Sashe 49
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read
Kamar daga sama naji saukar maganar tashi, na zaro ido sosai. Ban taba zaton zai kawo maganar yanzu ba shi yasa na rasa irin excuse din da zan bashi ma don haka nayi shiru ina jin kafafuna suna rawa a hankali, dama ta yaya nake tunanin tsayawa da kafafuna under Abbu's gaze?? Yace "ina jin ki Nafeesah, last time dana tambaye ki baki bani amsar data gamshe ni ba, yanzu na sake tambayar ki ina bukatar jin gamsasshiyar amsa wadda zata yi convincing dina, so gaya min, me yasa baki son aurena, na miki tsufa ne?" da sauri na girgiza kaina, "baki so na?" na zaro ido ina muzurai, me ya kamata in ce? Yace "kince kina da wanda kike so kuma ni na tambaya a gidanku ance babu kowa, Nafeesah! Dana ce ina son auren ki ba wasa da hankalin mu naso muyi ba, kada kiyi tunanin nima ban hango ko tunana abubuwan da kike hangowa ba, amma meye a ciki? Babban abin bukata Anan shine ace muna son junanmu kuma muna da muradin kasancewa tare, then babu abinda zai faru, there's no body that can criticise us saboda akan gaskiyar mu muke. Enough of all this Nafeesah, na gaji, na gama baki iya uzirin da zan baki, yanzu amsar ki nake so kawai, aure yes ko a'ah?" fuskata ta taru da kwalla, me yake so inyi a irin wannan lokacin idan yazo min da magana kai tsaye yana bukatar amsata? Ya kalle ni da mamaki, "kuka? Na bata miki rai ne?" nayi saurin girgiza kai, "to menene?" nace "I just need time to think over it" ya shafa sumar kanshi, "Lord! Wani lokaci kike so kuma bayan duk lokacin dana baki? Dana ce miki na gaji Nafeesah I mean it, and I don't have the heart to wait any longer" na dan rausayar da kaina gefe, wannan abun fa nice zanyi shi, idan ma da wani abu I'll be the one to take the responsibility, me yasa ba zai barni in yanke hukunci da kaina ba? Yace "ok.... ok... Naji. But believe me Nafeesah, wannan shine lokaci na karshe da zan baki, idan baki yanke shawara ba I'll just do it on my own way, Allah yasan cewa na baki hakkinki" na dan jijjiga kai, ya bude bayan motar ya ciro dan karamin kwali ya miko min, ba musu nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, ya bude motar ya shiga tare da mata key, na dan ja baya har yayi ribas, ya kalle ni yana murmushi, "any sako for pretty??" nima nayi murmushin, "a gaida min ita sosai, ace mata nayi kewar ta" ya gyada kai, "well, kiyi duk iya kewar ta din da zaki yi kafin kizo kema kiyi naki babyn na kanki" na zaro idanu yayin daya saki murmushi gami da min wink yaja motar ya wuce ya barni da bin shi da kallo kafin na girgiza kai ina murmushi na wuce cikin hostel. Firdausi bata dakin, na ajiye kayan hannuna akan gado naje na watsa ruwa tare da dauro alwalar sallah na fito, lotion kawai na murza a jikina na saka kayan barci tare da daura zani a saman kayan nayi sallah, dana gama na dauko Al-Qur'ani Mai Girma ina karantawa har aka kira sallar isha'i nayi tare da Shafa'i da Wutiri, ina cikin nade abun sallar Firdausi ta dawo, na mata sannu da zuwa ta amsa. Waya na dauka na kira Mom muka gaisa tana tambayana karatu na amsa mata da lafiya lau, naso in tambayeta dalilin da yasa bata son Aurena da Abbu sai kawai nayi shiru, na mata sai da safe tare da kashe wayar. Anty Shafa na kira muka gaisa, mun jima muna hira da ita tana kara bani shawarwari akan rayuwata, tace idan har ina son Abbu I should just go for it, na mata godiya muka yi sallama. Na janyo assignment dina na karasa, lokacin dana gama karfe goma tayi already, kwanciya nayi ina tunanika a cikin raina. I think I should just give it a try kamar yadda Anty Shafa tace, after all ba wani sabo ne muke shirin aikatawa ba da nake kokarin kashe kaina saboda son faranta ran mutane wanda nake tantamar ko zasu ga farin abinda nayi at the end of the day?? Nayi murmushi tare da lumshe idanuna, ba jimawa barci mai dadi ya daukeni.
*****
Washegari da safe sai ga kiran Anty Ameenah a cikin wayata, da mamaki na daga muka gaisa da ita, tambayana tayi ko ina free yau? Nace mata ina da class dai amma karfe biyu zan gama, tace how about we have a cup of tea a Flower Garden by four?? Nace mata ba damuwa. Muka yi sallama tare da kashe wayar. Na ajiye wayar a hankali daga kasan raina ina tambayar ko lafiya take son ganina? Curiously.
~Well, m sorry kwana biyu ba kwa ganin posting akai-akai, commitments sun yi mun yawa ne har yanzu ina kokarin sorting out dinsu ne shi yasa amma komi ya kusa zuwa karshe in shaa Allah
~So me kuke tunani game da chapter din yau?
#TeamAbbu 💞💞💞
*♡Jeedderh♡*
[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*Wannan shafi na Sadaukar dashi ga Marubuciya SADNAF da MAKAWA, I really appreciate you guys with your cheerful and concern, thanks. Sauran Marubuta ina gaishe ku sosai tare da duk wani Makamancin littafin Ni Da Abokin Babana!*
*39*