← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 88

Sashe 2

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Bus na hau directly har kofar gate din  KadPoly inda anan nake karatun Diploma na akan Science Lab Tech. Kasancewar an tafi hutu makarantar babu mutane sai tsilli-tsillin wadanda basu tafi hutu ba kawai, a hankali nake takawa har cikin ofishin IT coordinator namu na karbi IT letter na na fita. Hostel din mata na wuce daga can dakin kawata Ramla don nasan bata tafi hutu ba, ila kuwa, Ina sallama cikin dakinsu muka ci karo da juna. Cike da doki muka rungumi juna muna juyi a tsakar dakin kafin daga karshe muka dire a Kan gadonta muna dariya. Kallona tayi tun daga sama har kasa har sama, ta gyada kai tana er dariya, "inye diyar daddynta! Wannan fresh haka kamar wadda aka wanke da inji?" duka na kai mata a cinya Ina dariya, "ke ba baki da mutunci Ramla, duk uban kashin wannan dana tara a wuya zaki ce wai nayi fresh?" sai da muka gama shakiyancinmu na abokai sannan na kalleta, "ke ni ba wannan ba, ya zancen inda zamu je muyi IT ne don ban karbi letter na da wuri ba ban sani ba cikin wajajen da suka bamu ko zan samu?" Ta girgiza kai, "duk an cika a wajen pa gaskiya babu, nima tun last week na kai nawa suka ce wae an cika" fuskata ta dan yamutse, "lallai! Ya zanyi kenan?" kafada ta daga, "oho! Bake wae dadi gida ba kinje kin zauna kina hutu ba? Gashi next week zamu fara. Ni a Kano zanyi nawa" na kalleta "Kano? A Ina??" "cikin BUK, kin san Aunty Habi tana aiki da Lab dinsu, shine tace in je can inyi kawai. Har an kai letter sunyi accepting. Abinda ya shigo dani makarantar kenan na kawo accepting letter din" shiru nayi ina jijjiga kai, "Ramla ko dai nima can zanje inyi nawa IT din kawai? Nasan mawuyaci ne in samu waje anan" ta kalleni, "wa kike dashi a Kano?" nace oho! Daddy yana da mutane da dama acan, nasan ba za a rasa ba. Idan can dinne sai in dinga zuwa weekend gida..... Zan tambayi daddy inji dai tukun. Yaushe zaki tafi Kanon?" "ranar assabar kila" ta bani amsa. Na gyada kai kawai. Kayanta na tayata hadawa, tare muka fito da ita na janyo mata trolley ita kuma tana jan karamar jaka. Muna tafe muna hira da ita har bakin gate, anan muka ci karo dashi, My Crush!. Wata irin farinciki da murna suka rufe ni, Ya Allah ji nayi kamar in daka tsalle. Ta gaban mu ya wuce without glancing at us, duk yadda naso in daure kasawa nayi, ban san lokacin dana kira shi ba. "Muneer!!" cikin wata iriyar murya mai kama da whisper, duk da haka sai daya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalleni, Kai na sadda kasa ina jin wasu irin abubuwa na min yawo a jiki. Cikin siririyar muryar shi da zan iya cewa ita tafi daukar hankalina game dashi yace, "ohh Ummie, ya kike?" Murmushi na saki a hankali kaina a kasa, nace "lafiya qalau, ya karatu?" "Lau..." ya amsa, "....bari in wuce sai anjima..... By the way, I like ur dressing" bin shi nayi da kallo yana tafiya a nutse ina wani irin murmushi kamar kumatuna zasu hade da kunnuwana. Sai dana daina ganin kurar shi sannan na maida Kallona ga Ramlah wadda ta coge a gefe tana jifana da harara, murmushi kawai nayi tare da daga mata kafada naja trolley din nayi gaba. Tsaki taja ta biyo bayana, "wallah Tallahi Babe kina bashi haushi a rayuwa akan Muneer dinnan, kin rabe wa namiji yana yazga ki. Yanzu kaf fadin KadPoly waye bai san cewa kina crushing din wannan player din ba, abun haushi ma da alamun baya yi dake!" fuska na hade sosai. Abinda ke hada ni da ita kenan, kushe Muneer. Bata damu da yadda na hade fuska ba taci gaba, "haba babe, ki daina bayar damu mana. There r so many guys out there ciki da wajen makarantar nan dake karakaina akan ki, don Allah ki kyale wancan yaron. Ba son ki yake yi ba!" a fusace na kalleta, "yeah right! Ai dama ban ce miki yana so na ba koh? Hakan bai dame ni ba, inda rai da rabo, zan ci gaba da bibiyarshi kuma har sai ya so ni Ramlah! Idan hakan yana bata miki rai ki kauda idanun ki daga gare mu, dats all" Kallona ta tsaya tana yi kawai, ba wai yau muka saba irin wannan musun ba in dai akan Muneer ne, Kai ta girgiza a hankali tare da furta Allah ya ganar dake! Cikin gatse na amsa da Ameeen. Muka ci gaba da tafiya har bakin gate ba tare da kowa ya sake cewa komi ba, dama zuciya ce ta kowa a wuya, magana kadan sai ta tunzura mu. Muna fita bakin gate kowa yayi nashi bangaren, ita ta hau motar Abuja ni kuma na dau drop din tricycle har Unguwar Rimi.

