← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 62

Sashe 9

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A uwargida Ni Kadai Zan tafi dai Su Zahira zasu Dan zauna su kwana biyu sabida wani Dan dalili dafatan Dan Allah ban takuraki ba" ?

"Haba Yaya wane irin takura Nan ma ai gidane karka wani damu"

Godiya Naseer yayi ta yiwa Murja.

Murja kuwa har da rike hannun Nadeeya suyi rakiya har waje.

Sai da suka daina hango su Tijjanin da suka hau Vespa Dan ya fita dashi titi

Murja naganin sun wuce ta yarfar da Hannun Nadeeya ta ja baya tare da musu wani irin Mugun kallo tana "Yan bura uba daga zuwanku sabida kwadayi zaku hau cinye min abincin Dana girka shegu dangin kwadayi zaku ci.ubanku ne Dani kuke maganar Haka kawai Ina zaman zamana a kwaso.min gayya Yaya har guda biyu Uwarku ma ta kasa rikeku ta gudu shine Ni aka rainawa wayo.zaa wani kawoku wajena shi Kuma Tijjanin zai Zo ya sameni Kuma wlh kun Gama cin rabonku"

Daga Haka ta wuce daki fuuu tana bakin cikin abincin ta da suka ci sosai ta ringa shirya ukubar da zatayi wa Yara da basuji ba Basu gani ba Wanda idan sukaji azaba da kafarsu zasu gudu.

Zahira kuwa kuka ta fara yi Nadeeya kuwa na kikifta Ido Zahira duk da kankantar shekarunta gani take Bayan mahaifiyarsu da mahaifinsu Babu Mai kaunarsu har suna murna zasu zauna a gidan baba Tijjani da suke ganin kamar sai sunfi jinn dadin zaman Nan Akan gidansu sai dai daga yanda Murja ta musu yasa Zahira taji dama sun bi Bayan mahaifinsu.

Tijjani kuwa Yana fita da Naseer bakin titi ya d'auko duk kudin jikinsa ya bashi ya kara Masa alkawarin idan ya samu sarari zai Zo idan sukayi albashi.

Godiya Naseer ya Masa sosai ya tari bus da zai je gadon Kaya ya hau

Tijjani Kuma ya juya ya koma gida

Murja tana Jin karar vespa ta duro daga Kan gado tayi waje tayi wajen da su Zahira ke rab'e ta ruk'o hannun su biyun a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da vespa ya Parker

Murja kuwa ta hau cewa "kaga tunda kuka tafi nake fama dasu akan su shigo Suka k'i wanan kamar wata karamar Yarinya har da kukanta Wai sai tabi bayan Abbanta"

Fa karashe tana nuna Zahira

"Kukan me kike Yi Zahira bakya San ki zauna damu"?

Tijjani yace a daidai lokacin da ya karasa wajensu Yana ruk'o hannun Zahira

Girgiza Masa Kai Zahira tayi Murja kuwa ya harareta a fakaice sosai take ganin kamar Zahira munafinci ne yasa take kukan sabida ta hadata fada da Tijjanin.

Dan duk da kame Mata Tijjani da mahaifiyarta tayi wani zubin inya tashi sai ya botse Mata.

Cikin palon suka Shiga Tijjani ya zauna akan kujera Ya zaunar da Nadeeya a gefensa ya kalli Murja Yana "Dan Allah Kara Dora Mana wani abincin yunwa nakeji wlh"

"Wlh na dazu ma dakyar na dafa ko dandanawa banyi ba ka bawa yaran Nan da babansu"

"Toh sai nak'i Basu Murja wane irin magana kike Haka yayana na bawa abincin fa ke Mai yasa kike haka ne Mai da anzo wajenka ka bada abinci anci gaskiya ki gyara halinki Bari nayi Sallah na Shiga da kaina na dafa abincin

Daga Haka ya mik'e ya shige dakin
Murja ta bishi da wani irin kallo ta maido kallonta kansu Zahira datake ji kamar ta jawosu ta rufesu da duka

Ahaka ta daure tayi waje ta Dora musu jollof din taliya tana zagin Naseer da yayansa da take ganin sun zo sun takura Mata.

