← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 62

Sashe 16

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Haka ya saka kayan aikinsa suka hau aikin ginin.

Nadeeya nadaga inuwa tana surutai har ta Saba da Yan aikin wajen wani ya siya Mata shinkafa da miya har da nama surutunta da manyance ta yasa tayi farinjini akayi ta Mata siye siye tana Jin dadi Dan inda tafi kwarewa kenan

Ahaka wani Abba magini da gidansa ke kusa da wajen da suke aiki ya Dan hau tambayar Naseer dalilin dayasa yazo da Nadeeya wajen.

Shi kuwa yace Masa ba kowa a gidan ne iyalinsa sunyi tafiya shiyasa ya taho da ita Dan mak'otan nasa Basu fiye shiri ba.

Take shi kuwa Abban yace Mai zai Hana idan sunzo ta ringa Shiga gidansa idan sun tashi Kuma sai su koma gida tare.

Sosai Naseer Yaji dadin maganar Abba Dan Dama Yana ta tunanin Inda zai na Kai Nadeeya Dan Sam Baya San barinta a gida makaranta ne dai sai ya samu kudi zai saka ta islamiyya Kuma zai nema anan din har uniform ya Dinka Mata ta ringa zuwa Wanda yaran Abban ke zuwa.

Sai da suka Gama aikin Suka koma gida Naseer ya Dan siya musu kayan shayi ya tafar musu dashi.

A tsakar gida ya samu Safiyya taci uban kwalliya tana zance da wani.

Shi kam ya gaji da kwashe kwashen da Safiyya ke Masa a gida hakane yasa ya Isa wajensu Ransa a had'e ko amsa gaisuwar da suke Masa baiyi ba

Naseer yace Masa "idan dagaske kake kana San ka Aureta ka turo magabatanka"

"Dama yau tacemin na maka magana Dan inaso na turo magabatan nawa sai Kuma fad'uwa tazo daidai da Zama acan garin da dangin mahaifinta yake anan nake aiki.

Inada Mata daya da Yara shidda

"Zanje jibi insha Allahu mu tsayar da Magana Dan Nan da wata biyu nakeso ayi bikin namu"

"Allah ya yarda"

Kawai Naseer yace Dan har ga Allah gani yake Safiyya ta na cikin wayanda suke Masa Karen tsaye a rayuwarsa shiyasan ita ke saka Umma yin wani Abun.

A ranar Nadeeya ce ta ringa deb'e Masa kewa da surutanta ya hada da Bata tarihi annabi Yusuf Dan surutan nata ma ba wani Kan gadone dashi ba hakane yasa ya hau Bata tarihin Annabi Yusuf ta kuwa nustu tana ji ahaka har bacci ya d'auketa shima ya d'aura alwala Yana iddar da shafai da wutr ya d'auko Quraninsa Dan ya karanta.

Hajara ta fado d'akin kamar an hankadota.

A Gefen katifa ta zauna tana "Kai Naseeru dazu naji kana cewa saurayin Safiyya ya turo da fatan ka tanadi kudin da zaka Mata kayan daki Dan kasan banida ko sisi ban Kuma bawa wani ajiya ba".
"Banida ko sisi Umma Nima ban bawa kowa ajiya ba idan sun turo taje wajen dangin mahaifinta su harhada kudi su Mata kayan daki kamar yanda sukayi wa Lami Umma Nima ta kaina nake bazan iya zuwa nayi sata ba"

"Ai nasan da dangin mahaifin nata nace ka Mata kayan d'akin Dan ko Lami da iya katifa aka kaita har gobe Gori ake Mata ita kuwa Safiyya tana da kishiya Dole ayi Mata kayan daki "

Naseer Bai ce Mata komai ba ta Gama surutanta ta tafi.

Murja kuwa tana komawa gida ta fara tunanin hanyar da zata bi batare da Tijjani ya zarge ta ba Dan tasan Ransa sai ya b'aci idan yaji Mai tayi Su Hajara kuwa bashi suka dauka sai ta Rama abinda suka Mata idan ta samu ta Shawo Kan matasalar daya kunno mata Kai Sosai ta ringa tsinewa Nadeeya da Zahira tana Jin inama taga Nadeeya a gabanta da ba abinda zai Hana ta shaketa har lahira.

