Sashe 4
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dana kwashe lokaci mai tsawo a cikin farfajiyar gidan a tsaye kafin na samu kwarin gwiwar jan kafafuna da kyar na koma falon. Ina shiga na ci karo da er aikin gidan wadda saboda tsabar wata irin shiga mara fasali da tayi yasa na kasa gane ko wace irin yare ce, cewa tayi in zo muje ta nuna min dakin da zan kwanta inji madam dinta, babu musu na dauki jakar hannuna na janyo daya daga cikin jakunkunan dana taho dasu nabi bayanta bayan itama ta dauko wasu. Abinda na kula duka dakunan gidan a falon kasa suke, ni tunda nazo ban ga kowa ya hau saman ba. Wani dan madaidaicin daki cikin jerin dakunan dake cikin falon ta bude muka shiga ciki. Dakin yana da fadi ba laifi, Akwai toilet a ciki ga wani medium size gado ruwan golden, mirror da closet sai er karamar sofa da study table. A tsakiyar dakin an malala wani tattausan circle carpet baki, sauran dakin kuwa malale yake da wasu en ubansun marbles fari da gold, well, ba laifi ya burge ni sai dai yadda aka tsara dakin ne sam bai min ba. A raina nace sai na canza shi. Ina ta karewa dakin kallo har ta gama shigo min da kaya na duka, ta tambayeni idan Akwai abinda nake bukata? Kai kawai na girgiza mata tare da mata godiya, ta min sai da safe ta wuce abinta. Jakar hannuna na jefa akan gado na samu gefen gadon na zauna Ina kara karewa dakin kallo, tashi nayi na leka toilet, Shima babu laifi ya hadu, na dawo na bude closet din babu komi a ciki sai er guntuwar kura data yi, tsumma na lalubo na goge ta tas na lalubo turaren kaya a cikin kayana na watsa a gefen closet din kafin na fara shirya kayana a ciki, sai dana cika ta tsil da kaya wasu ma da kyar suka shiga, na makare kan mirror na da tarkacen kayan shafa dana kwalliya da nau'in perfumes kamar a wani dan karamin super store. Sallar isha'i nayi na hada da shafa'i da wutiri, ina gamawa naji wayana tana kara, ringing din dana sakawa daddy ne. Da sauri na tashi na daga kiran, gaisawa muka yi ya fada mun sun isa gida lafiya, mun danyi hira kadan yaba mommy wayar itama muka dan yi hira, sai data kara min da en nasihu akan wadanda ta min sannan muka yi sallama na ajiye wayar. Ruwa na watsa a jikina na nemi kayan barci marasa nauyi na saka na kwanta, amma kwata-kwata barci yace bai san idanuna ba, tunanika iri-iri suka dinga min yawo a kwakwalwa, daga karshe waya ta na dauko na fada duniyar gizo.
Washegari kamar yadda na saba da asubahi na tashi nayi sallah, shiru Ina kan abin sallah a zaune ina debating akan in fita in taya matar gidan aiki ko kuwa in zauna a daki? Daga karshe dai kawai na tashi na fada wanka, usual ways din harkokin rayuwata na bi, kwalliya data kwashe ni kyawawan mintuna talatin, minti ashirin na fiddo kayan sawa da shiryawa, zuwa lokacin dana tsaya a gaban dogon yaro ina sake duba kaina, karfe bakwai da mintuna ashirin. Cike da tunanin yadda zan karasa cikin makarantar BUK na fito falo, babu kowa a cikin falon amma na jiyo motsi a can wata kofa dake gefen dakin matar gidan. A hankali na karasa tare da lekawa, hangame baki nayi kamar zai rabe biyu. Wani dankareren kicin dana gani wanda zan iya cewa ya lunka dakina sau biyu, kayan electronics na kicin babu kalan wanda babu. A gaban gas cooker na hangi er aikin gidan tana soya plaintain, karasawa wajenta nayi muka gaisa cikin girmamawa, na tambayeta matar gidan tace min wai bata tashi daga barci ba, Kai na gyada cike da mamaki. Wace matar aure ce ke kai karfe takwas na safe saura tana barci?? Tambayarta nayi yadda zan isa wajen IT dina, tace ai Direban da zai kaini yana waje yana jirana, tun dazu yayi magana. Juyawa nayi na fita, daga kicin din tace min breakfast fa? Nace mata zanyi acan. A farfajiyar gidan na hangi direban, a mutunce na gaida shi ya bude min gidan baya na shiga yaja motar muka wuce. Mintuna talatin mun shiga cikin BUK, har gaban microbiology lab muka je yayi parking, tare dashi muka shiga lab din ya samu lab attendants suka yi maganganun da zasu yi, ya tafi ya barni bayan ya fada mun lokacin da zai dawo ya dauke ni. Ina zama sai ga Ramla sun shigo ita da Antin ta, nan muka rungume juna cike da murna, itama Anty Halima tafiya tayi ta barmu anan. Da yake ranar farkonmu ce a wurin babu wasu ayyuka da muka yi, wajen karfe goma sha daya muka fito ni da ita zuwa Cafeteria din dake cikin department din. Tafiya muke yi a hankali, tsarin makarantar ya burgeni kwarai, er hira muke yi da ita game da wajen har muka shiga cikin cafeteria din, babu students sosai zama kawai muka yi muka yi order din abinda zamu ci.
