← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 62

Sashe 57

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana samun kamar wata biyu Zahira ta sameni a daki tana min zancen San cigaba da makaranta dan Nadeeya har ta kusa diplomarta dan itama Wanda ke santa so yake tana gamawa ya turo mune muke dan ki da tuni ya turo,na karanci saurayin Nadeeya yana balain santa abu daya ke sanyaya min jiki wani zubin sai naga kamar laifin Zahira zai shafesu Amma Ina adduar Allah yasa Kar a Kai ga haka a Kuma burina Zahira nakeso ta fara aure kafin Nadeeya sabida zanji wani iri ace Zahira na zaune Nadeeya ta rigata aure sosai na dage da Addu'a akan Zahira har da yarana gabadaya ban saki jiki akan kila su Umma sun kyallemu ba hakane yasa daga ni har Naseer muke addua duk abinda ma zasu yi Allah ya maida kansu ko ya kawo Mana da sauki.

Hankali na maida wajen neman kudi dan idan result din Zahira ya fito mu nema Mata admission itama ta cigaba da makarantar Nadeeya Saurayinta ne ya tsaya Mata wajen cigaba da makaranta ba dan Haka ba dak'yar in zamu iya sanin Nadeeya ta tsayar mana dashi akan shi zata aura hakane yasa bamu hana shi hidimanta Mata ba dan koda Naseer ya hana shi dagewa yayi.

Lokacin da result din din Zahira ya fito bai yi kyau ba daga ni har Zahira bamuji dadi ba ganin damuwar da Zahira tayi yasa na boye nawa damuwar na kwantar Mata a hankali na Dade da karantar kamar taba Zahira da akayi yasa ta rage k'ok'ari bata Kai sauran kanenn nata kokari ba ko ni nakan ci gyaranta wani zubin.

Rashin cin jarrabawar ta ne yasa bata samu admission ba Naseer yaje ya biya Mata wajen da ake koyan dinki da zaman da zatayi haka zuwa wani shekarar mu Kara biya Mata waec din

Daga fara fita koyan dinki Samari Suka Kara yiwa Zahira caa abin har tsoro ya ringa bani da farko zahira rashin mutunci ta ringa musu dan na lura tun abinda kabiru ya mata take ganin kamar duk mazan haka suke dak'yar nida Naseer muka shawo kanta ta fara tsayawa tana kulasu

A cikin ma nemanta akwai wani Khalid da ke balain santa mahaifinsa Mai kudine sosai dan sananne ne a lokacin Kuma dan siyasa.

Nacin da yake yiwa Zahira ba dare ba Rana har wajen koyon dinki yake binta yasa ta fara sauraransa duk da ba wani San shi take ba.

Kyautatawa kuwa sai da na sa Zahira da dakatar dashi dan ba karamin kudi yake kashe Mata ba

Ba Kuma iya Zahira ba har kanennta da waleed.

Kayan abinci haka zai jiddo a kurkuka a kawo mana.

Gashi da hankali koni yafi kwantamin akan kabiru zahira ke hana shi turowa dan tana ganin kamar shima zai iya cewa ya fasa aurenta idan aurensu ya kusa har lokacin bata San dalilin daya sa kabiru ya fasa aurenta ba dan data ce mu bata wasikar da kabiru ya rubuto Mata k'in bata mukayi sabida Kar hankalinta ya tashi.

Khalid yana ganin Zahira tak'i bashi dama ya turo ya nemi Naseer da kansa akan Yana san auren zahira.

Maganin kada ayi kar a soma Naseer bai b'oye wa Khalid duk abunda ya faru da Zahira ba na juyar Mata da Kai da akayi tayi rashin ji a shekarun baya ya nuna Masa bai San suwaye sukayi yiwa Zahira haka ba da Karfin Addu'a ta dawo daidai wanan dalili yasa har Wanda yaso Aurenta ya janye dan haka baya so sai tafiya yayi nisa shima ya janye.

Ga mamakin Naseer khalid sai ce Masa yayi ai ko da halin Zahira ne ba juyar Mata da kai aka yi ba Zai iya Aurenta ko haihuwa tayi shi bai had'a San Zahira da komai ba indai aka ga bai Aureta ba toh mutuwa yayi.

Ba ni ba har Naseer a ranar ba muyi bacci ba sabida tsananin murna Zahira ta dace da Mai kaunarta duk fargabar daya cikemin zuciya duk ya kau.

Sati d'aya a tsakani dangin kabirun manyan masu kudi Suka kawo kudin neman aure a shiryensu suke har da akwatunan lefe dozen.

Ni kaina na tsorata da irin dukiyar da suka kawo.

Kanenn Zahira kukan farinciki kawai suke suna wani hanin ga Allah baiwa ne.

Mahaifin Khalid daya kasance dan siyasa a lokacin chairman ne da kansa ya taka yazo gidan Sabida San da yake yiwa Khalid.

Bayan babban sallah da sati biyu aka saka bikin Zahira da Khalid.

Iyayen Khalid sunce basa bukatar a kawo Zahira da komai.

Su zasu mata dan ba Khalid kadai ke san Zahira ba duk dangin Khalid da iyayensa balain San Zahira suke so daga Allah.

Tabbacin ba abinda zai hana auren nan idan dai ba mutuwa ba yasa hankali kwance muke ta shirye shiryen mu Allah kadai yasan farinciki da nake ciki dani da Naseer da inna Amina

Addua kam ba dare ba Rana haka muke yi har da azumin mu sadaka duk alhamis da jumma da kaina nake girka abinci Mai yawa na ciyar da almajirai.

Ana saura sati uku auren Zahira da Khalid mahaifin Khalid ya turo wasu mutane biyu da mukullin sabon gida da takardu akan an bar Mana gidan mu tashi daga wanan gida sabida ya Mana kadan a hidimar biki.