Bata San Mai yasa duk kamun da take wa Tijjani baya kamuwa ba tsinanen taurin Kai ne dashi ta Rasa dalili ballantana ta Mallakeshi Wai a Haka ma Mahaifiyarta tayi aiki babba akansa.

Daba haka ba da tuni ya saketa Dan bashida mutunci ko kad'an daga aurensu zuwa yanzu ya Mareta ya Kai sau uku gashi ita Kuma balain San shi take.

Ahaka ta zauna a gidan cike da fargaba dawowar Tijjani duk da ta gama.hada makircin da zatayi idan ya dawo.

Karfe shidda taji karar vespa dinsa.
Tayi sauri.ta zauna a tsakar gidan kafarta a kumbure Yana kyalli Dan ta kware a kumbura jikinta da wani hoda da Mahaifiyata ta Bata sai numfarfashi take idonta ya kad'a yayi.jawur

Abinda ya Bata mamaki Bai wuce yanda taji har lokacin Bai shigo ba hakane yasa ta lek'a cikin sand'a Inda kuwa ta hango Tijjani a tsaye ya Kama kugu Jamilu Mai shago nata kwara Masa bayani.
Gabanta ne ya yanke ya Fadi a lokacin data ga Tijjani idonsa ya kad'a yayi jajir sunyi musabiha da jamilun ya nufo gidan

Ita kuwa Murja cikin tashin hankali ta Shiga palo da sauri ta zauna jikinta na Dan rawar tsoro tana tunanin hanyar da zata Kare kanta

Daga yanda ya bugo k'ofar hantar cikinta ya kad'a

Ta daure ta mik'a kafarta tana ta adduar Allah ya dorata akansa.

Wani irin kallo ya hau jifanta dashi daya shigo cikin wani irin murya yace "Ina zahira da Nadeeya"?

Kuka ta fashe dashi ta Kara Mika kafarta daya suntume Yana kyalli ta hau cewa "Kaga k'afata wlh a garin na bisu nayi tarkade Nazo Zan Shiga wanka naji mmn Hafsa ta shigo aguje tacemin gasu can zasu gudu kwana uku kenan suna cewa zasu gudu wlh a garin nabi bayansu na Fadi har bugewa nayi a cikina"

Ta karashe tana fashewa da kuka

Tijjani kuwa ya karasa wajenta Yana "Muga kafar ya sunkuya ita kuwa cikin makirci ta Kara mika kafarta tana cigaba da kuka Tijjani kuwa Yi yayi kamar zai duba kafarta aikuwa ya zaro belt ya hau tafkarta tana daga zaune.......
[7/8, 10:57 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 42*

Sosai.ya ringa tafka Mata belt din Yana soka Mata Ashar sai daya Mata lilis ya koma gefe Yana "Maza tashi ki tafi gidanku shegiya makira na tsaneki wlh Allah na tsani mutum munafiki Ashe tunda na kawo yaran Nan Haka kike azabtar dasu ba iya jamilu ne ya tareni ya gayamin ba har Mallam Ashiru wajen aikina yaje ya sameni ya gayamin Ina dawowa shima jamilu ya tareni da zancen ke wacce irin muguwa ce kina d'auke da ciki a madadin ki ringa addua Allah ya saukeki lafiya aa sai Kika saka mugunta agaba kina zalintar yaran da basuji Basu gani ba shegiya munafika Mai fuska biyu Maza tashi ki barmin gida.

Tijjani yace a fusace ya ruk'o hannunta ya fara janta da kasa ita kuwa sai numfarfashi take tana Magiyar yayi hakuri sharrin shaidan ne Bai saurareta ba sai daya kaita har waje.

Ya watsar da ita ya koma ciki ya cillo Mata takalminta da mayafinta.

Ya kulle gidan ya danne vesparsa tare da bada Mata k'asa.