Muna gama cin abincin lab muka koma, lab attendants din were very friendly don haka cikin dan kankanin lokaci muka saba dasu. Wadanda suke yin aikin project dinsu sun kawo ayyuka, nan ne fa muka tashi muka fara aiki. Sai wajen karfe biyu muka tashi, wani dan karamin garden muka zauna muna ta hirarmu ni da ita ina jiran Direba yazo tunda ita sai ta jira Anti Halima ta gama ayyukanta, sai wajen karfe biyu da rabi sannan Bala Direba ya iso. Ina hango motar na gane ta saboda a cikinta muka zo. Da sauri nawa Ramla sallama na tashi nayi wajen da yayi parking, a mutunce na gaida shi na bude bayan motar na shiga.
*♡Jeedderh♡*
[11/6, 17:17] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
©JeedderhLawalS
*05*
Wata kyakkyawar yarinya cikin kayan makaranta dogon wando navy blue da shirt fara ta dago kyawawan idanunta tana kallona, ban san lokacin dana sakar mata murmushi ba saboda tsananin burge ni din da tayi, a gaban motar kuma maza biyu ne suma cikin shigar kayan makaranta irin na yarinyar, duk suka juyo suna kallona. Zama nayi sosai a gefenta ina ta watsa musu Murmushi yayin da direba yaja motar, yarinyar da nake tunanin shekarunta zasu kai bakwai zuwa takwas tace min ke ce bakuwar da daddy yace zata zo mana gida? Na gyada kai ina kallonta, nice beauty, ya sunanki? Murmushi tayi, sunana Hafsah amma daddy yana ce min pretty Hafsey, su yaya Abdallah kuma suna ce min Hafsatu... Ta karasa tana pouting cike da shagwaba. Er dariya nayi tare da jan kumatunta, "kai amma Yaya Abdallah bai kyauta ba! Hafsatu ai sunan tsofi ne" ta gyada kai tana turo baki tare da kallon wanda yake kama da shine babban yayansu, "ai kullum sai na gaya mishi amma sai yace wae ai nima tsohuwar ce" na kalli yaron Ina Murmushi, "Yaya Abdallah baka kyauta ba gaskiya, tana yarinyarta ka dinga ce mata tsohuwa?" yaron yayi dariya, "sunan maman Daddy gareta pa, don Allah ba tsohuwar kenan ba?" daya yaron na gefenta ya kwashe da dariya, "tsohuwa ce mana, baka ga har ta fara furfura Akanta ba?" Hafsat ta kai mishi duka a kafadar shi, ya kauce yana mata dariya. Tsokanarta suka ci gaba dayi suna dariya har sai data fara kwalla sannan na tsaida su, "here, enough with the teasing, a kyale pretty haka nan ko?" ta gyada kai tana min murmushi, kanta na shafa ina jinta har cikin raina. Yarinyar tana da wani irin kyau duk da suma sauran yaran suna dashi amma ai kun san kyan mace ya banbanta dana namiji, ina mamakin inda ta gado shi a raina nace kila sai dai wajen mahaifinsu don babu mai kama da mahaifiyar su, dama dama dai Qaseem mai bin Abdallah, naga suna dan yanayi da Anti Mubeenah. Kafin kace me mun saba da yaran, dama ni bani da wahalan sabo suma naga hakan a tattare dasu. Muna isowa gida na dauki school bag din Hafsat ita kuma ta rike lunch box dinta, hannunta cikin nawa muka shiga falo ina taya ta miming din wakar twinkle little star. A daya daga cikin kujerun falon, Anti Mubeenah ce zaune ya harde tana duba jarida, yaran suka zube a gabanta suna bata labarin makaranta, sai dana bari suka gama hayaniyar su sannan na duka na gaida ta. Fuskarta dauke da dan murmushi ta amsa tare da ce min Akwai abinci a kicin, godiya na mata tare da cewa sai nayi sallah, dakina na wuce nayi sallah, na janyo wayata na kira mom don nasan daddy yana office ni kuma ban cika son kiranshi a wajen aiki ba, mun jima muna hira da ita kafin muka yi sallama, ana kiran sallar asr nayi na janyo system dina na kunna kallo tunda babu abinda zanyi, da a gida ne kila na shiga kicin ina taya mommy na girkin dare.
Ina zaune anan ina kallo Hafsat ta shigo cikin kayan makarantar islamiya, na daga Kaina na kalleta ina dan murmushi, "pretty Hafsat an dawo ne?" ta zauna a gefena tana turo baki, "malam ya bamu aiki a makaranta kuma ban iya ba, gashi Abbu da yake koya min karatun baya nan" zama nayi sosai akan gadona nace bani littafin in gani, ta bude jakar ta ta miko min na duba, Tawheed ne, tambayoyi akan imani. Murmushi nayi na kalleta nace "yanzu dai je ki kiyi sallahr magriba tunda an kira, bayan isha'i sai ki dawo mu yi" da murnarta ta tashi ta tafi, har ta kai bakin kofa ta dawo da gudu ta rungume ni, "Aunty thank u" dariya nayi na bita da kallo har ta bar dakin, kai na girgiza na tashi na fada bandaki.