← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 62

Sashe 56

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakuri Suka cigaba da bani nace musu ba komai suyi min hakuri Nasir ya dawo na Masa maganar kudin auren da kabiru ya kawo a mayar musu da lefen da suka kawo dan dama Allah cikin ikonsa ban Bari ta tab'a komai ba ganin kabiru ya rage Mana nauyi sosai yasa nida Naseer muka Mata dinkuna daidai karfinmu.

Mik'ewa suka yi da Sauri suna "wlh yace ya yafe mata komai ba sai mun karbo komai ba kuyi hakuri dan Allah"

Nima da Sauri na girgiza musu Kai Ina "ba za'ayi haka ba idan har zai fasa Aurenta banga dalilin da zai saka ya bar mata lefensa har da kudi ba.

Nayi dakina da Sauri Ina kwallawa Raheema da Humaira Kira da nake Jin shewarsu a d'akin Inna Amina da alama Basu San me ke faruwa ba kunshi ma ake musu a d'akin.

Da Sauri suka fito daga d'akin hannun humaira d'auke da kunshi

Dangin kabirun suka gaisar suka yo d'akin nawa.

Danne zuciyata nake Ina mayar da kukan da ke neman cin karfina ya fito da k'arfi.
Indai na nuna rauni na a gaban yarana su ya zasuyi kenan ya zama Dole nayi k'ok'arin danne zuciyata.

Umarni na bawa su Humaira da su kai min akwatunan waje yanzu nan kar su b'ata min lokaci.

Dan jikina rawa kawai yake ballantana na iya d'aukar wani akwati.

Had'a Baki sukayi wajen cemin "Umma lafiya kuwa Mai yake faruwa ne"?

Tsawa na daka musu a daidai lokacin da kuka ya kwace min Ina "Ku fitarmin da akwatin nan nace ku daina min tambayoyi sunce sun fasa aurenta"?

Kamar wayanda na watsawa ruwan zafi haka suka ja da baya suna dafe kirjinsu

Ni Kuma na zauna a gefen gadon na rufe fuskata Ina cigaba da kukan da na kasa dannewa.

Ni kadai nasan mai nake ji a kirjina

Waje sukayi gabad'aya Basu dau akwatin kamar yanda na umarce su ba sai ji nayi cikin muryar kuka suna tambayar danginsu kabiru mai Aunty Zahira ta yiwa kabiru da zai fasa Aurenta

Raheema har da cewa "Ku rufa Mana asiri karku Mana haka yau fa zaayi kamu ba Wanda bamu gayyata ba Mai aunty Zahira ta Masa da zafi haka da saura kwana uku aurensu zai ce ya fasa idan laifi tayi muku dan Allah kuyi hakuri"

Ta karashe tana fashewa da kuka dayake akwatin irin Mai taya dinan ne a zuciye na mike na hau Jan babban nayi waje.

Ina zuwa na Kara daka musu tsawa Ina su je su debbo min sauran akwatin Ana dole ne.

Humaira aguje tayi d'akin nawa Raheema kuwa ta cigaba da magiya bakin ciiki yasa nayi kanta a fusace wata dattijuwa a cikinsu ta tareni da Sauri tana "Kiyi hakuri mmn Zahira wlh baa San ranmu haka ya kasance ba yarone ka haifeshi baka Haifi halinsa ba wlh nasan da ciwo Abunda yaron Nan yayi Amma ba yanda zamuyi dashi"

Da sauri na katse ta Ina "kabiru da ma ba mijinta bane shiyasa Allah baiyi zasuyi auren ba halin da yarinya kawai zata Shiga ganin Aurenta saura kwana uku an fasa ni shine damuwa na Allah yasa hakan shi yafi alheri Allah ya musanya Mata da Wanda yafi kabirun ga akwatunan ku nan kudin auren na wajen baban Zahira idan ya dawo ya turo a karba Masa"

Kuka Humaira da Raheema kawai suke Waleed da ke tsaye a bakin kofar d'akinsu zahira da duk Abunda muke Yana kallonmu sai hucci yake.

Suna kokarin Kara magana ya daka musu uban tsawan daya sa suka gigice dattijuwan tayi hanyar waje da Sauri

"Dan ya fasa Aurenta sai me ku gaggauta kwasar kayanku.ku bar Mana gidanan kafin na muku watsi da kayan waje Banda kaddara Mai aunty Zahira zata yi da wannan Mai zubin tsofaffin"

Tsawa na ringa dakawa Waleed akan yamin shiru Amma ko kallona baiyi ba

Abinda har gobe ke hadani dashi kenan tunda aka tab'a shi zuciya da taurin Kai ne dashi wani zubin baka isa ka Hana shi ya hanu ba ko wani Abun yayi idan babansa zai dakeshi baya guduwa haka zai tsaya a ga ma jibgarsa har sai dai idan Naseer din ne ya gaji dan kansa.

Inna Amina ce ma tace ya bar Masa irin wanan dukan sabida Kamar hakan na Kara taurara Masa zuciya mu cigaba da binsa da Addu'a

A karshe Waleed da kansa ya rakasu waje da akwatunan su

Suka hau ja da sauri dan ba karamin tsorata su Waleed yayi ba.

Suna fita na zub'e a Palo na cigaba da rusa kuka takarda da ya bayar a bawa Zahira na hannuna

Tunani iri iri haka suka cikemin zuciya Ina tunanin Mai dalilin fasa auren Zahira da kabiru yayi

Raheema da Humaira d'akin Inna Amina suka Shiga suka gaya mata Ina jinta tana ta zuba sallati.

Waleed Kuma ya zauna Akan kujera Yana hucci Yana girgiza kafa.

