← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 62

Sashe 25

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safiyya kuwa idonta kur Akan abinci da yarana keci Umma Kuma ta tsaya a tsakiyar gidan tana karewa ko'ina kallo tana "Lailai Naseeru Ashe Haka yake.jin dadin rayuwarsa shine muke cin ubanmu a gidan tsinannen yaron can Banda abin Naseeru Dan zai zauna da Naeema har sai yamin karyar zai Shiga duniya"

Muryar Hajara ne yasa Naseer dake sallah yin saurin Sallame sallahrsa ya fito Dan ya gasgata muryar wacce yake ji.

Daskarewa yayi a bakin kofa a lokacin daya daga labule ya hango Hajara da uban Kaya agabanta tana karewa gidan kallo Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha ya hau fada a fili Sam bai lura da Safiyya ba sai daya ji tashin muryarta tana "Mai kuka wani tsatsaremu da Ido kamar Baku sanmu ba shegu Wanan uban abinci da kuke ci Haka har da kifi lailai kun samu duniya Umma Bari na fara cin wanan tukunna na samu nutsuwa kafin a zubo Mana Dan Naga matar gidan kanta a sama yake Bata so ganinmu ba"

Ta nufi wajen su Nadeeya gadan gadan

Naseer kuwa ganin Safiyya ya tayar Masa da ciwon kirjinsa Yana jin ciwon siyar Masa da gidan da tayi na dawo Masa tamkar a lokacin ta siyar.

Bai San lokacin da ya isa gaban Safiyya dake k'ok'arin Zama Dan taci abinci ba Ido rufe ya cakumeta ya tsayar da ita ya hada kanta da bango tare da shake Mata wuya Yana k'ok'arin rabata da numfashinta da yakeji a Ransa tabbas kashe Safiyya ne kawai zai saka ya daina Jin ciwon dayake ji a kirjinsa.

Hajara. Hankali a tashe ta nufi wajen Naseer ta fara ihun ya cikata kar ya kasheta Bai ga cikine a jikinta ba

Amma Naseer ko gezau baiyi ba sosai ya Kara shake Safiyya Yana ta biyashi kudin gidansa.

Ni kuwa ko kallonsu banyi ba na ja hannun yarana na turasu dakina na rufe k'ofar dakina na nufi daya d'akin shima na rufe na saka kwado.

Kitchen Dina ma Haka na koma na zauna akan kujera danake Kai na dau Reza na fara gyara farcena.

Dan Basu isheni kallo ba wajen Naseer Suka zo ba wajena ba so nake su Gama abinda suke su juya su bar min gida.

Dan Naseer a yau zai San da da yanzu ba daya bane ko kusa ko alama bazan dau abinda sukamin a baya ba a da Dan Ina zaune a gidansa ne suka min abunda ransu keso Amma yanzu kuwa gidana ne Bari Naga iya gudun ruwansu.

Azaba ne yasa Safiyya sumewa

Dan ba iya shak'a Naseer ya Mata ba sai daya hada.mata da duka.

Duk dukan da Hajara ke Kai Masa tana ihun kuka har da su cizo Naseer Duk baiji ba sabida yanda idonsa ya rufe.

Sai dayaga Bata motsi ya cikata Hajara ta zub'e gaban Safiyya tana zagin Naseer akan gida zai kashe Mata 'ya Naseer kuwa a tsawace yace"Umma Mai kuka Zo Nema Kuma a gidanan"?

Hajara butar data gani da ruwa ta watsawa Safiyya.

Safiyya kuwa taja dogon numfashi

Hajara ta saki ajiyar zuciya tana "Naseer bakada hankali ko kasheta kake so kayi sabida kawai ta siyar maka da gida ba na baka hakuri ba a gidan uban wa kakeso ta samo kudin da zata biyaka.

