← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 62

Sashe 17

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murja kuwa cikin tashin hankali ta dira gabanta tana "Mama Dan Allah karki Masa komai wlh inasan mijina Dan Allah karki Masa komai wlh ba laifinsa bane Mama karki makantarmin da miji Dan Allah

Fusge kafarta Rabin tayi tana "wlh sai nayi Abunda nayi niyya Dan ya kaini bango na tsani mijin Nan naki wlh tunda Naga Yana da taurin Kai duk aikin Dana Yi akansa Baya ci na tsane shi na rasa Mai yasa Kika nace kina San zama dashi"

"Nidai Ina San shi mama Dan Allah karki Masa komai nidai burina kimin aiki akansa Mai zafi yazo da kansa ya maidani gidansa a Kuma mallake min shi ya daina min taurin Kai duk abinda nace yayi shi zaiyi.

Mutane biyu nakeso kimin maganinsu wani jamilu da wani Ashiru makocina su nake so ki Gama min dasu Dan su suka hada min munafirci Nan sai Kuma uwar mijina da kanwar mijina Umma inaso Suma ki kawomin karshensu duka sukamin yau har kasa suka bani naci"

Tsaki Rabi tayi ta janyo bakin tukunyar tsafinta gabanta dake cike da wani irin ruwa tana "Daga Kan shegen mijinki zan fara Dan wlh Bai daki banza ba

Take ta hau surkulle Tijjani ya bayyana saman ruwan Yana Kan vespansa Yana ta tuk'i

Murja cikin tashin hankali ta hau ihu tana Mama Dan Allah karki Masa komai ki taimaka min wlh inasan mijina"

Wani dogon Abu Rabin ta d'auko kamar kibiya zata caka a ruwan.

Murja ta fizge kibiyar da k'arfi.

Rabi kuwa ta girgiza tukunyar da Tijjani har lokacin yake bayyane Yana tuki.

Take kuwa vespan nashi ya hau tangal tangal dashi har sai daya bige wani Mota dake gabanshi ya hantsulo daga Kan vespan.

Ta daki ruwan Tijjani ya b'ace Murja ta hau zunduma ihu

Ita kuwa ta daka Mata tsawa tana ban masa.komai ba na dai Masa gargadi ne kawai

Dan wlh wanan shine na farko na Kuma karshe idan ya Kara tabaki wlh sai na raba shi da numfashinsa

Sai wa kikace "Nidai nunamin shi nagani na tabbatar ba Abunda ya sameshi"

"Ba Abinda ya sameshi dalla karki dameni wlh Kika batamin Rai Zan Masa Mai gabad'aya

Tace a tsawace Tana Kara surkulle Sai ga Mallam Ashiru ya bayyana a cikin Massallaci a zaune tana daga kibiyar tsafin ta ya b'ace

Duk abinda take Murja na kallo

"Wanan sai anyi da gaske Dan Baya Wasa da Addu'a"

Surkulle ta Kara Yi amadadin Jamilu ya bayyana sai Murja ce ta bayyana

Hankali a tashe Rabi ta girgiza tukunyar tana "wanan Dan iskan ne Ina tab'a shi kanki zai dawo shima sai na shirya sosai Dan bahaka yake zaune ba

Ita Kuma uwar mijinki da kanwar mijinki kibarni dasu sai kin koma.zaki dau fansar abinda suka Miki

Wanan mijin sai nayi dgsk Zaki mallakeshi taurin Kai ne dashi"

Sosai Murja ta ringa Jin dadin mallake Mata Tijjani da mahaifiyarta tace zatayi

Tijjani kuwa Yana hanya zaije gadon Kaya wajen Naseer yana dab da Isa wajensa yaji Kan machine din na rawa Yana neman kwace Masa duk yanda yaso rik'e Kan machine din kasawa yayi har sai daya buge wani Mota dake gabansa ya hantsula.

