← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 88

Sashe 12

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya Allah! Cheerful Abbu din dana sani ya tafi, wannan Abbu din ban taba ganin shi ba, a fusace yake sosai kamar wanda zai tashi daga zaunen da yake ya hau ni da bugu, gabadaya jikina ya dauki rawa hawaye suka ciko idanuna, bana son fada ko kadan a rayuwata. Cikin rawar murya irin ta wanda yake so ya fashe da kuka nace, "Naje saloon ne shine na biya gidan su kawata Ramlah" ya galla min harara, "da ixinin wa??" nace "umh, ai na fadawa su Malam Bala da suka zo dauka na dazu", yayi shiru kawai yana kallona. Malam Bala ya fada mishi tun dazun, that means he have no right to be angry at her, but still, he's just pissed up. Dan siririn tsaki yaja ganin har na fara shesshekar kuka, ya shafa tattausar sumar kanshi da a koda yaushe a gyare take tana sheki, "it's okay.... Bani ruwa a fridge" da sauri naje na dauko na kawo mishi, yasa hannu ya amsa fuskar shi har lokacin a murtuke, ganin nayi tsaye naki in tafi yasa ya juyo yana kallona, "what?" he sounds so pissed up at me, da sauri na hau share kwallar data fara xubo min again nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi ba zan kara ba don Allah" ya lumshe idanunshi a hankali, "it's okay Nafeesah, banji dadin abinda kika yi ba, a gidanku kina kai har Magriba a waje?" nayi saurin girgiza kai, "to me yasa a gida na? Saboda kin raina ni ne ko kuma don kin baro gidanku kina tunanin zaki yi duk abinda kike so anan ba tare da an miki fada ba?" nan ma kai na girgiza a hankali nace "tun dazu muka taho, gidan Akwai dan nisa ne daga yau" yace "bana tolerating abubuwan nan Nafeesah kin gane? Daga yau kada ki sake wuce bayan Magriba a waje...... No! Duk inda zaki fita you must tell me first indai kina cikin garin Kano, understand?" nayi saurin jijjiga kaina, yace "you can go now!" kamar wadda take akan kaya, da sauri na wuce dakina. Sallah na fara yi kafin na kira mommy muka gaisa, labarin abinda ya faru na shiga bata, budar bakinta cewa tayi "ai yayi min daidai wallahi, wato har kin fara yawo barkatai ko?" sai lokacin naga wautata dana fada mata, na batan fuska kamar ina gabanta tare da turo baki, "mommy! Saloon fa naje saboda Allah daga can na wuce gidan su Ramlah, Ramlah ce fa kawata ke kanki kin shaida sau nawa take zuwa gidan mu ta kwana?" tace "but still baby, bai kamata ki tafi ba tare da kin fada mishi ba, kin san dole ranshi ya baci dama" na shiga diddira kafata a kasa ina gunaguni, "ni dana sani dama ban fada miki ba tunda ba zaki goyi bayana ba" ta sassauta muryar ta, "Ohh Nafeesah baki fahimta koh? Ba goyon bayan shi nayi ba, it's just the fact. Ke yanzu amanar muce a hannunsu, kina ganin ya dace ya barki ki dinga fita kina dawowa duk lokacin da kika ga dama a garin da yake bakon ki iye? Ko kina ganin girmamawa ce ki kama hanya ki fita ba tare da kin sanar dashi ba? Wani Malam Bala is not an excuse tunda ba a karkashin kulawar shi kike ba kin gane?" na gyada kaina a hankali she's right. Muryar daddy na jiyo ta cikin wayar, "Habibty ke da waye kuke waya kika kyale ni ni kadai a falo?" da sauri na shiga mata magiya akan Kar ta fada mishi hirar da muke don nasan kadan daga cikin aikin Mommy ne, ta ba daddy din muka gaisa. Hira muka shiga yi yawanci ta wajen aikin shi ce, mun jima sosai kafin muka yi sallama dasu. Kayan barci na na zura na bi lafiyar gado ko abinci ban nema ba.

Ina kan sallaya ina lazumi bayan nayi sallar asubahi, ban cika komawa barci ba a irin wadannan lokutan, kofar dakin naji ana kwankwasawa, na tashi naje na bude, Harira ce. Muka gaisa da ita a mutunce tace "dan Allah Nafeesah ko zaki taimake ni da girkin yau? Bana jin dadi ne" nayi fuskar tausayi nace "Eyyah sorry pa! Meye za a dafa?" tace "ki dafa duk abinda kika ga ya dace nace "to shikenan" tace nagode ta wuce dakinta. Daki na koma na dauko karamar hijabi data tsaya a kuguna na saka na fita zuwa kicin, yam delight nayi, kafin dahu sai na dauko fresh kifi a cikin fridge na fara shirin yin farfesun kifi.

(Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe please, da kyar ma na samu na warci lokaci nayi typing dinshi wollah)

*♡Jeedderh♡*
[11/16, 01:44] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*13*
Chapter 12 · 0% Book details