← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 88

Sashe 68

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 9 min read

This page goes to Maryam Maman Muhammad, nasan cewa hakan bai kai rabin abinda kika yi mun ba, I just hope that hakan zai bayyana farin ciki da godiyar da nake son nunawa. Nagode, Allah ya bar kauna.
UMMI-BABBA, Abbu yace a gaishe ki da kokari.....

*49*

Kwanan mu biyar a gidan Anty Uwani. Daki guda aka killace mana ni da wata mata, babu abinda take yi sai gyaran jiki dana fata, hatta da ruwan wankana ya koma na turare, man shafawa na turare, hodar da zan shafa, turare. A iya kwanakin nan ban taka ko kofar gida ba, kullum ina daki, daga matar nan ta fita da wannan abin daga dakina na ci sai ta shiga da wannan abin na sha. Aikin kenan. A kwana na shida ne ta min wani irin wankin gashi wanda yasa gashina yayi wani irin taushi mai ban mamaki, ya kara kyau, tsawo da baki. Washegari kuma aka min lalle, a ranar da yamma da muka yi video call da Abbu baki ya bude yana kallona kamar wata sabuwar halitta, koda yake kusan kamar an canza ni dinne, fatata ta kara haske da laushi da komi ma, ni kaina idan na kalli kaina a madubi sai nayi mamakin canzawar da nayi balle Abbu. Hirar ranar dai base on tambayoyin yadda aka yi na canza haka muka yi ta. Sai da Anty Yagana wadda take min gyaran jiki ta shigo tasa muka yi sallama, ina kashe wayar ta hau ni da fadan bata hana ni yin video call da kowa ba? Ni dai baki na turo gaba na kauda kaina gefe, kwanaki shida rigis ba tare dana saka Abbuna a ido ba ji nayi kamar numfashina zai dauke saboda kewar shi shi yasa na ture gargadinta gefe na danna mishi kira, murmushi nayi ina jin yadda naga ya rikice daya ganni. Ta dai gama fadanta ina sauraronta, sai data gama ne nace mata tayi hakuri, sannan ne ta fara gudanar da aikin daya kawo ta.
Washegari da safe muka yi sallama da Yagana saboda ta gama aikin da zata yi, ta tafi cike da alkhairan da Mommy da Anty Uwani suka mata, ni kuma na sha shawarwari da koyarwar abubuwan gidan miji da rayuwar aure. Da yamma aka yi sitting a gidan Anty Uwani. Mata ne zalla a wajen yawanci kawayen su Mommy ne, sai kadan daga relatives da abokai na da muka gaiyata. Anty Shafa ce ta shirya ni, sai a lokacin nasan tazo ashe kwananta biyu a Naija. Ta shirya ni cikin wasu riga da zani da wani farin yadi mai holes a jikin shi, sai aka min nadi da blue din tie, blue din takalmi high heel, blue purse, blue mayafi karami data dora shi akan kafadata. Fadar irin kyawun da nayi ma bata bakine. Haka dai aka gabatar da bikin cikin salama komi ya tafi yadda aka tsara, anyi ciye-ciyen abinci, snacks da lemu kamar ba gobe, bayan nan su Ramlah suka fita suka kwashi rawa har da su Anty Shafa, koda aka nemi da in fita filin rawa ki nayi, na kara hakimcewa akan tuntu inda aka yi shirin kayan gargajiya kamar irin bikin nan na gidajen sarautun da, sai da Hajiya Amina kawar Mommy na tazo ta fiddo ni sannan na tashi naje filin nayi tsaye, dama can ni ba gwanar rawa bace balle kuma a gaban manyan mutane irin wannan kuma ace bikina ne? Taya ma zan iya rawa?? Nan mutane suka fara sauke ruwan naira a kaina sababbi kamar wasu takardu, ba shiri DJ ya maida sautin wakar dake tashi zuwa Ruwan Kudi, taro dai yayi lafiya lau Alhamdulillah, da yammaci likis aka watse taron.
