← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 62

Sashe 10

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murja kuwa ba karamin mamaki tayi ba a lokacin data fito taga koina fes ko ita kanta bata taba gyara gidan kamar yanda Suka gyara ba.

D'akinta tace su shiga su gyara Mata Nan da Nan suka gyara d'akin suka wanke band'akin tas.

Duk aikin data saka su Nan da Nan taga sunyi har a karshe ma ta rasa aikin da zata saka su

Wajen karfe goma ta Shiga kitchen ta dafa ruwan tea Kofi daya ta soya kwai guda hudu tayi hadin kauri ta zauna a Palo ta fara ci Tana kallonsu Zahira dake rab'e a gefe Nadeeya kuwa sai had'iyar yawu take Dan ita Bata Wasa da cikinta

Zahira kuwa tsoro ma yasa ta kasa d'ago Kai ta kalleta.

Suna kallon Murja ta Gama Shan shayinta tsaf ta rufe sauran bredin ta mik'awa Zahira Kofin Akan ta wanke ta mayar kitchen.

Zahira jiki na rawa ta mik'a hannunta Dan ta karba Murja ta Kara daka Mata tsawa akan ta karba mana aikuwa tana karbar kofin nan ya sulmiye daga hannunta ya fashe........

*Wlh babu fiction a rayuwar da su Zahira sukayi a gidan Tijjani akwai Abubuwan da bazan rubuta ba sabida wasu zuciya bazata dauka ba sabida tausayi Kuma kamar Yanda na fada labarin nada tsayi masu Dan mahimmancin Zan rubuta sabida Allah na fara gajiya Ya Allah kar ka kawo sanadin da zamu rabu da yaranmu kasa mutuwa ce zata rabamu ameen*
[7/3, 11:43 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 38*

"Kutumar uba kofin danake ji dashi Kika fasamin"

Zahira kasa ta zub'e akan gwiwarta jiki na rawa ta hau Bata hakuri.

Murja kuwa kofin kawai take kallo

Wani irin mik'ewa tayi ta fusgo Zahira ta hau dirmarta Kamar ta Samu babba sai wuli take da ita sabida Zahira siriiriya ce Bata da jiki Nadeeya sai kuka take Tana rik'e Murja da idonta ya rufe ko tausayin Zahira da ta kasa kuka bata ji ba sai data gaji Dan kanta ta kyalleta tana sosoka mata Ashar.

Tsawa ta daka Mata akan ta tashi ta kwashe Mata fasassun kofin kafin ta Mata bille a fuska

Zahira ta rarrafa wajen da kofin ya fashe jikinta yayi jawur sai rawa Yake.

Fasassun kofin na yayanke Mata hannu Haka ta kwashe ta Kai dustbin

Ta tsaya a tsakar gida.
Murja kuwa ta hankada Nadeeya tsakar gida ta rufo k'ofar Palon tana kiransu shegu.

A Haka Suka zauna a tsakar gidan cikin rana.

Daga Zahira har Nadeeyan kuka suka ci su ka Godewa Allah har gwara gidansu sau Dubu da gidan da mahaifinsu ya kawosu Dan Safiyya ce ma take takura musu Hajara kuwa ita zagine tsakaninsu sai rankwashi Bata Kuma tab'a Hana su cin abinci ba

Ga zafin Rana gana dukan da zahira ta Sha Haka Suka zauna a ranar Dan tsakar gidan a wawuke yake iya dakuna ne masu rufi ballantana su samu inuwa su rab'e

Murja Bata fito ba sai karfe Biyu da rabi na Rana ta musu wani irin kallo ta nufi kitchen.