Sai data daina hango vesparsa ta mik'e dak'yar tana cije lebb'e sabida yanda jikinta ke balain rad'adi ko ta ina sabida ba karamin Jibga ya Mata ba.

Gidan dake jikin gidansu ta shiga ko Sallama babu

A tsakar gida ta tarar da matar gidan na zaune a Kan tabarma tana yiwa yarta kitso Mallam Ashiru Kuma na zaune akan kujera Yar tsugunno da buta agabansa da alama jira yake a Kira sallah yayi alwala.

"Lafiya Kika shigo Mana ba Sallama "

Dalla rufe min Baki Dan ba wajenki Nazo ba wajen wanan Dan iskan Mai dogon wuyan Nazo wato sabida munafinci shine kaje ka samu mijina kace Ina zalintar yaran da aka kawomin Ina ruwanka da rayuwata da ina ruwanka da abinda nakeyi shege munafiki tsinane kaji da matsalolin da ke gabanka Mana na me sai ka Shiga abinda Bai shafeka ba toh burinka ya cika ya ce na tafi gida wlh Allah kayi addua Kar munafirci da kayi ya zama sanadin mutuwar aurena Dan wlh idan Aurena ya mutu zakayi mamakin abinda Zan maka sai ka gwammace ma da baka sani ba"

Daga Mallam Ashiru har matar tasa ba Wanda ya iya magana har ta juya ta tafi.

"Sai Dana Gaya maka ba ruwanka Dan matar Nan wlh ba mutunci ne da ita ba kaf unguwar Nan ba Wanda take muamalla arziki dashi ba Mai Shiga harkarta sabida mugun halinta Amma gashi"

"Dalla kirufemun Baki Taya zakice Kar na Gaya masa tana zalintar yaran daya kawo gidanan ke kanki anan kin Sha kukan tausayin yaran idan kika jiyo tana jibgarsu aikin kenan Haka zatayi ta zaginsu tana duka Akan me bazan Gaya masa ba sabida yayi wa tufkar hanci kafin ta Kai ga tayi kissan Kai yanzu Dana fada Masa bashine ya sani ya dau mataki ba"

"Allah ya kyauta"

Kawai matarsa ta iya cewa

Shi kuwa yaja Tsaki Yana Dan Jin sanyi a Ransa Dan sosai yake tausayin Su Zahira idan Yana jiyo irin bugun da take musu Badai tab'a yiwa su Zahira magana bane.

Murja kuwa tana fitowa daga gidan

Shagon Jamilu ta tsaya sukayi ta zagin Juna tana rantsuwar sai taga bayansa tunda ya hadata da mijinta shima rantsuwa yake akan ba Abunda zata iya Masa Dan Kar yake kallonta idan takamarta uwarta matsafiya ce zata Masa wani Abu ta gwada ta gani wlh sai ya kawo karshenu shima ai ba Haka yake zaune ba"

Murja kasa magana tayi sabida mamaki yanda Jamilun yasan Mahaifiyarta matsafiya ce ba ta iya Kara magana ba ta fice daga shagon tana cigaba da Shan alwashin sai ta ga karshen Jamilun.

Tana Isa gida ta zub'e a tsakiyar palon nasu ta hau kuka.

Mahaifiyarta Rabi ido ta zuba Mata Bata ce Mata komai ba.

Sai da Murja ta gaji Dan kanta ta bud'e baki da zumar Mata magana Rabi ta daga Mata hannu fuskarta hade tana "Ba sai kin gayamin komai ba Naga duk abinda ya faru dazu kawai na dauko tukunya ta Dan na duba halin da kike ciki Naga Yana ta jibgarki ai sabida Dan iska ne shi bashida mutunci Bai ga cikinsa da kike d'auke dashi ba yayi ta dukanki ai ba jaka na aura masa ba Amma ba komai yyi na farko yayi na karshe shi da ganin Haske sai dai a lahira"

Rabi tace Tana k'ok'arin mik'ewa
Chapter 16 · 0% Book details