne yasa na warware har na samu naci abinci. Nan dai ta min sallama ta tafi akan cewa zata dawo Washegari, bayan na rakata zuwa bakin kofar hostel din na koma daki nayi sallar isha'i, bayan na gama na zauna nayi ta jero addu'o'i game da neman albarkar Allah da zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da nake tunkara a cikin rayuwata. Abbu ya kira ni yace yana jirana a parking lot inda muka saba tsayawa, na tsinci kaina cikin faduwar gaba da sanyin jiki, cikin sanyin jikin na tashi na gyara zaman hijabin jikina na sauka kasa. Jingine yake da motar shi yana danna wayar shi, sanye yake cikin shadda ruwan Makuba yau kam har da hula a kanshi, akwai wadataccen haske a wajen hakan ne ya bani damar ganin fuskar shi sosai kamar cikin rana. Tunda na hango shi naji kafafuna sun fara hardewa, ban taba tsintar kaina cikin fargaba da tsoron fuskantar Abbu ba tunda nake a rayuwata sai ranar, da kyar na iya karasawa gaban shi ina maida numfashi kamar wadda ta sha gudu, babu abinda yayi motsi a jikinshi sai idanun shi da suke kare min kallo tun daga sama har kasa, kafafuna ba zasu taba iya daukana a haka ba sai nima na jingina da jikin motar ina kallon zara-zaran yatsun kafar shi da suka fito ta cikin kyakkyawan bakin budadden takalmin kafar shi yana ta sheki.....
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!
~Me zaku ce game da Shafin yau??
~Lots Of Love and Hearts
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare...
*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®•°Fikrah Writers Association°•*🖋
_In Dedication to Aunty Zee_
_Tukuici zuwa ga Marubuciya SADNAF_
_Godiya Mara Adadi Masoya, Makaranta Littafin Ni Da Abokin Babana, yawan ku ya kai adadin da ba zan ma fara jero sunayenku ba, just know that where ever you are Jedderh really appreciate your love and kindness, #OneLove_
*47*
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!
~Me zaku ce game da Shafin yau??
~Lots Of Love and Hearts
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare...
*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*®•°Fikrah Writers Association°•*🖋
_In Dedication to Aunty Zee_
_Tukuici zuwa ga Marubuciya SADNAF_
_Godiya Mara Adadi Masoya, Makaranta Littafin Ni Da Abokin Babana, yawan ku ya kai adadin da ba zan ma fara jero sunayenku ba, just know that where ever you are Jedderh really appreciate your love and kindness, #OneLove_
*47*