Sashe 18
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mahaifiyarmu ce fa Tijjani idan na siyar da gidan na gudu a Ina zata zauna Naga basa shiri da matarka balle nace gidanka zata dawo bama Zan Sam kwanciyar hankali ba idan Naga tana garari"
"Toh naji yanzu dai abinda zaayi kayi k'ok'ari ka nemi Inda Naeema take ka ringa zuwa kana dubasu Koda baka Kai musu komai ba yaranka su ringa ganinka Suma suna Jin dadin kaima sanin halin da suke ciki zai saka ka Dan samu kwanciyar hankali Sanan Nadeeya gaskiya gwara ka maidata wajen Naeema Sabida daga Kai har Naeema sai kunfi samun kwanciyar hankali bazai yiwu ka ringa fita kullum da ita sai kace namiji ba ke Nadeeya ki Bari Abbanki ya maidaki wajen ummanku shima Nan zai dawo idan an kwana biyu"
Nok'ewa tayi Tijjani ya hau rarrashinta da Mata alkawarin siya Mata kaza da nama take ta hau washe baki tace ta yarda.
Tijjani kuwa yacewa Naseer yayi kokari yasan Inda su Naeema suka koma Bauchin ne ko Kano ya maida Nadeeya ya Kuma ringa lek'a su akai akai.
Naseer godiya ya Masa sosai Yana Jin dadin shawarar Tijjani Dan kwana biyun Nan sosai ya ji Yana k'ewan Naeema.
Har kyautar kudi Tijjani ya bashi kafin ya tafin
Naeema
Washegari da safe na bazama nemowa yarana makaranta Mai Dan saukin kudi.
Dan Zahira Naga ta tsayi Tama Zama budurwa tunda a yau na wayi gari Naga period ya zo mata boye boye ta ringa min duk da ciwon marra da take fama dashi Amma kasancewar waje daya muka kwana yasa nasan halin da take ciki.
Zaunar da ita nayi na Bata ilimin Shi kansa haila banji kunyar ta ba na fada Mata komai da yanda zatayi wanka idan jinin ya d'auke har yanda zata tsaftace jikinta da Kuma Kara kame Kanta daga wasa da maza
Daidai da kuzungu ma Ni na koya Mata yanda zata saka Dana saka tayi wanka ta wanke zanin data b'ata sai wani sunne Kai take Wai kunya ta takeji.
Ni kuwa a Raina ma mamakine nake yaushe har nayi auren wai Yar cikina ta fara period kila kwanan Nan ma naga ana Sallama da ita Akan Ana Santa.
Hakane yasa Dana karya na bazama nemo makaranta Dan so nake ma ta fara secondary daga jss 1
Wani karamin makaranta na samu Mai Dan saukin kudi.
Sai dai ba secondary sch Wai sai dai ta zanna common entrance tunda baifi saura sati biyu a zanna ba samun secondary bazaiyi wahala ba indai ta zanna common entrance din.
Sai Dana koma gida na tafi dasu Zahiran gabadayansu sabida tace zata musu gwaji sabida tasan ajin dazata saka su.
Ba laifi yaran nawa na da Dan kokari duk da akwai slow learner's a cikinsu kasancewa na biya duk kudin da aka bukata har na uniform text books kawai Zan siya musu littattafai Kuma inadashi a shago
Nadeeya ce kawai nace mata Zan kawota Bata Nan ne ta bani uniform dinta na tafi dashi yarana kuwa kamar Wasa Naga sun shige aji.
Zahira Kuma ta wuce primary 5
Cikin farinciki na dawo gida
Na dau littattafai dozen uku da fensura na bawa Isihu ya Kai musu da biscuit ya zama Dole na dauko Nadeeya Dan nasan Bai Zama lailai Naseer ya samu kudin sakata a makaranta ba.
Safiyya
Kwana biyu da maganar da Naseer yayi wa Saurayinta Umar akan ya tura neman aurenta.