Ta dafa taliya daidai cikinta ta zubo a plate ta shige palon ta hau ci

Zahira da Nadeeya kuwa zuwa lokacn yunwa taci ta cinye su Zahira ta Dan fi Nadeeya dauriya dan Bata da ci sosai tafi auki a wajen kayan kwadayi su biscuit da alewa Haka.
Nadeeya kuwa Sam Bata da juriyar yunwa tana da balai ci Dan bama tasan koshi ba in zaka Bata abinci sau goma sai ta karba taci

Cikinta ta rik'e tana kuka wiwi ganin Murja da plate din taliya yasa ta Kara Jin wani azbar yunwa.
Bata iya jurewa ba tana ganin ta shige ciki ta mik'e ta nufi kitchen Zahira kuwa ta hau kwala Mata Kira cikin karamin murya akan ta dawo

Nadeeya kuwa ko kallonta batayi ba

Ta shiga kitchen din

Tsakin garin masara data gani ta zuba a kwanu ta zuba suga akai da ruwa

Ta saka cokali biyu cikin sand'a ta karasa wajen Zahira dake a tsorace tana suci.

Zahira girgiza mata Kai tayi tana "ki Mayar Nadeeya Kar ki janyo Mana wani dukan Dan Allah "

"Wlh bazan iya mayarwa ba Aunty Zahira yunwa nakeji kici Dan Allah"

Zahira Bata kulata ba tayi ta kallon k'ofar palon tana tsoron Murja ta fito

Nadeeya kuwa ta hau Danna tsakin massarar da ruwa ya shanye da suga a bakinta

Sosai take zabga Loma kamar wacce ta samu garin kwaki

Fitowar Murja da plate din data Gama cin abinci yasa Zahira ta mik'e a tsorace jikinta na d'aukar rawa.

Nadeeya kuwa dayake Baya ta Bata Sam Bata San da fitowar Murjan ba Murja kuwa ganin Nadeeya da plate dinta yasa ta nufi wajenta da gudu tana "Barauniya uban me Kika dauko kikeci iyye wato har kitchen Dina Kika Shiga waye ya Baki izinin shiga"

Kafin kace me ta fusge plate daga hannun Nadeeya itama ta hau kilarta

"Gobe ko Tijjani ne yace ki Shiga kitchen Dina Zaki ji tsoron shiga shegu Mayyu Haka kawai Ina zaman zamana an kawomin jarraba maza kuje ku dau bokiti ku debomin ruwa"

Ta karashe tare da daka musu tsawa

Zahira kuwa a guje ta kinkimi bokiti Nadeeya itama tabi bayanta
Ta dau Wanda Bai Kai na zahiran girma ba har waje Murja ta rakasu ta ce suje can kasan layin wajen makabarta akwai rijiya su debo Mata ruwa maza tana jiransu.

Siyan ruwa take Kuma tana da ruwan tsabar mugunta yasa ta aikesu diban ruwa.

Nadeeya Dan tsakin data ci ya Dan rage Mata yunwar da take ji

Zahira kuwa kasa tafiya tayi sabida rawar da jikinta keyi kafin su karasa karshen layin ta samu inuwa ta zauna ta rik'e cikinta Tana kuka.
Nadeeya kuwa cewa take "Aunty Zahira mu ajiye bokitin mu gudu"

"Ai bamu San hanya ba Nadeeya Kar mu Bata nidai idan baba Tijjani ya dawo Zan rokeshi ya maidamu gida yunwa nakeji cikina ciwo yake da Umma tana Nan da Abba Bai kawo mu Nan ba"

Zahira tace tana fashewa da kuka

"Wai toh Ina Umman ta tafi ne ta barmu"?

"Bansani ba Nadeeya Abba Bai fada min ba"

"Idan Baba Tijjani ya dawo sai na Gaya masa dukan data Mana ta Hana mu abinci"

Nadeeya tace itama hawayen na zubo Mata.

Ta mike ta nufi shagon data gani a bud'e tana zuwa ta zub'e a kasa tana "Dan Allah ka bani bredi na bawa yayata yunwa takeji tace cikinta ciwo yake"

Mai shagon kallo Inda ta nuna Masa yayi yaga Zahira a zaune sosai yaji wani irin tausayin su ya rufeshi ya hau yiwa Nadeeya tambayoyi Ina iyayensu suke Mai ya Hana suci abinci

Nadeeya dake tana da surutu take ta hau bashi labarin abbansu ne ya kawosu gidan kaninsa shine matarsa taki Basu abinci.

