← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 62

Sashe 3

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganar matar Ala ramma da nake cewa Aunty ya fad'omin yanzu Haka ma gidan kanwar ta zanje na jirata idan gari ya waye zata kawomin kayana daga Nan su rakani Tasha Dan isihu ya dage sai yaje ya ga garinmu yaga Inda nake zaune kafin ya dawo

Duk da hankalina ya rabu gida biyu ahaka nayita zabga Sauri har na iso bakin titi na tsallaka na cigaba da tafiya har lokacin kuka Waleed yake Ina jijjiga shi Nima kaina kukan nake a Haka na iso gidan kanwar Aunty na bubbuga ba dadewa kuwa ta bud'e dayake mun tab'a haduwa a gidan Ala ramma ta sani ta kuma San da zuwana

Ciki na shiga ta rufe k'ofar Haka kawai na fashe da kuka da yake mijinta baya gari Palonta muka Shiga na kunto Waleed na rungume shi a kirjina Waleed Kamar yasan Mai ke faruwa bashida kuka amma sai gashi yana ta kuka.

Hakuri kawai take bani tana rarrashina.

Nidai gani nake kamar bazan iya tafiya na bar yarana ba ada na dauka zan iya Amma yanzu Kuma da na fito daga gidan Ina tuno yanda Suke wa yarana sai naji bazan iya ba.

Dayake itama kanwar matar Ala ramma yayarta ta Bata labarin komai a kaina cikin tausayawa ta fara min magana tana "Ni sai nake ganin kamar guduwa ki bar yaranki bashine mafita ba Naeema kikayi hakuri duk tsawon lokacin Nan ballantana yanzu Agaban idonki ma Ana cin zalin yaranki Ina ga bakya Nan nidai Dan aunty ta dage ki tafi ne wlh da kinyi zamanki ai wuya Bata kissa Kuma komai Mai wucewa ne idan kayi hakuri idan. Allah ya raya Miki yaranki wlh da kansu zasu iya kwato Miki yanci a wajensu tunda ance Minal karama ma na musu rashin kunya Amma har ga Allah Nima ban goyi bayan tafiyarki ba"

Cikin tsananin kuka na fara magana Ina "Ya zanyi Nagaji ne mmn Abdul nayi hakurin nayi biyayyar nayi rokon duk a banza shekara Sha biyar Ina k'unsar bakin ciki mmn Abdul ba Dan Ina da tsawon rayuwa ba da sun Dade da kasheni wlh gajiya nayi da abinda sukemin tacemin Ni Mayya ce naki rabuwa da danta Ina neman na kaina tace karuwanci nake yaron Nan sai data sheganta shi Naseer baya iya komai sai dai ya bani hakuri nace Miki da cikin yaron Nan guba suka zubamin a abinci Dan kawai naci na mutu yau da gobe watarana zata iya cin Nassara akaina shiyasa na yanke tafiya na bar Mata gidan indai na tafi da yarana wlh Naseer sai ya biyoni Ni Kuma shiyasa na bar yaran Dan tasan dgsk nake zan iya rayuwa babu Naseer Amma yanzu Dana bar gidan wlh sai naji kamar bazan iya tafiya ba Ina tausayin yarana da basu ji ba Basu gani ba bana San a cutarmin dasu gwara Ni na cigaba da Shan wahalar da su Sha wahalar.

Kuka itama mmn Abdul ta hau yi tana "Allah ya tsinewa matar Nan Albarka k'arfi da yaji ta hanaki zaman lafiya da miji ta Kuma rabaki da yaranki Allah ubangiji ya saka miki"

Kuka nake sosai har ta mik'e ta fita bud'e kofa da ake kwankwasawa sai Gata ta shigo ita da aunty da Niki Niki kayana Isihu shima da wasu kayan jikinsa a sanyaye shima Kamar zaiyi kukan

Aunty palon ta shigo ta zauna tana "Ya Naga kuma kina kuka kinsan Allah Kika biyewa tausayin yaran bazaki iya tafiya ba gwara ki tafi tsinaniyar ta Gane ke kike rik'e da gidan ko ba ke bace kina da amfani a gidan ko bakida shi.

