← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 62

Sashe 26

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shawarar da Safiyya ta kawo akan Naeema ne yasa Hajara mik'ewa ta taka rawa Dan idan suna San su cimma burinsu wajen tarwatsa rayuwar Naeema sai sun hada da makirci tamkar yanda Murja keyi.

Washegari Naseer ya samo musu gidan Haya Mai had'aka da.mutane da yawa a ciki daki dayane sai tabarma da ya saka musu Dan bashida kudin katifa

Cikin murna su Hajara suka koma gidan Dan gwara.munsu kwana a Kan tabarmar da dai zaman gidan Tijjani

Naseer kuwa ce Mata yayi shi a company da yake aiki zai ringa kwana tunda ta koreshi daga gidan Naeema

Budar bakin Hajara sai cewa tayi Kar ya wani damu ya koma gidan Naeeema su zauna ita dai fatanta ya ringa lekosu Yana kawo musu na abinci ya Kuma Bata jari tana siyar da kosai tunda ta lura gidan kowacce na Sana'a

Har hakuri ta bawa Naseer Akan wnan karin da gaske take yayi zaman aurensa da Naeema.

Naseer kuwa ya zub'e a kasa ya hau Mata godiya

*Chapter 3*

*Dama ku barni na huta sai bayan sallah na dawo muku da karfina Dan chapter 3 yafi na daya Dana biyu Kuma wlh na gaji**😟😟😟😟😟😟😟😟😟*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 47*

Nidai tunda Suka tafi naji hankalina ya tashi da irin kallon da Safiyya tayiwa Zahira da alwashin da suka Sha na ganin bayana dauriya kawai nake Amma bansan Mai yasa nake cike da fargaba da Kar su yiwa Zahira wani Abu ba Dan nasan halinsu nasan abinda zasu iya Yi na rasa wane irin masifa da balai ne wanan na rabu da Naseer ma na dawo gidan kaina Amma duk a banza hakan Bai saka sun sararamin ba nikam inaga sai na saka Naseer ya rubutamin takardar Saki na Kai musu sun ga shaida sanan zasu shafamin lafiya.

Ban damu da Rashin dawowar Naseer da sai daya kwashi kwana uku Bai lek'o mu ba Ni kuwa tunda Suka tafi na sake zage damtse wajen yin addua Ina rokon Allah Kariyarsa gareni da yayana addua ma ya Riga da ya zama jikina bana sake idan lokacin da nake tashi idan yayi sai na tashi daga bacci naje gaban Mahallicina

A Rana na hudu Naseer yazo.min da yamma bakinsa a washe ya hau bani labarin Umma ta bashi hakuri ta Kuma sawa aurenmu albarka Wai yanzu ba ta da matsala dani tunda ya Kama Mata gida ya Kuma Bata jari.

Wani irin murmushi takaici nayi ina "Umma ce ta baka hakuri akan ta Kuma yarda mu zauna ba matsala Naseer.kai Kuma sai ka yarda"

Dan rage faraa daya shigo dashi yayi ya cigaba da kallona

"Naseer halan ka manta wacece.umma Taya Umma zata ce maka Bata da matsala da zamanmu tare.har ka yarda Bayan gidana ta zo naki yarda su zauna Kuma Haka kawai sai tace ma ta sawa aurenmu albarka ka yarda Naseer inaga har yanzu baka San wacece Umma ba idan ka manta Ni ban manta ba idan kaga Umma ta biyo ta wanan fuskar toh wlh wani mugun abun zata Mana sai dai na roki Allah ya kareni da yarana haihuwar Minal Haka tace Mana tayi nadama Mai ya biyo baya guba ta zuba a kunnu ta bawa Safiyya ta kawomin.na Sha Akan zan samu ruwan no-no akan naki Sha Suka rufeni da duka Naseer har sai da ka shigo ka k'waceni a hannunta Naseer har ga Allah na gaji da abinda umma kemin wlh Nagaji na rasa wanan masifar da.mai yayi kama tunda na aureka ban taba samun kwanciyar hankali ba daga wanan sai wanan da Ido daya nake bacci sai a yanzu Dana fara samun nutsuwa Umma da Safiyya suka Kara durowa ranar da.suka.zo sun Sha alwashin ganin bayana Safiyya ta kalli Zahira ta girgiza min Kai Naseer idan wani Abu ya Samu yarana ko Ni wlh Tallahi bazan yafe wa Umma da Safiyya ba sai na Kai kararsu gaban Allah nidai ka koma wajenta kar.ma tayi tunanin kana gidan Nan ma ringa lek'omu idan ka samu sarari"

Na karashe Ina fashewa da kuka Dan har ga Allah su Umma sun isheni Naseer.ya bani takarda ta kawai na huta Zan jure komai banda su tab'a min yarana ba dole bane sai nayi rayuwa da Naseer auren Naseer ya isheni ya gundureni bazan karashe rayuwata Su Umma na wahalar Dani ba.

