← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 88

Sashe 50

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Muna fitowa daga lectures masallaci na shiga nayi sallar La'asar daga nan na wuce flower Garden. Anty Ameenah tana zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada, tana hangoni ta fara waving dina tana murmushi, nima murmushin nayi na karasa gareta, kujera naja na zauna ina fuskantar ta, na gaisheta ta amsa tana tambayata abinda nake so a kawo min nace a bani egg roll da lemu don tun safe da zan fita dana sha shayi ban kara komi a cikin cikina ba, aka kawo mana egg roll, meat pie burger da lemun peach. Anty ta kalleni tace "Allah yasa ban takura miki ba da nace ina son ganin ki?" nayi saurin girgiza mata kai, "haba ko kadan wallahi" tayi murmushi tare da gyara zamanta akan kujera, "da farko ban yi niyar sa baki ba akan maganar wannan sai dai ina ga lokaci yayi daya kamata in saka baki, ba shisshigi nake miki ba amma ina so inji inda maganar ku ta kwana?" na dubeta cikin mamaki, "Anty wace magana kenan?" tace "maganar ku da Ibrahim mana!" sai dana kusa zubdo da abinda nasa a bakina saboda maganar da naji cikin bazata. Ta miko min tissue na goge bakina tare da korawa da ruwa, Anty Ameenah tace "m sorry idan baki so hakan ba" kai kawai na girgiza mata, amma a kasan raina ina mitar me yasa don kawai Abbu yana son aurena sai kowa a cikin dangin sa ya sani? Kamar wadda take karanta mind dina, tace "kada fa kiyi zaton Ibrahim ne ya gaya min ko ya turo ni, bashi bane. Kwanakin baya dai ya taba neman shawarata akan cewa yana so ya aure ki, me nake gani? Naji dadin hakan sosai, wallahi abu ne wanda ya jima yana min amsa kuwwa a cikin kaina, tun ranar farko dana fara ganin ki Nafeesah na yiwa Ibrahim sha'awar kasancewar ki matar shi, sai dai sanin halin Ibrahim yasa na kame bakina nayi shiru. Ba tun yau ba nake mishi maganar kara aure amma sai ya wawantar da maganar, ba ni Kadai ba Hajiyar mu ma tayi nata kokarin ganin irin zaman da yake yi da matar shi but to no avail. Amma jin da kanshi yazo yana ce min yana sha'awar kara aure nasan cewa da gaske yake, Ibrahim baya nuna bukata akan abinda yasan baya so, musamman akan zancen nan Nafeesah, I've seen something different in him. To kuma tun daga lokacin har yanzu ban sake jin yayi magana game da hakan ba, last time dana mishi maganar ma sai ya sake wawantar da ita, ni kuma gaskiya na kasa mantawa da zancen shi yasa nace bari in tuntube ki da kaina inji" nayi shiru tare da sadda kaina kasa, ince me? Tunda ni a karan kaina ban san ya muke ciki ba. Anty Ameenah ta kamo hannuna ta rike cikin nata, "look Nafeesah! I am not trying to persuade you or something else.... I just.... I mean ina cikin eagerness nason ganin rayuwar kanina tayi haske, ya samu farin ciki da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren shi. It has been good thirteen years tun auren shi da Mubeenah, aure ne aka musu na zumunci, ita diyar wani abokin Alhajin mu ne. Tun daga auren su Ibrahim ya rasa farin cikin shi, he was young, amma bai dandani abinda matasa kamar shi suke dandana idan suka yi aure ba. Ya rasa jin dadin yarintar shi a wajen yarinyar da bata san darajar shi ba saboda kawai bata son shi. A matsayin Ibrahim na namiji ya hakura da auren dole din da aka mishi amma ita ta kasa hakura, a wajen Mubeenah ne kadai na karyata maganar bahaushe da yace duk kiyayyar da mace take wa namiji da sun fara haihuwa take dawowa so, a gareta kam sai kiyayyar ta koma har kan 'ya'yan shi. You wouldn't believe me Nafeesah, lokacin da ta samu cikin Abdullahi da kyar ta iya haifeshi, Allah ne kawai ya nufa zai zo duniya amma sai da tayi attempting din zubar da cikin sau biyu, haka aka zo aka sha dabi da cikin Qaseem, daga haihuwar Hafsat taje aka saka mata loop a cikinta ba tare da sani ko yardar Ibrahim ba. Bata dauke mu a tsiyar komi ba, sai mu hadu da Mubeenah a hanya idan ba dama ta gani ba ba zata mana magana ba, idan mu mun mata sai ta ga dama take amsawa. Babu yanda bamu yi da Ibrahim ba akan ya kara aure amma ya ki, yace baya so yaci amanar da marigayi