Sashe 48
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga yanda yake dukanta na Kara gasgata dana ba'a hayyacinsa yake ba haka ne ya sa ni ma na hau Kai ma sa dukan Ina ya cika ta dan wani irin karfine da Waleed din daya sa muka kasa raba shi da humaira.
Sai dana fashe da kuka Ina ihun a kawomin agaji kafin ya saki humaira daya Mata jina jina ya bangaje sauran yayyensa ya Kara yin waje
A gefen gado na zube na fashe da kuka Ina sallati
"Umma yau mu Waleed yake zagi har dasu duka Umma Waleed ko ya fara shaye shayene"?
Cewar Nadeeya
"Kema ai ko ba'a fada Miki ba kinsan ya fara shaye shaye Waleed Nan ko Raheema yayi wa ba daidai ba yayi ta binta Yana bata hakuri kenan bai tab'a maida Mana magana ba Amma kiga yau shine har da kokawa da humaira"
Cewar Minal tana bubbuga bayan humaira dake numfarfashi
Ban iya tanka musu ba dan ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata muryar Inna Amina dake kwalla min Kira yasa nayi d'akinta Ina cigaba da kuka.
A gabanta na zub'e Ina cigaba da kukan da nake Sanin kukana na d'aga Mata hankali yasa na tsayar da kukan Ina "Mama wlh an tab'a waleed dana ba haka yake ba mama kema shaida ce yanda yake girmama yayyensa Mama yau Waleed shine da zaginsu har da dukan Humaira wani yaro Mara kunya a unguwar Nan dasu naga Waleed fa Mama wlh an tab'a waleed mama kila shima an Masa turen Aljannu da zasu ringa saka shi Rashin ji Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na karashe Ina Kara fashewa da kukan.
"Mama na rasa mai nayi wa bayin Allah nan suke san ganin bayana ko wata uku Zahira batayi da dawowa daidai ba yanzu Kuma sun dawo Kan Waleed laifine dan na auri Naseer mai na musu da zafi haka suke San tarwatsa min rayuwa"?
Inna Amina bata hana ni ba sai data bari na ci kukana na koshi
Ta fara rarrashina "ki kwantar da hankalinki mamana ki daina zubar da hawayenki,indai turen Aljannu aka yiwa Waleed insha Allahu zanyi iya k'ok'arina na Raba shi da su nima duk abinda kuke yi Ina jiyo ku daga yanda yake daga murya nasan yaron nan an tab'a shi banso kawai na Miki maganar ne na d'aga Miki hankali insha Allahu zai dawo daidai da iziinin Allah kiyi k'ok'ari ki turo min shi akwai Addu'a da Zan Masa indai da jinnu a jikinsa sai sun fita Kuma wanan Abunda ya faru da Waleed ya Zama dole mu dage da Addu'a har sauran yaran naki Allah ya karesu daga sharrinsu Ina mamakin halin bayin Allah nan da basa tsoron Allah nakan ji labarin mugaye Amma na bayin Allah nan na daban ne ace uwa ce ke san ganin bayan danta haka dana tunanina wlh bake suka tsana ba babana Suka tsana tunda har zasu iya tab'a yaransa Allahu ya shiryesu su gane tin lokaci bai kure musu ba"
Inna Amina sai dai Allah ya Mata sakayya da Aljannatul firdausi tayi k'ok'ari a kaina sosai da yarana.
Dak'yar na samu na bawa su Nadeeya baki akan su bi Waleed a hankali dan gani suke shaye shaye Waleed ya fara,nawa ma waleed din yake da zai yi wani shaye shaye.
Haka na zauna zaman jiran dawowar Waleed har aka yi sallah Isha Sam hankalina ba'a kwance yake ba.
Sallah ma ba'a nutse nayi ba sabida tashin hankali
Ina tsoron Kafin Waleed ya dawo hayyacinsa ya jawo min wani maganar
Yayyensa duk basu bi ta kansa ba suka duba littattafansu Suka je suka kwanta dan Haushin Waleed suke ji sosai suna ganin Kamar ban dau.matakin daya dace na dauka a kansa ba.
Inna Amina ke dan Jana da Hira Wanda rabi waazi ne akan yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka a fadarta duk abinda zasu min yanzu ba zai kai na baya ba idan har Allah dana dogara dashi ya kareni da tsawon lokacin nan nayi Imani akan shi zai karemin yarana ruwan addua da ta saka a Kofi ta Kara nuna min akan Yana dawowa zata bashi insha Allahu zaa dace
Hankalina ya dan kwanta sanin wacece Inna Amina macece Mai baiwa burina Waleed din ya dawo kawai na samu na bashi ruwan Addu'a.
Agogo na duba Naga goma har ta dan.wuce ba Waleed ba dalilinsa
Waleed da daga Massallaci sai makaranta sai.kuma gida sai gashi Waleed din ne yau bansan Inda yaje ba har karfe goma.
Waje na fita da hijab a jikina na hau duduba hanya ko zan ga Waleed Wasa Wasa sai gashi nice har gidansu shagari ban same shi ba.
Duk dandalin dana san suna zama na duba ban gansu ba.
