← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 88

Sashe 56

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikin barci na kai hannu kasan filona na lalubo wayata dake vibrating, duka-duka karfe goma ne da rabi na safiyar ranar Assabar, da yake ranar hutu ce kuma ban samu nayi barci da wuri a daren jiya ba shi yasa na ke jina kamar wadda ta kwanta a lokacin saboda tsabar barci. Ban ko tsaya duba caller ID ba na dauka, muryar Sadiya ce ta doki kunnena, "Asslm, Nafeesah hope ban katse miki barci ba?" cikin muryar barci nace "kin katse min mana" tace "sorry, dama muna nan AKTH ne shine zan fada miki" na tashi zaune a sukwane nace "Teaching Hospital kuma? Waye babu lafiya?" tace "Ni'imah ce wallahi, ta samu miscarriage yau da safen nan" jikina yayi sanyi sosai, Allah sarki Ni'imah. Nace "ki turo min da number din dakin da kuke, gani nan zuwa" na ajiye wayar tare da dirowa daga kan gado. Wanka nayi na fito na Karya, ban wani tsaya yin kwalliya ba na saka kayana kawai na fita, sai a cikin mota ne na kira Ramlah Ina fada mata, tayi jimamin abin sosai tace zata kira ta mata jaje. Ban samu Sadiya ba a dakin da aka ajiye su lokacin da naje, Anty Ameenah da Anty Rayyah suna nan a dakin tare da wata dattijuwa sai kannen Bashir mata su biyu, Ni'imahr na kwance tana barci an sa mata drip, ta wani dashe tayi fari tas kamar wadda babu jini a tattare da ita. Muka gaisa dasu Anty Ameenah cikin mutunci har tana bani hakuri akan wai an taso ni daga makaranta, nace a kunyace haba Anty, Ni'imah tafi karfin haka a wajena ai.... Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, suka amsa da ameen. Sadiya ta shigo dakin hannunta rike da na Jameel dan Anty Jameelah wanda yake tafiyar ta-ta-ta, muka gaisa da ita itama na musu jaje, naja Jameel a jikina ina tambayar shi inda yaje yana ta min gwaranci ina murmushi. Ni'imahr bata farka ba sai bayan azuhur, su Anty Ameenah suna waje suna sallah da yake ni fashin ta nake yi, na matsa gefen gadonta Ina mata sannu tare da tambayar ta abinda take bukata? Kuka kawai ta saka tana shafa cikinta, na rungumo ta a jikina ina dan jijjigata kamar nima in rushe da kukan nake ji, it's not easy ka dauki cikin abu ka raine shi, bayan ka gama kwallafa ranka a kanshi kuma sai Allah ya jarabce ka da rashin sa, hakika Allah kadai yasan irin sakayyar daya tanadarwa irin wadannan matan. Nace "kiyi hakuri Ni'imah, haka Allah yaso. In shaa Allahu zai kawo miki mafi alkhairin sa, stop crying please kinji?" ta jijjiga kanta. Naje na xubo mata ruwa a cikin cup ta kurba, lekawa nayi na gaya musu ta farka sai gasu sun duro cikin dakin, kowa sannu yake jera mata tare da nasihar fawwalawa Allah lamuranta, nan aka zuba mata abinci muma muka zuba namu muka ci. Da yamma sai ga Bashir din yazo ashe ma baya gari saukar shi kenan daga Abuja, bawan Allahn nan har da hawayen shi abin gwanin ban tausayi wallahi. Bayan Magriba su Anty suka yi haramar tafiya gida, Anty Rahina tace in zo ta sauke ni a makaranta mana nace mata ai ni anan zan kwana, tace inah! ga Sadiya nan da Gwoggo Hinde sun isa in zo ta maida ni makaranta kawai, nace mata ni fa anan nayi niyar kwana. Tayi shiru tana kallona ganin na kafe kafin tace "kin fadawa iyayen ki?" nace "zan fada musu anjima dai" tace ai shikenan, Gwoggo Hinde zo mu wuce gida dake kawai. Da haka suka mana sai da safe suka tafi bayan sun ajiye mana duk abinda zamu bukata. Na shiga bandaki na gyara jikina, ban taho da panties bama sai dana fita waje na sayo wasu pad ce ma ban nema ba da yake ni ma'abociyar ajiyar su ce a cikin jakata saboda emergency. Na fito daga bandakin ina gyara zaman rigar jikina, daidai lokacin Abbu yayi sallama ya shigo cikin husky voice din nan nashi Hafsy na biye dashi a baya, zuciyata tayi wani irin fari da ganin shi kamar zata haske duniya da abinda ke cikinta, gabadaya ranar ban ji muryar shi ba mun dai yi exchange din messages a tsakaninmu da rana, fuskar shi ta nuna zallan mamaki da ganina kafin baiyanannen farin ciki daya kasa boyuwa ya nuna akan fuskar tashi, na ja kujerar kusa da gadon Ni'imah din na zauna. Na Kalli Hafsy dake tsaye a bakin gadon Ni'imah na mika mata hannu alamun tazo ina murmushi, ta makale kafada tare da kara lafewa a jikin Abbu alamun ba zata zo ba, na janyo ta jikina tana kokarin kwacewa amma na hana ta, nace "haba Hafsy na ni dake bata baci, Waye ya tabo min ke?" ta turo baki tana nuna ni da yatsan ta, nace "ni da kaina? Me na miki?" tace bake bace ba kike kin zuwa ki gaida ni, kullum sai nace kizo ki ganni amma baki taba zuwa ba! Na dan saci kallon Abbu dake gaisawa da kannen shi amma idanuwan shi suna kanmu yana mana dan murmushi, na janye tare da kallonta nace "kiyi hakuri kinji? In shaa Allahu zan dinga zuwa Ina ganinki, so stop frowning and smile kinji?" tace "promise?" na gyada mata kai. Aka kwala kiran sallahr Isha'i a daidai lokacin, Abbu ya zube min wayoyin hannunshi a gabana ya fita da niyar yin sallah.....
~Nasan zaku ce chapter din yau ma yayi kadan, amma ya zanyi? Wallah bani da lokacin yin typing da yawa Ne shi yasa
~Lots of love and Hearts Ni Da Abokin Baba Na Fans
#TeamAbbu
#OneLove❤❤
#AnaTare🤝🤝🤝

*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*_Wannan shafi dungurungum na marubuciya RUFAIDA UMAR IBRAHIM ne. I was touched and impressed lokacin dana ji cewa cikin masoya kuma makaranta littafin Ni Da Abokin Baba Na kina ciki. Sauran Marubuta dake bibiyar littafin ina gaishe ku, wadanda suke kan posting nasu littafan ina musu fatan alkhairi. Masoyan Ni Da Abokin Baba Na ina gaishe ku a duk inda kuke. #OneLove_* ❤❤❤

*43*
Chapter 56 · 0% Book details