Sashe 14
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai dana yi cracking din kwalwa na kafin na lalubo abin fada, "Chocolate cookies, sweets and chocolate" cikin kamar kiftawar idanu ya maido reply, "noted and done! A tanadar mun delicious dinner pa!" nayi murmushi kamar yana kusa dani, "yes In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya". Shiru shiru bai dawo da reply ba, na ajiye wayar na fita zuwa kicin. Harira nata kokarin hada wuta, na shiga kicin din. Da murmushinta ta juyo tana kallona, wani lokaci dama idan bana komi nakan kama mata da wasu ayyukan. Nace me za a girka mana ne yau kam? Tayi murmushi, tuwon semo ne zanyi da miyar egusi. Shit! Ba abinda nayi niyar girkawa ba kenan, I had to change her mind. Nace "amma tuwo? Baki ganin dare yayi, zamu iya gamawa da wuri kuwa? Don dai ni I need something simple to cook saboda yunwa nake ji" ta dakata da ciro nama da take yi daga fridge "kuma fa haka ne, me zamu dafa to?" nayi er dariya, "just watch me!" na fada store. Na fito da duk kayan da nake bukata na ajiye, ta kalle ni tare da dan dafe kai, "Ohh! Nafee ina zuwa don Allah! Na manta zan goge kayan su Qaseem na makarantar gobe" ta fita da sauri ko amsa mata ban samu nayi ba, Kai kawai na girgiza ina murmushi. Ba yau ta saba ba, duk ranar da nake taya ta girki ni nake karasa shi, bata taba rasa excuse din tafiya ta bar ni da aiki kaji pa dan Adam! Na kara gyada kai kawai na fara yanka green beans, albasa, carrots, cabbage, na watsa su cikin frying pan nayi frying sama sama. Na bude freezer da suke ajiyar dangin nama da kifi na ciro kayan ciki, na wanke su tass na dora a wuta tare da er citta, tafarnuwa da albasa. Kafin kace me gida ya kaure da kamshin daddadan girki mai dadi.
Dambun cous-cous nayi wanda na yanka hanta kanana a ciki, na zuba veggies dinnan dana soya, na soya cous-cous din sama-sama under low heat, kafin na kara ruwa kadan na barshi akan wuta ya turara. Nayi farfesun kayan ciki na hada lemun cocktail, ana kiran sallar Magriba na gama hada komi a kan dinning table, na ajiye numfashi cike da jin dadi. Daki na koma nayi sallah, ina gamawa na fito falo ina jiran dawowar Abbu. Nayi shiru na tsunduma cikin duniyar tunani, meye haka nake yi? Girki? Zaman jira? For what?? I sound like a married woman waiting for her husband, meye haka nake yi saboda Allah? Anya bana yaudarar kaina kuwa?? A hankali na mike jiki a sanyaye zan wuce daki na, karar bude kofa naji, da sauri na juya. Tuni nayi gefe guda da tunanikan da suke neman tarwatsa min kwalwa, na bude baki ina murmushi sosai "Abbu welcome!!"..... A hankali murmushin ya fara dusashewa ganin yana dingisa kafar shi.....
*♡Jeedderh♡*
[11/16, 01:44] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*14*
Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya.
Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe ina kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.