Yanzu Nan na biya na karbi kudin engine nacewa wacce ta siya anjima ta je ta dauki injina Naga ta tsiya ba dai kin bar Wa Naseer kudi ba"

Gyad'a Mata Kai kawai na iya Yi

Ita kuwa ta cigaba da bambami "Maza share hawayenki ki tashi muje Tasha Dan inaso na dawo a yau d'inan karbi kudin injin"

Tace tana mik'o min kudin hannunta

Kasa karbar kudin nayi inajin kamar bazan iya tafiya ba nadamar ma siyar da engine din markade na nake yanzu dame su Naseer zasu ringa samun na abinci Ni sai na ringa nadamar ma daukar shawarar ta duk da nasan duk tayi hakane Wai Dan Umma ta Sha wahala Amma Ni Naseer da yarana nake tausayi.

Tana k'ok'arin Magana mmn Abdul ta fara magana tana "Aunty sai nake ganin kamar tafiya ta bar yaran Nan bashine mafita ba ki dai sake tunani duk tsawon lokacin Nan wuyan data Sha sabida yaran Nan ne Bata gudu tun lokacin ba sai yanzu Kuma Naseer ya Mata hallaci da Bai cancanci Haka daga wajenta ba taurin Kai daya gwada.yaki bin umarnin Mahaifiyarsa ya jefa shi a halin da yake ciki Amma kwatsam yanzu yaga ta gudu ta barshi da Yara wlh zaiji ba dadi a ransa Ni nasan Mai yasa Baya iya yin komai mahaifiyarsa ce Bai San ya zai Mata ba Yana k'ok'arin biyayya ma tace Yana fifita Naeema akanta inaga Kuma ya fito ya nuna bayaso abinda ake yiwa Naeema kinsan abinda zatayi sai yafi Haka a gaskiya aunty ki duba maganar nan"

"kimin shiru larai kinsan Mai matar Nan take yiwa Naeema kuwa?kinsan Abubuwan da duk take mata kuwa kasheta takeso tayi fa akan me zata cigaba da zama a gidan?

Ke idan kece Zaki iya jure duk abubuwa da ake wa Naeema.?Naseer da kike magana akansa Naga guduwa yayi ya barta da yaran Naeema ita ta tsaya tsayin.daka ta nemi kudi duk da cikin jikinta ta tsayawa yaranta itace cinsu da shansu makarantar su abinda Naseer ya guje wa itace ta ringayi kwatsam wanan tsinaniyar matar Nan ta danno ita da kanwarsa suka hau gallaza Mata duk abinda zatayi idonsu.na Kai Naseer din ma ya dawo ba abinda ya canja sai ma gaba da yayi Dan me zata cigaba da zama wlh cigaba da zama a gidan kamar tana Wasa da rayuwarta ne Yara nawa ne suke rayuwwa ba iyaye ballantana yaran Nan da ubansu Dan nasan tafiyar.Naeema bashi zai saka shima ya tafi ba Dan Haka ya zama Dole ya kula dasu Kuma Nima duk abinda zasuyi idona na kansu tunda Isihu zai cigaba da zuwa gidan Kuma yaran na zuwa islamiyya Mallam idan dai ta musu wani Abu wlh Tallahi sai na Kai kararta na tsani matar Nan wlh Tallahi yau da nice Naeema da tuni nayi maganin matar nan"

"Duk da haka Aunty Tafiyar Naeema bashine mafita ba dann kamar ka kashe miciji baka sari kansa ba Naeema zata tafi ne Amma tunanin ta na Nan Dan Haka Aunty Mai zai Hana tayi Zamanta a garin Nan Amma a wani unguwar hankalinta sai ya Dan fi kwanciya inyaso duk lokacin data so ganin yaranta zata iya zuwa gidanki a boye idan sun zo islamiyya sai ta gansu batare da Shi Naseer yasan Inda take a garin Nan ba ta Kama haya ta had'a Kan kudinta ta ringa sana'a

