← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 88

Sashe 61

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read

A hankali ya gangara motar shi cikin gareji yayi parking, “Amour, sai anjima, take care" nace “toh Abbu na, take care too" yace “mimm, wai Abbu" dariya kawai na saki wadda nasan tana saka shi cikin nishadi na kashe wayar, yayi murmushi yana bin farar Toyota data shigo cikin gidan tayi parking a daidai inda yayi parking din tashi motar. Saddiqa babbar Yayar su Mubeenah ta fito daga cikin motar, shima fita yayi ya gaidata cikin girmamawa, ta amsa a tsaitsaye tana kumburi kafin ta wuce shi fuu, ya bita da kallo cike da mamaki, matar tana da kirki unlike sauran kannen Mubeenah da ita kanta Mubeenar, duk cikin danginta daga ita sai Shafa'atu ne masu sanyin hali a cikin su, yau kam ko mai ya hau kanta? Ya tabe baki ya wuce wajen maigadi suka dan yi en maganganu ya shige cikin gida. Tun daga cikin falo yake jiyo hayaniyar dake tashi daga can dakin Mubeenah. A can dakin na Mubeenah kuwa akwatuna ne a tsakiyar dakin manya har guda shida, Saddiqa na tsaye a gabansu ta kama kugu tana kallon Mubeenah dake kwance akan gado tana latsa waya, tun kayan barcin ranar data tashi dasu ne a jikinta bata canza ba gashi lokacin har karfe hudu na yamma, gashin kanta ya cukurkude ya cure waje daya, Saddiqa ta saki kugu data kama ta fara tafa hannayenta tana sallallami bayan ta gama sauraren abinda kanwar tata Mubeenah ta fada mata, “Innalillahi.... Mubeenah?! Anya kina da hankali kuwa? Kishiya ake shirin miki amma what?? You are cool with it?? Wai ke wace irin mahaukaciyar yarinya ce Mubeenah??" ta dago ta kalli Yayar tana gunaguni, “ni fa wannan aure za zai yi gaba ya kaini ba baya ba, kina kallon akwatunan daya zube min shake da kaya a matsayin kayan fadar kishiya, 5 millions ya bani in kara jarina bayan haka yana nan yana sake gina mana sabon gida kuma ya min alkawarin zai canza min kayan daki sababbi, bayan haka ita yarinyar da zai aura ta zauna damu anan, na riga da nasan halayenta ciki da bai na tabbata da cewa ba zata taba cutar dani ba balle ‘ya‘ya na ke in fact na tabbata Ibrahim ba wai don yana son ta zai auro ta ba sai don kawai ya bani haushi kamar yadda yake fada tun ba yau ba, to kin kuwa ga menene nawa na yin fushi ko in wani kama bori kamar yadda kike cewa inyi? Kin ganni nan wallahi ko a kwalar rigata, in dai aurene yaje yayi tayi ga fili ga mai doki" bayani take zubawa tun karfinta babu ko digon aya balle comma, yayin da Saddiqa ta sake baki da hanci tana kallon kanwar tata kamar wadda tayi gamo, ta jijjiga kai cike da takaici tace “naji dai ana cewa ke mahaukaciya ce, amma ban taba zaton cewa haukan naki ya kai mataki na farko ba sai yau. Ke don kaza kazar ki, (ta kawo zagi ta lailaya mata), kowace mace tana shiga cikin tashin hankali da fargaba idan za a mata kishiya, amma ke kina zaune hankalinki kwance kina gaya min wai an baki jari kuma za a miki sabbin kayan daki. Kudin banza kudin wofi? Ke don ubanki kin manta yadda muka sha dabi da amaryar Abban mu?" ta kuta, “koda yake kina yarinya dama ya za ayi ki tuna? Ga kuma wata irin kwalwa ta kifaye da Allah ya halitta miki?" ta wani cuno baki gaba, “Na gaya miki yarinyar tana da kirki sam ba halinta daya da sauran matan da kike fada ba..." Saddiqa ta warci kofin dake kan mirror ta saita bakinta ta jefeta dashi Allah yasa ta kauce da sauri, da sai ya dauke mata hakoran gaba biyu, Saddiqa tace “banza mahaukaciya wadda bata san inda yake mata ciwo ba. Kina ta daga murya kina wani fadan cewa kin san yarinya, kin san halinta ko tasan naki halin? Tazo gidanki ta zauna ta gama sanin sirrinki dana gidanki ciki da bai, taga weakness dinki taga komi naki, taje ta gama damarar kwace miki miji daga hannun ki amma kina zaune hankalinki kwance har kina da confidence din daga min wannan bakin naki ki ce wai kin san halinta?" da alamu ko kadan maganganun Saddiqa basa shiga kunnen Mubeenah, tace “ke ce kika kasa fahimtata dai, ni nasan Abinda nake yi. Da wadda ban sani ba ai gwara wadda na sani, ko babu komi yarinyar tana da biyayya sau da kafa, hakan zai bani damar juyata yadda nake so!!" Saddiqa ta dafe kanta da hannuwa biyu kamar zata kurma ihu, Mubeenah ta kalleta cikin mamaki, “wai ni kam don Allah menene damuwar ki akan maganar auren nan, ke za a yiwa kishiya ko ni?" Saddiqa tace “Yi miki kishiya fa kamar yi mana ne, kin sani kamar yadda nima na sani, Ibrahim zama yake yi da ke kawai ba wai don yana jin dadin zama dake ba, kin sani" Mubeenah ta katse ta, “ni nasan Ibrahim yana so na" Saddiqa ta daka mata wata tsawa data sa tashi zaune dangargar akan duwawunta babu shiri, tace “ki min shiru Mubeenah!! Ke ce banza da kika kasa tantance so da dole, idan kika kuskura kishiya ta tako kafarta cikin gidan auren ki wallahi ina mai tabbatar miki da cewa kashin ki ya bushe, idan kin san ma'anar OUT to tsab zata yi waje dake kuma ina mai tabbatar miki da cewa idan har kika sa kafa kika bar gidan Ibrahim to ki tabbata cewa kinyi sallama da aure, I am as sure as hell babu wanda zai yi marmarin daukar ki a matsayin mata a yadda kike dinnan, wallahi Ibrahim kadai ne rufin asirinki" Mubeenah tace “Ibrahim yana so na, ku daina cewa wai baya so na, auren da zai yi babu abinda zai ragu daga son da yake yi min" Saddiqa ta juya ta kara juyawa a cikin dakin kamar wadda take fareti, “idan na gama da case din auren ki I'll make sure to take you to psychiatrist for sure. Amma kafin nan bari inje in samu Haja (mahaifiyar su) babu macen data isa ta shigo gidannan wallahi" ta sa kafa ta bar dakin fuuu a matukar fusace kamar guguwa, Mubeenah ta daga kafada ta koma ta kwanta abinta. Saddiqa na fita taci Karo da Abbu a tsakiyar falo, bata damu da cewa yaji maganganun su ba ko bai ji ba ta shura kafa ta bar gidan. Ya girgiza kan shi a hankali yana murmushi amma fa can kasan xuciyar shi ji yake murmushin yafi mishi madaci ciwo, zuciyar shi kamar ana diga masa ruwan dalma saboda yadda take azalzalar shi da kuna, me yafi ciwo irin kaji cewa matar aurenka bata kishin ka??
~So what did you think about today's chapter?
~Kuna tunanin akwai mata irin Mubeenah a cikin duniyar nan kuwa? Idan akwai, wane irin hukunci kuke ganin ya dace da ire-iren su??
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare🤝🤝

*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*46*
Chapter 61 · 0% Book details