Naseer karka manta nifa Mahaifiyarka ce kaina Kuma babbn D'ana yanzu Dan an siyar ma da gida shine zaka min karyar ka Shiga duniya Ashe kana Nan kana Jin dadinka da Naeema Ni danake mahaifiyarka Ina can Ina Shan wahala abinci ma na neman gagararmu Tijjani dayake tsinanne daga shi har matarsa azabtar damu suke idan baka rik'eni ba wa kake so ya rik'eni Safiyya ma da ciki tsinannen mijinta ya korota bamuda kowa sai Kai d'in Dan Haka hakuri zakayi mu zauna a nan gashi Allah nata Buda maka ga katon shagonka cike da Kaya ga Dan karamin gida karka wani damu tunda ka dage zaka zauna da Naeema ba yanda zanyi Haka zamu zauna"

Sai a lokacin na Dago kaina daga yanken farcen da nake na mike Ina "A Ina zaku zauna Umma ba dai a gidana ba ko? Dan wanan karamin gidan da kike gani halal Dina ne da kudina na siya babu ko sisin Naseer a ciki.

Gashi Nan agabanki ki tambayeshi kiji shima Dan yaransa na barshi yake zaune a gidanan Dan Haka ki nemi wani gidan ki zauna ba dai gidana ba idan ma Dan Naseer na gidan ne shima wlh Tallahi Zan hado masa kayansa ku tafi Dan bazan yarda ku zauna a gidana ba kamar yanda Baku yarda na zauna a gidan Naseer ba"

Hajara tsananin.mamakin Naeema yasa ta kasa magana Naseer kuwa b'acin Rai ma Bai Bari ya iya magana ba sabida karfin halin mahaifiyarsa da kanwarsa shi kam badan Kar yayi sabo ba dayace Allah ya dau Ransa da Wanan abinda mahaifiyarsa ke Masa

"Karya kike Yi Naeema wanan ba gidanki bane gidan Naseer ne Kun hada Baki da Naseer ne Dan kuce min ba gidansa bane Dan Kar mu zauna toh karyarki ta Sha karya wlh sai mun zauna dan bake Kika haifamin shi ba da zai tare a gindin keda yaranki gida Wasa ne da Zaki iya siya ki bude katon shago ga injinan markade har biyu yanzu Naseer Dan Kar mu zauna a gidanka shine zaku hada Baki kucemin gidan Naeema ne toh ko uwar gidan Naeema ne wlh sai mun zauna Dan itama ai da kudinka tayi arzkin.

Hajara tace tana k'ok'arin komawa ta zauna a gefen Safiyya da ta Dade da farfadowa tsoron Naseer yasa ta kasa bud'e idonta

Tana Jin duk abinda suke cewa

Ni kuwa Ina ganin ta zauna na kalli Naseer nace "Kasan wlh Tallahi bazan yarda su zauna min a gida ba Naseer kasan yanda zakayi dasu.

Idan dai har Dan kaima na barka ka zauna ne suka biyoka suna takamar kana gidana ne a zaune wlh sai dai kayi hakuri ka bisu Abunda na dauka a Baya wlh Tallahi bazan dauka yanzu ba"

"Umma wlh Nan ba gidana bane Nima albarkacin yarana nake ci shiyasa ta barni na zauna Kun siyarmin da gida hakan Bai Isa ba sai Kun biyoni Inda zaa taimakamin

"Nima albarkacin jikokina zanci ta hakura ta barni na zauna Dan na Gaya maka ba Inda zanje kaji na rantse maka"

Umma tace tana Kara gyara Zamanta

Ni kuwa mik'ewa nayi da zumar shiga daki Naga Naseer ya rigani Shiga d'akin Rai a b'ace ya fara tusa kayansa a cikin bakkonsa ban ce Masa komai ba ya gama had'awa ya fito daga d'akin ya kalli Hajara Yana "idan ma Ni kuka biyo toh na barwa Naeema gidanta sai kusan Inda dare ya muku bazaku kasheni da Raina ba"

Daga Haka ya fice daga gidan Ransa a b'ace yarana na San suyi magana na daka musu uban tsawa Suka koma ciki da Sauri.

