← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 88

Sashe 15

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mijin Anty Ameenah yana dawowa falon ya mana sallama ya tafi, Anty Ameenah ta dan taka mishi kafin ta dawo suka hau hira da Abbu. Mu kam muna zaune muna kallon news don in Abbu yana falo bamu cika kallon tashoshi barkatai ba, motsi kadai zai yi in Allah ya yarda da sannu na yake motsawa, bana ji a rayuwata na taba jin irin wannan feeling na 'protecting' da 'caring' ga kowane Bil'adama irin Abbu ba. Aka kira sallar Azuhur, Anty Ameenah ta umarce mu da mu tashi muje mu yi sallah, duk muka mike, mazan har Abbu suka fita zuwa masallaci ni kuma na tashi zan wuce dakina, Hafsy tana kan kujera tana barci, har na kai tsakiyar falon sai na juya na kalleta, "Anty ko zaki shigo kiyi sallah a daki na?" ta kalleni tana dan murmushi, "Eyyah, hutu nake yi Nafeesah, je ki abinki" a dan kunyace da jin kalamanta na juya. Ina gama sallah na koma falon, ina zama suma su Abbu suka shigo, muka bi Abbu da sannu ni da Anty Ameenah har ya zauna akan kujerar daya tashi. 'yar aikin gidan ta fito da niyar dora abincin rana, bata san abinda yake faruwa a gidan ba, ita dai taga bakuwa ta gaishe ta sannan ta wuce kicin abinta. Muna nan zaune sai ga Anty Rahina ta shigo goye da danta a baya, na tashi da sauri ina mata sannu da zuwa, hannu na mika a bayanta ta sauko min da babyn, na rungume shi tsam a jikina, Ya Allahu!! Ina son yara kamar me!
Anty Rahina ta zauna a gefen Abbu, sannu take jera mishi kamar bakinta zai tsinke na kula suna matukar ji da kanin nan nasu, fuska cike da damuwa take kallonshi, "me ya faru Ibrahim? Garin Yaya??" yayi shiru kawai yana kallonta, to me zai ce??

*_Flashback_*
Yana tsaye a bakin titi a kokarinshi nason yayi crossing ya shiga wani babban shopping mall a garin Lagos kafin su taho ya tuno da ita, haka kawai ya tsinci kanshi da son yi mata tsaraba ko don shima ya faranta ranta yadda itama take faranta mishi ta hanyar yi mishi dadadan girke-girke masu kara lafiya. Don haka ne ya ciro wayar shi ya tura mata da text.
"......yes, In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya....". Reply din data dawo mishi dashi kenan, yayi murmushi sosai, har kullum kulawar yarinyar zuwa gare shi tana matukar burge shi ba kadan, tunanin amsar da zai tura mata yake yi lokacin da aka ba wadanda suke kasa hannu su wuce, taku daya biyu yayi, bai tantance mai ke faruwa ba sai jin shi yayi kwance a kasa rike da kafar shi ta dama, ashe yabi ta wrong way ne, daidai lokacin an ba ababen hawa dake wajen hannu, ba tare da su duka sun kula ba wani mai mashin yabi ta kan kafar shi ya wuce.....!