Yaje har garin calabar ya nemi kanin mahaifinsu ya gabatar da kansa dayake a shirye yake har Sadaki ya bayar Dan sosai kwallin da Safiyya ke sawa ya rikita shi yaji idan Bai Aureta ba bazai samu nutsuwa ba.
Anan garin calabar yake zaune da matarsa Hafsa da yayansa.
Matarsa macece Mai balain kishi masifafiya a unguwarsu kowa yasanta shegen bin Mallamai ne da ita dan wanann bashine Karo na farko da yake neman aure tana wargazawa.ba Har mallake Umar din tayi sai yanda tayi dashi.
Karfin kwallin tsafine yyi tasiri a wajen Umar din ya kamu da San safiyya dayazo.kano.wajen abokinsa da Safiyya ke aiki a gidansa.
Ita kuwa Tana ganin Yana da Dan canji yasa tana dawowa gida ta hargitsa d'akinsu har sai data samo kwallin daya shiga rububi ta rambada kwallin a idonta ta koma.da.sauri tana adduar Allah yasa Bai tafi ba
Tana kuwa zuwa taci Karo dashi a bakin kofa yazo fitowa daga wanan hada.idon Umar ya kamu da San Safiyya.
Kwana uku yayi a Calabar ya dawo ya sanar da Safiyya duk yanda sukayi da kanin mahaifinta Nan da wata Mai zuwa zaa daura aurensu.
Safiyya sosai hankalinta ya tashi dataji wata guda kanin mahaifinta yasa Dan tasan Basu tanadi komai ba
Hakane yasa Yana tafiya ta sako Hajara da maganar kayan dakin da za Mata harda kukanta.
Akan Hajara tasan yanda zatayi da ita Dan Bata San kishiyar ta ta rainata tunda Umar yace a gida daya zasu zauna.
Hakane yasa Hajara itama ta Sako Naseer agaba da maganar kayan dakin
Har fargabar dawowa gida yake Dan shi Dan kudin da yake tarawa so yake idan ya tashi zuwa gidan Naeema ya Dan yiwa yaransa siyayya Kar ya tafi haka hannu na dukan cinya
Dan ya je har gidan Alaramma ya tambayi matarsa ta Masa kwatance Gidan da Naeema sosai yaji dadi da Naeema ta zauna a kano bataje garinsu ba da yasan ma Tana garin Kano Nan kusa dashi da tuni ya nemeta.
Hakane yasa ya Tara kudadensa da zumar yiwa su Zahira siyayya har Naeema ma sai ya siya Mata wani Abun.
Rabin kudin kuwa Dama Waleed zai kashewa Dan yayi kewarsa sosai shima
Gobe ya ke Shirin siyayyan daga wajen aiki ya shirya shi da Nadeeya su wuce Yana shigowa gida ko palon Bai Kai ga shiga ba Hajara ta tare shi da maganar kayan dakin Safiyya.
Baya San wani Abu ya dameshi sabida farinciki da yake ciki
Cewa Hajara kawai yayi toh zai nema suka shige shi da Nadeeya
Ta kaiwa Nadeeya rankwashi akan Bata gaisheta ba ta hau bambamin Kar ya Kara fita da Nadeeya Bata San iskanci idan Nadeeya ta zauna ta tayata aikace aikacen gida laifine.?
Naseer Bai dai tanka mata ba ya d'aura alwala ya tafi massallaci sallah Magriba
Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi sallah Isha ya tsaya a shago ya Dan Yi aski.
Daga nan ya Kara sa Bakin titi yayi siyayar da duk zaiyi a wani shago Dan da safe yake San suje wajen Naeema.
A shagon ya bar kayan akan gobe idan zai wuce zai dauka.
Ya dawo gida ya tarar da Safiyya tasa Nadeeya ta wanke Mata Kaya tana ganin ya shigo ta hau zunduma kuka
Sabida har Dan zaneta sai da Safiyya tayi.
Naseer kuwa a fusace ya Shiga har d'akin Safiyya ta buya a bayan Hajara
Naseer kuwa hakan Bai hana ya cire belt ya tsula Mata ba
Hajara sai Masifa take akan me zai daketa Dan ta daki Nadeeya ai Nadeeya Bata da kunya ne.