Mik'ewa nayi na nufi d'akinsu zahiran dan Naga halin da take ciki

Akwance na tarar da ita ta juya bayanta tana kallon bango daga gani kasan kuka take kasa kasa

Daga gefen ta na zauna banyi Mata magana ba na warware takarda da aka saka a envelope dan na ga mai kabiru ya rubuto a cikin takardar

*KIYI HAKURI BAZAN IYA AURENKI BA ZAHIRA DAN BURINA NAGA NA AURI MACE TA GARI NAJI LABARAI AKANKI KALA KALA A CIKI HAR DA WAI KIN ZUBAR DA CIKIN SHEGE BAN YARDA BA SAI DANA JE GIDAN KAWAR TAKI TA TABBATAR MIN DA HAKA ASHE BA KARAMIN RASHIN JI KIKAYI BA INA SANKI AMMA A HAKA ZAN HAKURA DAKE NA BAR MIKI KOMAI ALLAH YA KAWO MIKI WANI MIJIN AUREN*

ban Iya karasa karantawa ba na runtse idona kirjina na min nauyi Abunda nake ta tsoro kenan sai gashi kabiru yaji labarin rashin jin da zahira tayi da ba halinta bane juyar min da Kan ya akayi ko da tayi rashin jinta Alhamdulillah Allah ya karemin ita da Karfin Addu'a baa rabata da budurcinta ba sai dai wayanda tayi muamallan dasu ne idan za'a kwana Ana rantsuwa ba halin Zahira bane ba lailai a yarda ba dan kawayenta duk ba mutanen arziki ni nasan zasu iya komai suma dan su rama abinda Zahira ta musu dan da ta dawo hayyacinta da kanta ta musu rashin mutunci tace su daina zuwa nemanta tana kuka tazo ta sameni tana wlh bata San ya akayi tayi kawance dasu ba ita da take da kunya Mai ya had'ata dasu.

Murmushi kawai nayi dan ni nasan da ma ba halin Zahira bane sai gashi duk da mun bar unguwar suna nufarta da sharrin ta zubar da cikin shege Ina mamakin halin wasu mutanen da Basu da burin daya wuce su bika da sharri
dak'yar na taushi zuciyata na rik'e hannun Zahira na hau rarrashinta Ina Mata nasiha.

Nasan itama kawaici kawai take min tana nuna min ba komai.
Shigowar Nadeeya da Minal ya Kara hargitsa gidan suna koke kamar gidan rasuwa sai dana musu da gaske suka Shiga hankalinsu Nadeeya ta hau jawa kabiru Allah ya Isa har da cewa zata je gidansu.

Inna Amina ta taimaka sosai wajen kwantarwa da Zahira hankali ta hade har da kannenta ta musu naseeha.

Wajen karfe Takwas Naseer ya dawo niki niki da kayan abincin biki har da dinkin Daurin auren da zai saka inaga farinciki da yake ciki bai bari ya karanci yanda mukayi cirko cirko ba dan duk mun kasa walwalar har gwara ni Ina dan dauriya sabida yarana Amma kannen Zahira da suka ci buri Kamar an musu rasuwa haka su kayi cirko cirko.

Daga yanda suka gaishe shi yasa ya fara lura da halin da muke ciki.

Sai a lokacin ya kalleni ya tambayeni Mai ke faruwa ya Kara da Ina Zahira take

Dan har Waleed Yana zaune a palon Zahira ce kawai a daki

Ban bashi amsar tambayarsa ba dan bansan ya zan Masa bayani ba illa takardar hannuna kawai Dana Mika Masa.

Kafin ya bud'e Naga ya kallemu duka Yana "Wai Mai hakane ba zaku gaya min mai ke faruwa ba"

Ya bud'e takarda hannunsa ya hau karantawa

Sallati kawai yake ni kuwa na kalli su Nadeeya take Suka mik'e suka hau barin palon sukayi dakinsu Waleed ya mike yayi d'akin Inna Amina.

Yanda muryarsa ke rawa yasa hawaye ya hau zubomin Ina "Dalilin da yasa wai ya fasa aurenta kenan abinda nake ta gudu kenan Naseer duk da dukanmu munsan Zahira baa hayyacinta duk tayi wanan rashin Jin ba Amma ba Mai yarda ba halinta bane kila wanan ya zame mana bakin fenti kenan tsorona Kar ba iya ita kadai ba abin yazo ya shafi su Nadeeya
An cutarmin da Yara Naseer wlh an cutarmin dasu bazan tab'a yafewa ba yanzu idan har masu neman auren Zahira zasu ringa Jin irin wadanan maganganun dak'yar Zahira ta samu Mai Aurenta"

Na karashe Ina fashewa da kuka

Naseer bai iya magana ba har lokacin illa sallati da yake yi idonsa ya kad'a yayi jajjur
Bai hanani kukan ba illa mik'ewa da yayi Naga ya nufi d'akinsu Zahira da shigarsa su Nadeeya suka Kara fitowa Suka barshi da zahiran da zazzabi ya rufeta

Nasiha ya Mata ya rarrasheta da kabiru ba mijinta bane shiyasa bai Aureta ba

Insha Allahu zata samu Wanda yafi kabirun.

Sai daya bata magani da kansa ya fito daga d'akin ya shige dakinsa tare da rufo kofarsa nima ban bi takansa ba na Kara duba jikin Zahira na koma dakina dan nima zazzabin naji Yana neman rufeni.

A haka cikin kunya muka hada karyar an daga bikin Zahira sabida Wanda zai Aureta bashida lafiya

Nadeeya ma karyar mutuwa ta ringa lankayawa kabirun.

Ba Abunda baya wucewa
a haka fasa auren Zahira ya wuce kamar baayi ba.
Chapter 56 · 0% Book details