Da alama ta silar Zahira arzikinmu zai farfado.

Kukan farinciki dagani har yarana da shi kansa mahaifinsu haka muka ringayi ga Karin alkawarin
bayan biki za'a nema wa Naseer aikin yi tunda iyayen Khalid su keda gwammnati a lokacin

Cikin farin ciki muka koma sabon gidan da muke ganin kamar duk mafarki muke dan gidane irin na masu kudi Mai gate komai akwai

Dukan mu sai da mu kaje gidansu Khalid muka yi godiya har da Inna Amina.

Da a wajena saninta a rayuwarmu alherine.

Khalid shi ya dau nauyin komai duk da muna ta hana shi ni kaina nasan bazan iya fassalta San da Khalid yake yiwa Zahira ba ga kyau ga kudi dan Zahira ma bazata gaya masa kyau ba duk da tana mace Ya ma fita fari.

Saura kwana goma bikin Zahira da Khalid da yamma ya kawowa zahira dinkunanta da ya kai Mata dinki da kansa ba iya nata ba har da nasu Nadeeya.

Suna hira a waje bayan ta shigo da ledojin ta koma wajensa.

Yana saman motarsa a zaune suna cikin hirar Zahira tace Masa "Wai ni ya Naga kamar baka da lafiya ne sai ramewa kake yi"

Murmushi yayi yana "Nima bansan Mai ke damuna ba Zahira kwana biyun nan bana Jin dadin jikina ne ga mugayen mafarki da nake fama dashi ayita tsorata ni daddare ban gayawa kowa ba idan bake yanzu da nake gayawa ba kema dan bana iya b'oye Miki komai shiyasa na gaya miki da Alhaji da hajiya sun San maganar Nan da sai sun daga hankalinsu amma ni nasan ba komai kila haka akeji idan an kusa aure"

Ya karashe da murmushi Zahira kuwa hankalinta ya balain tashi

Amma ta daure bata nuna Masa halin da take ciki ba yanzu tayi girman da tasan muna da makiya masu San ganin bayanmu tasan komai akan dangin babanta.

Haka sukayi hirar sama sama ta shigo gida.

Ta sameni a d'akina ta zub'e akasan carpet cikin kuka ta hau bani labarin abinda khalid yace Mata ta Kara da "Umma Ina tsoron umman Abba ko Aunty Safiyya suyi wani Abu ya wajen Hana auren Nan Umma kiji fa wai ana tsorata shi daddare.

Tunda ta fara min magana nake sallati.

Bansan ma na mike ba sai tsintar kaina nayi a d'akin Inna Amina Zahira na biye dani.

Yanda ta ganmu a firgice ya sa ta mik'e zaune dan a kwance take

Kuka na fashe dashi na hau bata labarin da Zahira ta bani ina "Mama Ina tsoron sharrin bayin Allah nan Ina tsoron suyi abinda zai saka a fasa auren nan ba abinda bazasu iya yi ba dan suga bayana dana Zahira kin San irin tsanar da suka yiwa Zahira sabida kawai tana Kama dani kinsan irin wahalar da suka bata Kar yanzu da suka ga ta dace da Mai kaunarta su cutar dashi"

Na karashe Ina fashewa da kuka

"Haba Naeema ki kwantar da hankalinki wlh basu Isa su hana abinda Allah ya kaddara ba ki mik'awa Allah lamuranki zai isar miki insha Allahu mu dai mu dage da Addu'a shima Khalid din idan yazo ta turomin shi Zan basa adduoi ya ringa yi ba abinda zai faru insha Allahu dan Allah ku kwantar da hankalinku idan dai kuga baayi auren Nan ba toh wlh dama Khalid ba mijinta bane haba Naeema kiringa amfani da hankalinki Mana yawan tsoron Nan naki ma na iya sawa Allah ya jarrbaceki Abu kad'an sai kice zasu Miki wani Abu kenan duk abinda zai sameki sune bazaa jarrabceki ba"

Naseeha ta min nida Zahira

Nayi k'ok'arin boye damuwa na ne kawai Amma hankalina a tashe yake.

A haka lokacin biki yayi ta matsowa daga ni har Zahira jikinmu a sanyaye yake

Naseer Dana gaya masa ma cemin yayi ba abinda zai faru insha Allahu dan baya bacci tunda bikin ya matso

Ana saura kwana hudu daurin Auren Khalid da Zahira khalid yazo gidanmu a firgice bai tsaya neman iso ba ya fado palon ya zub'e a gabanmu ya hau bamu hakuri duka Muna zaune a Palo

"Dan Allah kuyi hakuri na fasa auren Zahira wlh sunce idan na dage zan Aureta sai sun kasheni

Ido bud'e Ido rufe haka suke biyoni da wuka.

zasu kasheni har da micizai yanzu haka gasu Ina kallonsu da manyan micizai wlh tunda na had'u da Zahira suke tsoratani suke min kashedi nak'i ji yanzu naga da gaske neman rayuwata suke dan har hatsari suka saka nayi yanzu bansan Zan tsira da rayuwata ba dan Allah kuyi hakuri inasan Zahira wlh Amma bana so na mutu na fasa aurenta ne dan na tsira da rayuwata"

Tunda ya fara magana muke kallonsa Muna zuba sallati

Zahira kuwa Ashe ta Dade da sumewa

Naseer ne yayi karfin halin cewa ba komai Allah yasa hakan shi yafi alheri

Khalid daya jike da gumi idonsa duk hawaye

Ya kalli wajen da Zahira ke kwance kamar zai karasa wajenta kuma.ya fasa ya fita waje da Sauri yabi ya rame Kamar bashi ba
Chapter 57 · 0% Book details