Haka ya fito daga d'akin Ransa a bace
Ya rik'e hannun Nadeeya sukayi d'akinsa.
Nadeeya kuwa ta hau ce Masa ya Kai ta wajen Umma Aunty dukanta takeyi.
Murmushin Naseer yayi yana ",Kin fasa Zama a wajena"?
Gyada Masa Kai tayi ya saki dariya Yana "daga aunty ta dakeki shine Zaki gudu ki barni"
Kara gyada masa Kai tayi tana ita dai ya kaita wajen Umma.
Naeema
Sosai naji dadin makarantar da yarana ke zuwa da alamu Kuma suna Gane abinda ake koya musun
Har islamiyya na Nemo musu idan suka dawo daga Boko sai su wuce sai karfe shidda suke dawowa.
A yau ma bayan na rakasu har makaranta gida na dawo na gyara ko'ina Hassana Bata Nan ta tafi bikin Yan uwansu Nima sai anjima Zan je idan yarana sun dawo daga makaranta Dan yau ba islamiyya.
Isihune keta markaden.
Ni Kuma duk abinda aka zo siya Zan fita da kaina na bayar dayake na fitar da kofa ta cikin gida.
Gidan na gyara na Dora ruwan tea Dan nida Isihu bamu karya ba
Zobon Dana hada na kukula na zuba a kula na Kai bakin shago Dan Sana'ar zobon shima ya karbeni alhamdulillah duk da Ina siyar da lemon kwalba
Duk Sana'ar Dana Dan gwada Allah Yana Sanyamin albarka
Zuwa yanzu engine markaden nawa ma biyune
Har kujeru masu Dan saukin kudi na saka Mana a gidan
Isihu na mikawa shayinsa ya fita shago
Ni Kuma na koma ciki na Shiga wanka Dan nasan kafin na fito shayin ya Dan hucce.
A band'akin d'akina na Shiga wankan Ina fitowa Naga Naseer a zaune a Gefen gadona Waleed rik'e a hannunsa.
Wani irin ihu na kwalla na koma band'akin aguje Dan gani nake gamo nayi idona yake ganemin Kamar Naseer na gani..............
*AYIMIN HAKURI BANJI DADI BANE JIYA SHIYASA AKA JINI SHIRU SHEKARANJIYA KUMA AIKI NAYI NAGAJI SHIYASA BANYI POSTING BA INA MASOYAN SADNAF TRUE LOVERS NGD DA KAUNARKU A GARENI KU DIN MASOYANA NE NA HAKIKA BAZAN MANTA ALHERIN KU A GARENI BA ALLAH YASAKA DA ALJANNATUL FIRDAUSI YA BAR ZUMUNCI*
*WANAN SHAFIN NAKINE UMMA YAHAYA MUSA NGD DA KAUNARKI A GARENI MAI KAUNARKA SHI ZAIYI TUNANIN KYAUTATA MAKA ALLAH YA FARANTA MIKI NGD*
*NAGA TA KAINA GRP 1 KUN NUNA MIN KAUNA KUMA NGD SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI*
*SAKON GAISUWA GA DUK MASOYANA*
[7/9, 10:40 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 43*
Muryar Nadeeya dake dariya tana Umma mune fa
Yasa kirjina ya bar buguwa na sauke ajiyar zuciya na bud'e k'ofar Ina mamakin yanda suka Gane gidan.
Nadeeya ma Sam ban lura da ita ba
Ko kadan ban sa Rai da zuwan Naseer gidana kurkusa ba
Ban kalli B'arin dayake ba na fito
Nadeeya dake zaune dirshan a kasan d'akina na nufa kofin shayin Dana ajiye da zumar na Sha shine a hannunta,
Gaisheni Nadeeya ta hau Yi
Ni kuwa nace "Yar babanta Mai kikazo nema wajena acici daga zuwanki kin dau min shayi"
Duk maganar da nake wayancewa nake Dan bana San hada ido da Naseer dake ta kallona kamar ya hadiyeni.