Bansan lokacin Dana mik'e na rungume Mmn Abdul ba na kalli Aunty Ina "Aunty Dan Allah muyi hakan nima sai nafi samun kwanciya hankali a Haka ma wataran na kwashe yarana gabadaya batare da sun sani ba ki taimaka min Dan Allah banida kowa sai Allah sai ku danake ji Kamar Yan uwana"

Aunty ajiyar zuciya ta sauke tana toh shikenan.

Ni kuwa take naji sanyi a Raina Aunty ta koma ta zauna Suka fara shawarar Inda ya dace a samo min karamin gida na haya na zauna ahaka suka yanke nemo min gida a dorayi Dan suna da Yan uwa acan Amma kafin a samo gidan na dai tafi Bauchin na duba gidanmu na siyar sabida na samu ishahsen kudi a hannuna da zan ja jari.

Haka kuwa akayi wajen karfe goma na nufi Tasha bayan Aunty tace min ita Kuma zata wuce dorayi ta cigitamin gidan Haya idan an samu kafin na dawo zata biya kudin hayan.

NASEER

Haka kawai yaji ya kasa nutsuwa yayi sallah hankalinsa yayo gida gabadaya hakane yasa Ana iddarwa ya fito da saurinsa a bakin kofa yayi kicibis da zahira dake k'ok'arin yin waje cikin tashin hankali

Gabansa yanke wa yayi ya fadi Yana "Ke lafiya Ina Zaki"?

"Abba Umma nake nema yanzu tace na Shiga bandaki nayi alwala na tashi su Nadeeya shine Dana fito banganta ba na duba koina banganta ba"

Ta karashe da rawar murya idonta na cika da hawaye

Naseer jikinsa ne ya hau rawa cikin tashin hankali ya Shiga gidan ya duba koina ya fito Yana sallati
Tare da yin waje kafa ba takalmi duk nisan titi Haka ya je kafa ba takalmi Zahira na biye dashi tana kuka.

Ba ta Inda Bai duba ba Bai ga Mai Kama da Naeema ba.

Kamar Wanda ake sassarewa kafa Haka ya dawo gidan Yana Jan kafa Zahira nata kuka Dan tasan Naeema ta tafi ta barsu tunda kwana biyu kenan tana cewa ta kula da kanenta idan tace Umma tafiya zakiyi sai tace aa

Naseer d'akin Naeema kawai ya nufa Yana Jin jiri na dib'arsa.

Bayan ya d'au takardar da Naeema ta ajiye Mishi a bakin kofa.

Ya kwanta rigingine hawayen da yake San maidawa ta karfi Suka hau zubo masa.

Zahira kuwa Kamar wacce akayiwa duka tabi bayansa tana cigaba da kuka

Ahaka Hajara da Safiyya suka fito sabida yanda kukan zahiran ke tashi

Har d'akin Naeema Suka Shiga suna dube dube har Hajara na fatan Allah yasa Naeema ce ta mutu

Zahira na ganin sun shigo ta hadiye kukanta da Sauri jikinta ya hau rawa Naseer kuwa ya bud'e idonsa yana kallon Hajara dake kalle kalle a d'akin ta dawo da kallonta Kan zahira tana "Ke Dan uwarki kukan me kike Mana da asubar nan"?

Zahira bata iya magana ba ta matsa kusa da Naseer daya tashi zaune ya jingina da bango Yana kallon Mahaifiyarsa har lokacin hawaye na gudu a fuskar sa hawayen da ke Kara saka Zahira damke bakinta Dan Kar kuka ya kwace Mata a gabansu Hajara da take ganin tamkar malaikan da zai zare Mata Rai.

"Dan uwarki bazaki gayamin ba kukan me kikeyi ke da ubanki ko uwarki ce ta mutu"?
Chapter 3 · 0% Book details