Anty Shafa ta dauke mu a motar ta zuwa gidanmu, ai sai a lokacin take fada min cewa wai washegari za a kaini Kano. Na zuba mata idanu na a sanyaye cikin sanyin jiki kamar wadda aka zare mata laka, har muka isa gidanmu ban iya cewa komi ba. An sake fente gidan ya dawo kamar sabon gini, a farfajiyar gidan canopies ne an shirya su kashi-kashi ga kuma kujeru irin wadanda ake yi na tyres a shirye, hasken bulbs jajaye ya kawata wajen sosai da sosai, ina ji Ramlah tana tambayar Anty Shafa abinda za ayi tace wai shi kuma Dinner ce kawai su Mom da Dad suka hada min, a raina na girgiza kai ina jinjina bidi'a irin ta su Mom. Yan uwa suka wa motar da muke caa kamar kiyashi da kyar muka fito daga cikin motar, kai tsaye dakin Mom dina aka wuce dani, mutanen dake ciki basu wuce biyar ba duk abokanta ne sai Nene matar kawu Hassan da kuma Anty Asma'u matar Kawu Ali.
Mommy ta taso ta rungume ni, ina ji na a jikinta kawai naji na saki kuka, ta fara tapping bayana alamun lallashi ba tare da tayi magana ba nasan tana tsoron tayi magana ne kuka ya kufce mata. Anty Asma'u ce ta janye ni daga jikin Mom din ta kaini bandaki, nan ta cire min kwalliyar da aka min ta hada min ruwan wanka ta fita daga dakin, jiki a sanyaye na shiga cikin bath tub din nayi wankan tare da daura alwala na fita. Lokacin dakin daga Anty Shafa sai Mom da Anty Asma'u, suka umarce ni da inyi sallah, nayi. Ina gamawa suka fara caccaba min kwalliya, ana cikin yi aka kira Isha suka saki muka yi, Anty Shafa ta bar Anty Asma'u tana min kwalliyar ta koma wajen Mommy itama ta fara mata. Doguwar rigar shadda suka dauko mana maroon ta sha aiki tun daga sama har kasa, Mommy ma irin kayana ta saka sun mata kyau sosai ta fito kamar wata karamar yarinya. Muka jera muka fita falo da ita muna ta sheki, babu kowa a cikin falon sai Daddyna, ya sha babbar riga ta shadda irin ta jikinmu har ma da surfanin jikinmu, yana ganin fitowar mu ya tashi tsaye, hada mu yayi mu duka da Mommy ya rungume mu, na rirrike shi zan fara sana'ar hawaye yayi saurin daga fuskana yana girgiza min kai cikin murmushi, “umh umh Uwata, banda kuka ko so kike ki bata min kwalliyar ki?" na girgiza mishi kai, yace “good girl, muje koh?" suka saka ni a tsakiya shi da Mommy kowa ya rike hannuna muka fita. Wajen ya kara kawatuwa saboda dare da yayi, mutane duk suka mike tsaye suna tafi lokacin da muke wucewa ta gefen tables din da suke zaune har muka karasa wajen da aka tanadar mana muka zauna sannan suma suka zauna.
Anty Uwani ce ta bude taron da addu'ah, bayan ta gama ne kuma Daddy da Mommy suka fita suka wa baki barka da zuwa, daga nan suka fara bayanin farin cikin da suke ciki na aurar da kwallin kwal din diyarsu, Daddy yace yanzu duk wasu burikan shi sun cika sai fatan gamawa da Duniya lafiya Mommy kuma tace buri daya ya rage mata shine taga Diya na jikoki a wajenta, aka yi dariya ni kuma na sadda kaina kasa. Bayan sun gama bayanan su suka dawo suka zauna, aka ci farfesun kifi sardines, chips, da lemuka, aka sake rufe taro da addu'ah sannan aka watse. Bamu tsaya yin komi ba kowa ya nemi makwanci.