Na Kara rufo kofata na kalli Umma da ta bi k'ofar gidan da kallo tana mamakin tafiyar da Naseer yayi ya barta

Ni kuwa Isihu na kwallawa Kira ya shigo da Sauri

Na nuna Masa bacconsu Umma Ina "Fitarmin da kayan Nan can waje Zan Shiga daki idan sun tafi ka rufemin k'ofata Dan wlh bazasu zauna min a gida ba"

Safiyya da Umma mik'ewa sukayi da ganinsu da zasu samu wuta zasu iya jefani a ciki

Umma cikin wani irin murya tace "Naeema sai kinyi danasanin korarmu da kikayi wlh ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayanki ba dai mu Kika Kora ba wlh Zaki gani"

Umma tace tana yin waje Ni kuwa nace "Insha Allahu ba Abunda Zaki iyamin alheri Zan gani idan Allah ya yarda"

Hannuna Zahira ta ringa ja Dan har fara hawaye

Safiyya kuwa idonta ya sauka Akan Zahira da ta Dade Bata ganta ba wani irin murmushi naga ta sakarwa Zahiran daya sa naji gabana ya tsinke kamar wancan lokacin da idan zasumin mugun Abu kirjina ke tsinkewa.

Tura Zahira daki nayi da Sauri na fito daga d'akin ina "Dalla fitarmin daga gida"

Na karasa wajenta Ina turata waje

Ita kuwa ta Kara sakar min murmushi tana "ki shirya tarbar balain da zan jefo Miki"

Daga Haka ta fice waje.

Ni kuwa na rufo kofata Ina adduar insha Allahu ba balain da Zan gani

Hajara kuwa Tana fita ta hango Naseer daya kusa Isa bakin titi ta dib'a aguje ta bishi abaya.
Tana kwalla Masa Kira.

Naseer Bai tsaya ba har sai data cimmasa ta zub'e a gabansa ta fashe da kuka tana Kar ya tafi ya barta ya rufa Mata asiri Bata da kowa sai shi.

Kafarsa ta rik'e tana rusa uban kuka.

Naseer kuwa hankali a tashe ya Ajiye bakonsa Yana "Umma Mai Haka Zaki taramin jamaa Dan Allah ki mike tsaye wlh Umma Nima bansan Inda zanje ba Ina Zan tafi dake banida gidan da Zaki zauna umma wlh wancan gidan na Naeema ne Dan Haka ki koma gidan Tijjani ki zauna kafin na samu wajen Zama"

"Aaa wlh Dana zauna a gidan Tijjani gwara na kwanta a bakin titi kasan wuyan da muke Sha kuwa agidnsa Tijjani Bai d'aukeni da daraja ba a gaban idonsa matarsa ke azabtar damu Baya ce Mata komai idan na Masa magana sai yace Baya San takura ai Allah ya Isa no-no na da Tijjani ta Sha"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Wai Mai yasa burinki ki yiwa yaranki mugayen kalamai Umma a cikin mu hudu waye Baki yiwa Baki ba Umma kinsan bakin uwa kuwa daidai da shedaniyar yarinya can Haka Kika Yi ta Mata Baki gashi baa je koina ba Aurenta ya mutu ta dawo gabanki da ciki Umma bahaka uwa take wa yaranta ba Umma Yara koda kuskure suke Yi addua ya kamata ki bisu dashi gashi duk kin Mana baki Umma kema abin na shafarki"

A takaice Haka Hajara ta marairacewa Naseer da kuka har sai daya kaisu gidan wani da suke mutunci dasu Akan su kwana daya kafin ya samo musu Inda zasu zauna ya rasa yanda zaiyi da Hajara.

Gidan da suka sauka.kuwa tarb'a Mai kyau aka musu sai da suka ci abinci nutsu suka hau hirar Naeema da irin Abun da zasu Mata idan sun samu wajen Zama.
Chapter 25 · 0% Book details