Tambayar Nadeeya yayi gidan da suka zo ta kuwa nuna Masa gidan

Ya girgiza Kai gidan Dan ya San Murja zata Kuma aikata basa shiri da ita sabida Tijjani na zuwa wajensa hiran Dare.

Hakane yasa ta zo har shagonsa ta Masa tas akan shi munafiki ne ya Rabar Mata da miji k'arfi da yaji ta kuwa rabasun yanzu Haka ko siyan Abu batayi a shagonsa ta gwammace taje wani wurin .

Bredi ya d'auko Mai Dan girma ya bawa Nadeeya da kananan lemo guda biyu

Nadeeya kuwa jiki na rawa ta hau mishi godiya tana tambayarsa Dan Allah ya sunanshi

Murmushi ya Mata dayaga yanda take da wayo yace sunansa Jamilu bud'ar bakinta sai cewa tayi "Allah ya saka ka a Aljannna Yaya jamilu daga Haka ta diba a guje ta koma wajen Zahira dake rik'e da cikinta Zahira kuwa na ganinta da bredi da lemo ta fusge bredin daga hannunta ta yaga ledan ta hau dannawa a bakinta ko ta Kan lemon Bata bi ba.

Nadeeya itama sosai ta ringa cusa bredin a bakinta sai da suka ji Dama Dama suka Kora da lemon hannunsu.

Zahira kuwa tuni taji ta Dan koshi sanin Nadeeya Bata San koshi ba yasa ta fusge bredin tana "Karki cinye duka ki kawo na boye Mana anjima daddare muci Dan nasan bazata bamu abinci ba"

Daga Haka Zahira ta danne bredin ya kankance ta cusa a skirt dinta.

Suka dau bokitansu Suka dau hanyar karshen layin sai da suka tambayi Inda rijiya yake aka nuna musu Yana gaba da makabarta kad'an abinka da yarinta ko tsoro Basu ba ahaka suka Shiga ta cikin makabartar kafin su Isa wani ya taresu tare da tambayarsu Ina zasuje

Gaya Masa sukayi ruwa zasu d'ebo

Mutumin kuwa yace "Wane mahaukacin ne zai aiko ku Nan diban ruwa duk rijiyar unguwar Nan maza ku juya ku koma baa bi ta nan"

Juyawa sukayi da Sauri.

Suka koma suka Kara d'aukar hanyar da suka biyo Zahira kuwa ta hau cewa "idan muka koma bamu Kai Mata ruwan ba zata dakemu mu nemi wani wajen mu dibi ruwan

"Toh ai ba Inda muka sani"

"Kije ki tambaya mutumin Nan daya bamu bredi haka.kuwa akayi Nadeeya na tambayarsa ya nuna musu wani gida a kusa da shagon suka shiga gidan suka dibi ruwan suka tafi gida.

Sai da suka dade da ruwan Akansu Kafin murja ta fito tana zaginsu Akan Ina suka tsaya suka Dade haka a amadadin ta sauke musu ruwan Bata sauke musu ba ta Shiga kitchen.

Zahira kuwa bokitin sai rawa yake akanta

Nadeeya kuwa data ga bazata iya ba sakin bokitin tayi ya Fadi kasa ya fashe

Murja kuwa ta lailayo Ashar ta fito ta daya kitchen ta wawankawa Nadeeya Mari da rankwashi tace Mata ta d'au tsintsiya ta share Mata Inda ta jikam

Zahira kuwa tsabar tsoro Kara rike bokitin tayi akanta sabida Kar ya Fadi

Sai da Murja ta Dora girkin dare.

Ta fito.ta sauke mata bokitin data ga yanda jkin Zahira ke rawa tana kuka.

Sai data Gama girkin da take tsaf ta daka musu tsawa akan suje suyi wanka ta Kara da "Mitsiyacin ubanku ma daya tashi kawoku ko hadoku da Kaya baiyi ba ai kuwa shi zaku Kara maimaitawa maza kuyi wanka ku maida kayan jiknku kuzo ku sameni a Palo"

A band'akin Tsakar gidan sukayi wanka.

Jikin Zahira yayi jawur sabida dukan data sha
Chapter 10 · 0% Book details