Taliyar kad'an ta dafa duk da basu da matsalar kayan abinci sabida su kadai ne Murja kuwa rowa bazai Bari ma ta dafa abincin da yawa ba ballantana har ya ragu su bawa almajiri.

A plate ta juyo musu abincin Dan tare suke ci

A Palo ta tarar da Tijjani dasu Zahira Yana ta jansu da Hira sabida su saki jikinsu sai dariya yake kyalkyalewa Dan Nadeeya sosai ta zage take Masa surutu ita kuwa Zahira da Bata da surutun murmushi kawai take.

Murja kamar ta fashe Dan bakin ciki tsabar jahilci ma kishi ne ya rufeta data ga yanda Tijjani ke kyalkyala dariya a Haka ta ajiye taliya ta zauna a gefensa zahira tayi saurin barin kujeran.

Nadeeya kuwa ko a jikinta

"Ina abincin su Nadeeya Naga kin zubo Mana mu kadai"?

"Ai Naga sunci abinci shiyasa ban dafa dasu ba ga saura can ma na Kai kitchen"

"Zahira kin koshi Wai"?

Da Sauri ta gyada tare da sunkuyar kai kasa sabida mugun kallon da
Murja ke jifanta dashi

"Nadeeya ke Kuma fa kin koshi"?

Girgiza masa Kai Nadeeya tayi

Shi kuwa yace toh shikenan Bari muci gabad'aya jeki wanke hannunki

Waje Nadeeya tayi da Sauri

Ta wanko hannunta Suka fara cin abincin
Murja kuwa tusa abinci kawai take Dan bakinciki ji take kamar ta shake Nadeeya
A takaice Tijjani da kansa yayiwa Su Zahira shimfida har da Kai musu bargonsa ya musu adduar kwanciya bacci tare da ja musu k'ofar

Murja kuwa tsabar bakin Hali Kamar ta fashe da kuka Dan gani take Tijjani Dan tattalata da yake yi daga zuwansu Nadeeya ya shareta.

Rai ba dadi Haka ta kwana tana Shan mugayen alwashi aranta

Naseer kuwa sai daya yi sallah ishai ya karasa gida

A k'ofar gida ya tarar da Hajara ita da Safiyya sunyi jugum jugum sai kalle kalle suke

Safiyya kuwa Tana hango Naseer ta diba da gudu tayi ciki

Hajara kuwa duk da jikinta rawa yake sabida tsoro Mai zata cewa Naseer game dasu Zahira da Basu dawo ba ahaka ta maze Yana isowa gabanta ya gaisheta Yana k'ok'arin Shiga gidan kamar Bai San komai ba

Hajara kuwa kamar ta Dora hannu a ka Shigar Naseer da Yan mintuna ya fito waje

Ya kalli Hajara datayi tsuru tsuru Amma tsabar karfin hali ta daura fuska

"Umma inasu Zahira ne ko kin aikesu"

"Aaaa eee kana ji wlh talaucin Nan da muke fama dashine ya isheni shine na Nemo kudi na d'afa abinci da suka dawo na dorawa Zahira da Nadeeya akan su kaimin bakin titi su dawo sabida ma mu samu abincin da zamu ci daddare.

Wlh tun uku Suka fita har yanzu basu dawo ba naje titi nida Safiyya yafi sau biyar ko Mai kama dasu bangani ba ba Inda ban dubasu ba a unguwar Nan wlh ban gansu ba yanzu ma Haka daka ganmu a k'ofar gida wlh daga nemansu muke

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma talla Kika dorawa Zahira da Nadeeya kinsan kuwa akwai Yan yankan Kai a garin Nan Umma Kar fa masu satar mutane ne ne fa suka sacemun Yaya Umma Akan me Zaki Dora musu talla haba Umma kema kinsan idan na dawo ko ba yawa Zan taho Mana da abinda zamuci irin Haka nake gudu tun farko shiyasa naki Bari a Dora musu talla yanzu daga Ina Zan fara ta Ina Zan soma neman su Umma"?