*********
Yaja numfashi a hankali bayan ya gama tunano abinda ya faru, kallonta yayi yana dan murmushi, "kawai ikon Allah da tsautsayi" ta girgiza kai, "to Allah ya kara kiyayewa" duk muka amsa da Ameeeen. Maigadi yayi sallama ya shigo dauke da manyan kuloli, Malam Bala ya biyo bayan shi rike da wasu, Anty Rahina ta umarce su dasu kai kan dinning su ajiye, suka ajiye suka juya. Ta kalli Abbu, "na dafo maka abinci daga gida, kana jin yunwa ne?" ya gyada kai, ta mike "bari in zubo maka toh" da sauri na mike ina kara rungume Baby Jameel a hannuna, "Anty bari in zubo mishi" tayi murmushi tace to shikenan. Ta koma ta zauna ni kuma na wuce kicin. Harira nata kokarin hada miya, nace "kiyi abincin kadan fa, Anty Rahina ta kawo abinci" tace to shikenan. Na kwashe plates da spoon da zasu isa na koma falo, na zubawa Abbu abincin na kai mishi kafin na koma na zubowa su Anty Ameenah, ni da yara kuma muka hau dinning. Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, na kalli agogo. No wonder! Lokacin cin abinci yayi ai! Ganin su Anty Ameenah a falon sai data danyi turus! Kafin ta karasa, ta zauna akan kujerar dake kusa data Anty Ameenah tana dan murmushin yake, wai "su Yaya Ameenah ne? Ai ban san kuna gidan ba, ina daki ina ta barci" Anty Ameenah ta danyi murmushi, "Allah sarki! Muma mun zo duba mai jiki ne ai" tayi shiru kanta a kasa, Anty Rahina kam bata tanka ba Hankalinta na ga shayar da dan jariri. Ta gama kame-kame dai ta tashi tazo ta zuba abinci ta fara ci, Kai kawai nake girgizawa, rayuwar Auren bayin Allahn nan tana da matukar daure kai. Ita ta fara tashi daga kan dinning din, sai dai wannan karon maimakon ta koma dakinta, kan daya daga cikin kujerun falon ta koma ta zauna. Muma muna gama cin abincin na kwashi kayan da muka bata na kai kicin na sake dawowa falon, Baby Jameel kamar yadda nake kiranshi tunda suka shigo na amsa daga hannun maman shi, yaron ya bude idanunshi farare tas Mashaa Allah dasu yana ta walainiya dasu a tsakiyar falon, Ji nake kamar in lashe shi saboda yadda yake burge ni. Na fara jujjuya shi ina jan kumatun shi ina mishi en wasanni kafin na fara manna mishi kisses a kumatu, Abbu ya maida kanshi jikin kujera ya kwantar idanunshi a lumshe; "What he'll pay to become that baby!!".

*♡Jeedderh♡*
[11/21, 10:25] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*15*

*'In a nation where the Poor face hardships, suffering and fears, only the riches and the one's that has power lives in peace, thrives and prospers....... Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ya Ibaadullaheessaaliheen!!!......'*

Sai gab da Magriba su Anty Ameenah suka mana sallama zasu tafi, na leka dakin Anty Mubeenah wadda tunda aka kira sallar la'asar ta tashi da niyar zuwa tayi sallah bata dawo ba, na gaya mata zasu tafi ta leko suka yi sallama ta koma dakinta. Ni dasu Hafsy har Abbu mai kafa sai da muka taka musu har gaban motar da Anty Rahina tazo da ita. Anty Ameenah ta kalleni na goya baby Jameel a bayana yana ta shakar barci abin shi, tayi murmushi cike da tsokana tace "to Hajiya Nafee a bamu baby din koh?" na fara kokarin sauke yaron daga bayana, "Allah Anty ji nake kamar ku bar min shi!" su duka suka kwashe da dariya, Anty Raliya tace "kina son yara ne har haka?" nayi dan murmushi, "sosai ma! Amma mommy taki ta haifo mana wasu" na karasa ina pouting kamar inyi kuka dana tuno diramar da muke sha da ita idan ina mata maganar me yasa bata kara haihuwa daga kaina ba? Sai tace ai Allah ne bai kawo ba, ranar nan ma dana takura mata da tambaya zagi ta dankara min tace in cewa daddy na ya karo aure mana sai a Haifa min yaran, na tuna lokacin kuka na fashe dashi saboda zagin data min, shi kuwa daddy dariya ya dinga mana. Daga ranar ban kara mata korafi ba, sai dai in yiwa daddy. Su Anty Ameenah kam dariya suke min, sun fahimci tsantsan yarinta da sokancin da aka san Yaya irinmu nayi a tare dani. Anty Ameenah tace "Kar ki damu, in shaa Allah kema zaki haifi naki, kinga kin huta kenan koh?" na gyada kaina ina murmushi, "daddy ma haka yace ranar nan!" suka kara sakin dariya kafin suka shiga motar, na mikawa Anty Ameenah babyn tare da maida murfin motar na rufe mata tare da daga musu hannu, suka ja motar suka tafi. Na dan saci kallon Abbu kallona yake sosai with astonishment in his eyes, murmushi yake yi kamar kunnen shi zai zage, na samu kaina da tambayar dalilin sudden change dinshi curiously. Na kama hannun Hafsy muka koma cikin gida ya biyomu a baya. Muna gama dinner na musu sai da safe na koma dakina, sosai nake jina a gajiye ga wani barci daya rufe min idanu.
Chapter 15 · 0% Book details