Sallati mutane Suka saki sabida duk an dauka Tijjani bazai Kai labari ba sabida ya daki motar gabansa sosai

Ga mamakin.mutane Kuwa suka ga ya mike tsaye Yana karkad'a jikinsa

Mai motar kansa da aka buge sai daya fito ganin Tijjani Bai ji ciwo ba yasa ya koma ciki yaja motarsa batare da ya tsaya sauraran hakurin da Tijjani ke bashi ba Dan ya fasa Masa glass din motarsa.

Vespa din ya hau ya koma gida dan kayansa sun b'aci washegari da sassafe ya dau hanyar gidan Naseer sai daya fara tsayawa a tsohon gidan Naseer ya tambayi Inda suka koma da kwatance yaje har k'ofar gidan.

Da Sallama ya Shiga gidan

Nadeeya dake shara a tsakar gidan ce ta amsa ganin Tijjani ne yasa tayi wurgi da tsintsiya hannunta taje ta rungumeshi tana Masa oyoyo.

Naseer dake kitchen fitowa yayi da kofin shayi a hannunsa.
Duk da Yana Jin Haushin tijjanin Haka ya saki fuskarsa

Ya Yi wa Tijjani iso har palon

Hajara dake zaune da Safiyya a daki suna Shan shayi kamar a mafarki taji muryar Tijjani ta kuwa Mike da Sauri tayo waje Dan ta gaskata zarginta

Wani irin hade Rai tayi ta fito daga d'akin a daidai lokacin. Da Tijjani ya zauna Akan tabarma dake shimfide a palon hannunsa cikin Na Nadeeya

"Uban me kazo nema a gidanan Tijjani"?

"Aaaa hajajju makatu Ashe kina ciki Rai kanga rai hajiya Umma"

Tijjani yace Yana dariya dayaga yanda Hajara ta had'e Rai

Hajara kuwa tace "ubanka kake rainawa Hankali Tijjani bani ba maza kafin na kirga uku tashi ka bar gidanan Dan na Gaya maka na yafeka banasan ganinka"

Dariya Tijjani ya sakeyi Yana "Sai hakuri fa Umma nazama Dolenki ba ynda zakiyi inkika koreni Ina kikeso naje"

"Kaci ubanka Tijjani ka dauka Wasa nake ma ko Ni da ka kora daga gidanka har da biyomu da kudin mota ka zabi Zama da matarka Tijjani akan dai kabi Umarnina baka darajani ba a matsayina na mahaifiyarka ka zabi tsinaniya da Bata tsoron Allah k'arfi da yaji ta zaneni Akan shegen bredi kana shigowa ta had'a makirci ka k'i yarda da maganata har sai daka koreni daga gidanka ka dauka Wasa nake Akan na yafe ka a cikin yarana Murja tazama uwarka tunda ita ka zaba akaina Tijjani idan baka San na Kara maka wani bakin ka tashi ka bar gidanan Dan wlh ganinka b'acin Rai yak'e Kara sani"

"Umma Nima fa bansan makira na aura ba wlh sai Jiya nama koreta tana gidansu yanzu Haka Dan wlh bansan Haka take ba kinji na rantse Miki ban taba sanin munafika bace Mai fuska biyu ba sai Jiya da makocina da Mai shagon unguwarmu ya gayamin yanda take yiwa su Zahira bantaba sani ba sai Jiya shiyasa ma Nazo Dan na bawa Yaya Naseer hakuri kema na baki hakurin"

Sai a lokacin Hajara ta Dan saki fuskarta tana "Kana nufin yanzu Haka tana gidansu"?

"Eee tana can"

"Saki nawa kayi Mata"?

"Ban dai sakenta ban nace taje gida"

"Zancen banza baka saketa ba zaka dawo da ita kenan"?

"Aaa bazan dawo da ita ba hajiya Umma ai kina da kudin da Zaki aura min wata matar tunda gashi Nan kin raba Yaya Naseer da Aunty Naeema ya zama gwauro na k'arfi da yaji Nima ba sai na dawo gabanki kiyita kallonmu ba"

"Gwara nayita kallonku a gabana da dai ku zauna da wadanan shegun matan naku"

"Murja dai nasan shegiya ce tunda ta iya makirci ita aunty naeema fa mai ta Miki bakya santa"?