A haka na koma gida nayi zaman dirshan a k'ofar gida da za'a auna jinina ni nasan ya balain hawa daga safe zuwa yanzu
Ashe haka uwa ke Shiga tashin hankali idan danta ko yarta ya d'auko hanyar lalacewa ko ya iyayen Yan d'abba sukeji da karuwai da kullum.a cikin d'auko magana suke kila ma bakin ciki ke Zama ajalin iyayensu
Hawaye kawai ke zubomin Ina tuna irin tarbiyya da Allah ya bani iko na baiwa yara na da har ake Jin dadin zaman mu a unguwa anya da akwai ranar da zan tab'a farinciki a rayuwata?nidai badan Kar nayi sabo ba da nace nayi nadamar auren Naseer dan daga aurensa zuwa yanzu banga kalar bakin cikin Da ban kunsa ba,Ina fita daga wanan balain zan fada wani yanzu Kuma an bar kaina an koma Kan yarana
Har yanzu ni nasan zafin da nakeji idan na kalli Zahira yarinya Mai balain tausayi da hankali yanda suka maida min ita a kwanan Nan ma sababin halayye nake gani a tare da ita yarinya Mai sanyi hali ta zama masifafiya Abu kad'an zata hau kananenta da masifa har dasu Bugu idan taso
Ni da nake mahaifiyarta ma bata damu ta ringa gaisheni ba kullum tana d'aki a kwance.
Zurfin da nayi a tunani bai saka nasan karfe dayan dare ta kusa ba sauro sai kai wa fatata cizo suke.
Muryar Inna Amina data daddafa bango cikin dingishi ta fito waje Jin ban dawo ba ya saka na dago
"Haba mamana zaman mai kikeyi a waje ke kadai duk rashin Waleed din ne"?
Kukan da nakeyi a zuci na fashe dashi Ina "Mama bansan Inda Waleed yake ba Waleed bai dawo gida ba taya Zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa"
Inna Amina na k'ok'arin Magana na hango Waleed ya taho yana pito Wai Waleed dina ke fito Yana abun marasa tarbiyya.
Ido na zuba Masa har ya karaso ganina a zaune a dakalin k'ofar gida bai saka ya tsaya ba illa ma wuceni da yayi ya fara k'ok'arin Shiga ciki
Inna Amina dake tsaye a bakin kofa ganin Yana neman ratsawa ta gefenta ya wuce ciki yasa tayi karfin halin cewa "Babana ina kaje ne.kayo dare haka muke ta neman ka"?
"Kallon ball muka je da abokaina"
Yace ciki ciki Yana wucewa ciki
Inna Amina tamkar Mahaifiyata na d'auke ta zuciyata ta sosu da yanda ya Mata hakane yasa na mik'e a zuciye zan bi bayansa Inna Amina
Ta ruko hannuna tana girgiza min kai "Ki bishi a hankali Mamana ki Kai zuciyarki nesa bayin kansa bane ki taya shi da Addu'a ki Kara janyo shi jikinki kar duk abinda zaiyi ya b'ata Miki rai tunda kinsan ba yin kansa bane kila an Masa hakane ma dan a rabaku yayi ta Abu kina Jin haushinsa ko kina jibgarsa a karshe ma zuciya ya deb'eki ki furta kalmar da bata dace ba mu bishi a hankali kinji"
Gyada Mata Kai nayi maganganunta na shigata sosai dan wanan sam ba dabiun Waleed bane taba min shi akayi.
Ciki muka shiga na kulle k'ofar Gidan
A tsakar gida Muka sameshi ya zauna akan tabarma Yana cin abincinsa dan abincin ranarsa Dana darensa duk Bai samu yaci ba
Dak'yar na yakice shi ya daina cin abinci dasu Zahira dan a da tare suke cin abinci gabadaya ko fita yayi sai ya dawo suke yarda Suma suci akwai soyayya Mai k'arfi a tsakaninsu.
Dan zaman da Naseer yayi damu Mai tsawo a jinyar Zahira yasa suka.koma suna cin abinci tare.
Ko ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga Waleed daya ke ji a Ransa Kamar me ya dawo yaro Mara ji
Daki nabi Inna Amina na karbo ruwan Addu'a nazo na ajiye Masa agabansa
Bai cemin komai ba ya gama ci ya Sha ruwan ya shige Palo yayi kwanciyarsa.
Bacci bai ga idona ba ranar sabida dukufa nayi gaban Mahallicina Ina kaiwa Allah kukana akan ya karemin yarana ya dawo min da Waleed da Zahira yanda Suke a da Allah Kar ya Bawa makiyana dama suga bayana.
Sai da aka fara kiraye Kirayen sallah asuba kuma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana.
Fitowar su Nadeeya daya bayan daya daga d'aki dan su yi alwala yasa na wartsake dan duka yarana sun Saba da tashin sallah asuba.
Waleed shine ma kan gaba dan wani zubin yana riga Naseer tashi Yana alwala zai tafi massallaci Naseer ya bishi a baya
Amma yanzu iya su Nadeeya ne suka fito Banda Waleed da Zahira.
Ina kallonsu suka ringa alwala daya Bayan daya suna komawa ciki.
Hakane yasa na mike na Shiga d'akinsu dan na tashi Zahira itama tayi sallah dan na lura kwana biyun Nan da ta tsiro da sababin hali sallah ma Kamar bata so tayi.
Baccinta take ta shara ni kuwa na sunkuya na Dan bubbugeta dan ta tashi
Yamutsa fuska tayi data bude idon tana kallona
Cikin had'e rai nace ta tashi tayi sallah
"Idan na tashi zanyi"
Tace tana k'ok'arin gyara kwanciyarta
Take raina ya b'aci na daka Mata mugun tsawa dan zan jure komai banda Wasa da sallah
"Maza tashi sallah Bata jiran mutum sai dai mutum ya jira sallah tashi kije kiyi alwala kiyi sallah kafin raina ya b'aci"
A madadin ta bi umarnina sai ta turo baki tana kunkuni.