Lokacin dana isa gida karfe sha biyu na rana bata karasa ba, kayan jikina na cire na saka na shan iska marasa nauyi na tafi kicin. Tare da Mommy muka hada abincin rana, ta shiryawa daddy nashi a cikin wani katon Basket mai kyau har da wani kayata shi da roses. Wannan Al'adar tunda na tashi naga Mommy tana yin ta, Indai daddy yana gari to abincin shi daga gida ake kai mishi, ba zan boye ba, abin yana burge ni, ina da niyar yin wannan Al'adar idan nayi aure. Direba ta ba ya kai mishi ofishin kula da harkar shigi da ficin jirage ta jahar Kaduna inda anan ne yake aiki a matsayin President na wajen. Ni kam sallah nayi sannan na fito dinning din, tuwon semovita ne muka yi da miyar danyen kubewa wadda ta sha busasshen kifi da tantakwashi da man shanu sai tashin kamshi take yi, sai zobo mai sanyi Shina anyi decorating dinshi da fruits. Muna hira da Mommy jefi jefi muna cin abincin na gaya mata yadda muka yi da Ramlah game da IT dina, shiru tayi tana Kallona kafin tace "zaki iya kuwa Ummi?" er dariya nayi, "haba Mom! It's not like ban taba zaman Kanon nan bane. I will b fine, after all anan zan dinga yin weekend dina ai" kai ta gyada, "sai ki jira daddyn ki ya dawo".

      Koda na fadawa daddy abinda ake ciki ya dan nuna damuwarshi akan gida da zan bari, yace "Uwata tafiya zaki yi ki barmu mu biyu ne a cikin gidan nan kamar mayu?" ni kaina kuma sai a lokacin naji jikina ya fara sanyi, a sanyaye nace to daddy ko dai zan bari ne sai shekara mai zuwa sai inje? dariya suka saki shi da Mommy, daddy yace "oh ma silly princess! M not that wicked da zan hana ki karatun ki, bari in kira Dr. Ibrahim abokina ne, lecturing yake yi a BUK sai muji yadda za ayi" muna zaune ya kira shi suka gama magana suka yi sallama, "wai yace zaki samu sai dai a microbiology lab din su" Murmushi nayi, "daddy kasan fa dama nace maka idan na gama wannan program din zan nemi microbiology a ABU" yace faduwa tazo daidai da zama kenan? Na gyada kaina Ina Murmushi. Yace gobe zan tura mishi letter din sai a kai, Allah sarki princess dina zan yi kewar ki!.

Da dare kuwa kamar yadda daddy ya min alkawari muka fita, chicken republic muka je ya sai min gashin kaji muka tsaya a freeze center ya sai mana ice cream da tarkacen snacks muka koma gida. Tare muka zauna muka ci komi, sauran kayan mommy ta je ta adana su. Mun danyi hira dasu kadan har zuwa karfe tara da rabi, kafin na musu sallama na wuce dakina. Kayan barci nasa na kwanta a rub da ciki idanuna a rufe, daddy gaskiya ya fada. Tun yanzu nake ji kewar su tana dabaibaye ni, anya zan iya kuwa???!
[11/6, 17:17] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
                      ©JeedderhLawalS

                            *03*
Chapter 2 · 0% Book details