"Bansani ba ubana zaka iya matse bakina in gaya maka Naga alamar ka ma Raina min hankali toh gwara da kazo ma auren Safiyya Nan da wata biyu masu zuwa jibi xaaje neman Aurenta can wajen baffaninku kasan yanzu Naseeru bashida ko sisi Haka Muke zaune Dan Haka ka kawo kudi mu fara rage wani Abun "

Duk maganar da Tijjani da Hajara sukeyi Naseer Bai tofa musu Baki ba kansa a sunkuye yama tafi wata duniyar tunanin

"Umma kema da abin dariya kike Ina Naga kudin da Zan siyawa Safiyya wani Abu ai ko sisi bana magani nima.murja ke ci damu a gidanan tunda Kika Mana abinda kikayi arzikinmu ya tafi muke fama wanan Dan canter da Kika Sani dashi har yanzu shine Dani maneji kawai nake Dan Haka ki San yanda zakiyi da ita"

Dagowa da Naseer yayi ya kalleshi yasa ya kifta Masa Ido

Hajara kua ta dage wlh su biyu su nemo kudin da zasu yiwa Safiyya kayan daki ko satane suyi ita ba ruwanta

Tijjani dariya yayi Dan shi Sam Baya d'aukar ma maganar Hajaran da wani mahimmanci inzata matsa Masa ma saka takalminsa zaiyi yayi tafiyarsa

Hakuri ya bawa Naseer game da abinda ya faru

Naseer kuwa yace masa ba komai

Suka hau Hira da Nadeeya da ta hau bashi labarin irin dukan da Murjan ke musu ba abinda ta rage a azabar da ta gana musu Inda ran Tijjani ya Kara b'aci sosai dayaga tab'a b'unan jikin Nadeeya wake da sabulun ma datace Ana Basu suci yafi balain kona Masa Rai Bai taba sanin muguntar Murja ya Kai har. Nan ba Bai taba sanin ma Haka halinta yake ba.

Ita kuwa Hajara cewa take zatayi abinda yafi wanan Dan Haka ya saketa.

Tijjani cewa yyu in ya koma gida zai aika Mata da saki daya Naseer kuwa yayi saurin girgiza Masa Kai Akan Kar ya saketa ya dai Mata fada sabida ita kanta Bata San ya rayuwa zata kasance Mata a gaba ba ko shi kansa Bai taba tunanin akwai ranar da wani Abu zai saka ya Kai yaransa wani wajen ba sai gashi kaddara ta sa ya Kai su Zahira gidan nasa.

Tijjani sosai yaji tausayin Naseer Dan har ga Allah yasan dauriya kawai yake Yana cikin damuwa.

Bai bar gidan ba sai wajen Sha daya na Rana tare suka fito da Naseer da Nadeeya.

Hajara duk rokon data masa.akan ya Bata kudi dagewa yyi bashida ko sisi Naseer har mamakin Tijjanin ya ringa Yi Dan abinda Sam bazai iya ba kenan.

Har wajen da Naseer ke aikin ginin Tijjani ya raka shi Suka samu inuwa suka zauna

Naseer ya Dan Kara bashi labarin yanda Naeema tazo ta Debi yaran

Da yanda Nadeeya ta dage bazata bisu ba da shi zata zauna

Ajiyar zuciya Tijjani ya sauke Yana "can garin nasu ta Kai yaran"?

"Wlh bansni ba Ina cikin tambayarta Umma ta shigo ta hau ce Mata karuwa k'arfi da yaji Umma ta hanani zaman lafiya ta hanani na samu nutsuwa inasan na kasance da iyalina ta hanani"

"Kaine ka barta fa Yaya Naseer wlh Kai kabari take maka abinda ranta keso Ni bazan iya d'aukar abinda take ma ba Kai ma kagani ai Umma wani zubin zuma ce ita sai da wuta idan inasan Abu wlh sai dai tayi hakuri ta kyalleni ai ba Dole bane sai ka zauna da ita ka Kama Mata haya ka dawo da iyalinka gabanka idan tak'i ka siyar da gidan ka gudu ka barta Dole dai ta koma Calabar"
Chapter 17 · 0% Book details