Washegari Daddy ya ja mu sallahr Asubah a dakin shi, bayan mun gama sallar munyi karatu kamar yadda aka saba, Daddy ya fara min nasiha Mommy ma ta dora da nata, Daddy ya rungume ni yana lallashina daga kukan da nake yi babu kakkautawa, ya shiga lallashina har nayi shiru, yace “Allah ya miki Albarka Uwata, hakika ke ‘ya ce ta gari wadda ta zama sanyin idaniyar iyayenta, in Allah ya yarda sai kin samu wadanda zasu miki fiye da abinda kika mana, Allah ya albarkace ki da rayuwar aurenki gabadaya. Na hore ki da Biyayya ga mijin auren ki, ki bishi sau da kafa, ki mishi biyayya tsakanin ki da Allah, idan kika yi haka in shaa Allah ba zaki tabe ba Uwata!" kuka muke ni da Mommy, shi kan shi daddy sai daya share kwalla, bayan mun yi shiru muka koma dakin Mommy muka kwanta barci bamu tashi ba sai bayan karfe goma, break fast ya kammala amma na kasa cin abincinnan saboda tsabar fargabar rabuwa da iyayena, dama haka kowace ‘ya mace take ji ne?? Kwance nake shame-shame akan gado tunda na tashi daga kan dinning, yatsun hannuna ma da kyar nake iya daga su, Ramlah ce tazo ta dame ni da hira har na dan warware. Karfe daya motocin daukar amarya daga Kano sun dira, gabana ya shiga dukan uku-uku, kafin kace me! Na fara hawaye. Anty Shafa ta harare ni tace “wai ke tsabar iskanci ne ya miki yawa zaki saka mutane a gaba kina musu kuka, wa ya zage ki?" sai na kara kware mata baki, ta kama baki tace “to?! Ikon Allah, ni kam ba zan iya dake ba..." ta fita jim kadan ta dawo da Anty Uwani, da wuta-wuta Anty Uwani ta tura ni bandaki nayi wanka da wasu sabulai masu kyau da kamshi, ina fitowa nayi sallah. Anty Shafa ta min sharp kwalliya na fita muka gaisa da bakin da suka zo daukar amarya ciki har da Anty Ameenah, muna gaisawa na koma daki. Dama already duk wasu kayana an riga an kaisu Kano kwanaki biyu da suka wuce, bayan su Anty Ameenah sun huta sun ci abinci, nan aka fara min kwalliya data daukemu kyakkyawar awa guda, ana gamawa muka yi sallar La'asar aka bani riga da zani na atamfa super ruwan ganye nasa, Anty Shafa ta dora min gyale akaina suka kama ni har dakin Daddy muka yi sallama ta karshe, ya jaddada min yin biyayya, juriya da hakuri a cikin rayuwar aurena, ana tashi dani na yi rau-rau da idanu, Anty Uwani tace “wallahi kika kuskura hawaye ya zuba a fuskar ki sai na mazge ki!" Daddy yace “a'ah Uwani, bi ta a hankali mana" ta kamo hannuwana ina turjewa ta jani tana mitar Daddy ya bata ni da yawa gashi za a kaini gidan aure, mutane suka biyo mu duu har gaban farar rantsamemiyar Land Cruiser ta daukar amarya, Daddy da kanshi ya bude motar ya kamo hannuna ya saka ni a ciki, zuwa lokacin kam kuka nake yi sosai har da ihu, da kyar suka tura ni aka rufe motar, Anty Shafa da Ramlah suka shigo aka rufe motar, sauran masu rakiya da su Anty Ameenah suka shiga sauran motocin. Ina kallon su Mommy a tsaye, Mommy ta kwantar da kanta a kafadar Daddy tana kuka, motar tana fita daga gidanmu na yadda kaina a kafadar Anty Shafa na kara sakin wani kukan. Lalle gaskiyar bahaushe da yace ‘Aure yakin mata!' in ba aure ba meye zai raba ni da masoyan Ruhina bayan mutuwa??
~Hii dearies, sorry for the short Chappy da kuma rashin posting jiya, I was engaged in soooooo many commitments shi yasa amma in Allah ya yarda ku tara gobe, I promise a very long chapter for u my Dears.
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare
Chapter 68 · 0% Book details