mahaifin Mubeenah din ya bar mishi akan ya kula da ita da farin cikinta, shi a ganin shi cin amana ne idan ya kara aure. Haka Ibrahim ya rayu tsayin shekarun nan, ya danne farin cikin shi saboda matar da bata san yana yi ba, wadda bata appreciating dinshi da dangin sa har ma da 'ya'yan shi. Wallahi baki ji farin cikin da nayi ba lokacin da naji cewa ya shirya fitowa daga cikin ukubar daya sa kanshi a ciki ba, shi yasa kwata kwata naji na kasa yin hakuri in zuba ido ki kubuce masa Nafeesah" jikina gabadaya yayi sanyi, ban taba sanin cewa irin rayuwar da Abbu yayi ba kenan, koma yake kan yi. Anty Mubeenah kam wace irin mace ce? Anya akwai sauran mata irin ta a duniyar mu ta yanzu? Anty Ameenah ta shafa hannuna tace "kinyi shiru?? Baki son shi ne ko kuma ya miki tsufa??" na girgiza kaina ina dan murmushi, "ban taba mafarkin kasancewar wani mutum a matsayin mijina ba sai Abbu Anty" farin cikin dana hanga a cikin idanuwanta abun baya misaltuwa, na sadda kaina kasa cike da kunya ina jin kamar kasa ta tsage in shige. Tace "amma me yake hana ki cika burin ki?" nace "ina jin tsoron abinda zai je yazo ne, my mom seems to be strictly against it. Sannan ban san me zai je yazo ba a rayuwar auren Abbu da Anty ba, bana son abinda zai tarwatsa musu rayuwar auren su da kan iyalinshi" Anty tace "believe me Nafeesah! You are not. Allah kadai yasan iya ceton ran da zaki yi, wallahi babu abinda zai faru a rayuwar gidan Ibrahim sai ma farinciki dana san zai wanzu in shaa Allah, ke kadai ce wanda zaki iya yin wannan aikin saboda na tabbata Ibrahim yana son ki. This the first time in my life da naga Ibrahim wanting something very badly kamar ki, na tabbata idan ya rasa ki sauran rayuwar shi will be shattered to pieces. Naji dadin wannan lamarin sosai, ina tabbatar miki da cewa you are the perfect match for Ibrahim. You suits each other, na tabbatar da zai kula dake, zai so ki. Kada kiyi zaton saboda shi kanina ne wai nake koda shi, ba haka bane. Saboda na yarda da Ibrahim na kuma yarda da halayen shi. Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah babu abinda zai faru sai Alheri, in shaa Allah ba zaki taba yin nadamar Auren Ibrahim ba kamar yadda na tabbata zaki kasance a cikin farin ciki matukar kina amsa sunan Matar shi. So dear, stop holding yourself in and just go for it, kiyi abinda kike son yi kafin lokaci ya kure miki, Allah ya Albarkaci rayuwar ki" na sadda kaina kasa ina jin wani irin confidence da kwarin gwiwa yana shiga ta. In shaa Allah ba zan kara rike kaina ga yin abinda nake son yi ba, da yardar Allah zan zama mallakin Abbu tun kafin ya subuce daga hannuna ya sa in tagayyara. Anty Ameenah ta kara bani shawarwari kafin muka mike muka fita daga cikin garden din, har inda tayi parking din motar ta na raka ta. Ta bude motar ta shiga, ta mika hannunta baya ta dauko Leda mai dauke da tambarin kamfanin shop rite Ta miko min, naso nokewa in ki karba amma ya kamo hannuna ta dora min ledar a tafin hannu dole na karba tare da mata godiya, tace "babu komi Ameenah, and please make sure to make it very fast" na sunne kaina a kasa ita kuma ta tashi motar ta tafi.

Tarkacen kayan makulashe ne ta kawo min, dambun nama, cookies da tarkacen biscuits sai turare masu kamshi a cikin ledar. Na bude biscuit din short bread na kai bakina na cinye tare da korawa da lemu, kwana biyun nan abubuwan dana mayar abincin cina kenan. Bayan nayi sallahr Isha'i na gama shirin kwanciya, na kwanta akan gadona tare da janyo pillow na rungume a kirji na, Maganganun Anty Ameenah suka fara dawo min a cikin kaina. Na tsinci kaina cikin mutuwar jiki tare da jina ina narkewa akan katifar da nake kwance. Allah sarki Abbu! Ban taba zaton cewa rayuwar auren shi munin ta yayi yawa har haka ba, na kara juyawa a akan gadon. Poor Abbu! Da yardar Allah sai na zama dalilin sharewar hawayen shi da yayi ta zubarwa a shekarun baya, in Allah ya yarda sai na zama haske da fitila a cikin rayuwar Auren shi. Da haka na lumshe idanuna barci ya dauke ni, idanuwa brown masu sheki da kyalli suna gagari a cikin duhu.

*******
Chapter 50 · 0% Book details