"Insha Allahu baa sacesu akayi ba abincin dari takwas fa na Dora musu da hamsin"

"Umma ta abinci kike ko yarana Umma ta kudinki kike ko yarana Ina Miki zancen yarana kila sun b'ata kina min zancen abincin dari takwas Kika dora musu"

A takaice sosai Naseer ya tashi hankalinsa kamar gaske baiyi bacci ba Bai Bari Hajara tayi ba Dan itama sosai hankalinta ya tashi da rashin dawowarsu zahiran.

Tana ta bakin cikin asarar da tayi kasan zuciyata Kuma tana addua Allah yasa ba sacesu akayi ba.

Abinda suke turarawa shugaba ta bayyana kuwa sun nemeshi sama ko kasa sun rasa ballantana tasa shugabarsu ta gano Mata Inda suke.

Ahaka washegari Naseer ya bar gidan da wuri Akan ya tafi neman su Nadeeya

Bai damu da tsayawa ya bawa su Minal abinci ba Dan ya karanci a yaran nasa tafi San Minal Humaira da Raheema har abinci tana ragewa ta basu idan taci duk da Minal na musu rashin kunya wani zubin hakan Bai saka ta wani tsaneta ba.

Zahira ma ta tsaneta ne sabida balain Kama dataga tanayi da Naeema

Hankali ba a kwance ba Haka Hajara ta shirya su Minal suka tafi makaranta bayan sunci abinci.

Tijjani kuwa karfe shidda yake barin gida hakane yasa Yana dawowa daga Massallaci yayi wanka ya shirya ya kalli Murja dake Kan sallaya Yana "Zan fita Zahira da Nadeeya Basu tashi daga bacci ba Dan Allah Dan annabi ki Basu abinci suci su koshi Dan Allah nace Miki karki damu da Wai Dan kin bayar zai Kare wlh Zan Kara siyo wasu yaran Nan Kinga amanarsu yayana ya bani Dan Allah ki Tayani kula dasu kinji"

"Wai toh Mai ya kawo maganganun Nan baka yarda Dani bane Akan me Zan k'i Basu abinci bana San Haka wlh"

"Allah ya baki hakuri ba Haka nake nufi ba Bari na tafi sai na dawo Mai Zan taho miki dashi"?

"Ayaba kawai nake shaawa"
"Toh shikenan sai na dawo"

Daga Haka ya fito daga d'akin ya lek'a d'akinsu Zahira da har lokacin suke sharar bacci.

Har waje Murja ta rakashi sai data daina hango shi ta rufe gidan.

Direct ta Shiga kitchen ta bud'e karamin fridge ta d'auko karamin bokitin fenti dake cike da ruwan da ya fara Dan kankara.

Tayi d'akin dasu Zahira suke kwance
Sai data janye bargon da suka lulluba sabida Dan sanyin da suke ji ta daga robar sama ta watsa musu.

Wani irin ihu Suka saa Suka mik'e a gigice sabida yanda ruwn sanyin ya ratsa su

"Shegu Yan bura uba dole kuyi ta sharar bacci ku ga gidan ubanku maza ki fita waje kuje ku dau tsintsiyarku ku sharemin ko'ina kumin wanke wanke yanzu Nan ku Shiga d'akina kuzo ku gyara min"

Daga Haka tayi waje tana cigaba da danna musu Ashar.

Zahira da Nadeeya kuwa Suka kankame jikinsu suna rawar sanyi kayansu sai digar ruwa yake ahaka suka fito Suka daura alwala da jikakken kayan sukayi sallah suna ta rawar sanyi Zahira kuwa har da kukanta Dan Abu kad'an ke sakata kuka

Cikin awa daya Suka Gama aikin da Murja ta saka su dan gyara gida Kam sun Riga da sun Saba Koda Bata saka su ba zasuyi.
Chapter 9 · 0% Book details