Naseer rarrashina ya hau yi Yana "Yana Naeema wlh da ikon Allah kawai nake rayuwa har.yanzu rabona Nima da kwanciyar hankali tun ranar Dana budi Ido nasan Umma a matsayin Mahaifiyata na Sha Zama nayi tunanin Anya Umma ce ta haifeni kuwa Dan har yau danake yawo.ban tab'a ganin Mai irin Halin mahaifiyata ba ko a tarihi Umma gaba take da kwanciyar hankalina nayi kukan nayi naseehan duk a banza Nima data ce min naje ba komai a zuciyarta nasan ta fada ne kawai Bai Kai zuci ba Amma koma menene Zan cigaba da Addu'a Allah ya shiryeta ta Gane gaskiya wlh Naeema nasan tsinaniyar yarinya Nan ce ke zuga umma.na balain tsanarta duk wani mugun Abu ita kesa Umma amma karki damu insha Allahu ba Abunda zasu iya Miki ko yarana kema shaida ce akan yanda nake Addu'a"

"Duk da Haka ka koma wajenta Naseer zamanka a gidana hatsarine"

Nace na mik'e tsaye Dan har ga Allah banasan zaman Naseeru a gidana Ni nasan zamansa a gidana sai saka Umma ta cigaba da nufata da mugunta

"Taya Zan koma gidanta alhalin haya na Kama Mata daki daya"

"Naseer kayi hakuri ka koma wani wajen da Zama ka ringa zuwa kana ganinsu Waleed wlh zamanka anan zai saka Umma ta ringa kuntata min Amma idan taga baka gidana Zan samu saukin wani Abun Dan idan ma Dan Kai zata min wani Abu idan.taga bama.tare zata kyalleni.

Rai a Dan bace Naseer ya mik'e Yana "Mai yasa kike sawa a ranki Umma zata iya Miki wani Abu duk wani Abu da kika ga ya samu bawa daga Allah ne Umma Bata Isa ta Miki Abunda Allah ya Bai hukunta zai sameki ba wuyanta ki dogara ga Allah"

"Naseer inaga ka manta Abubuwan da Umma tamin ne inaga ka manta Kuma wacece ita shiyasa kake fadar Haka ganganci ne ma na saki jiki nace Umma bazata min komai ba duk wadancan data min a baya ai ita ta ringa min Allah na kareni din"

Katseni yayi a tsawace Yana "kice na fita na bar miki gidanki kawia Naeema ba sai kin biyo min ta wanan hanyar kina fakewa da Umma ba Karki.manta Nima ba a San Raina nake zaune a gidanki ba Naeema a matsayinki ta matata Naeema kaddara ce ta hau kaina na rasa komai nawa amma.kinsan badan kaddara ba Ni Mai bawa wani kyautar gidane Amma ba komai Naeema Zan tafi bazan zauna a gidan naki ba Allah ya bani arzikin da Nima zanyi gidan kaina idan na samu sararin Zan ringa zuwa Ina duba yaran nawa kamar yanda kikace"

Daga Haka ya juya ya fice daga gidan Kamar zai tashi sama

Kan kujerar na koma na zauna Ina fashewa da kuka mumunan fassarar da Naseer yamin Dan har ga Allah bazai Gane Mai nake fada ba da abinda nake gudun Amma Ni nasan watarana zai Gane

Idan nace fushin da Naseer yayi Bai dameni ba karya nayi Dan Naseer nada hawan jini na Kuma San duk a dalilina yak'i rabuwa Dani yake ta fuskantar wadanan tashe tashen hankulan Amma Allah yasan na gaji bazan iya cigaba da jure abinda mahaifiyarsa kemin ba abinda na jura a baya bazan dauka yanzu ba sabida Kar ma ya fassarani yasa ban nemi ya sakeni a halin yanzu ba har sai idan ya Dan farfado daga karayar arzikinsa.

Ban Bari na saka wani damuwa a Raina ba na maida hankalina Kan sanaoina da yarana da na balain sawa ido.nake.kuma addua kariyar Allah a garesu

Safiyya da Hajara a hankali Suka fara karantar mutane da suke zaune dasu wayanda.zasu iya yin talatin sabida gidan katon gaske ne.

Wasu matan Aurene wasu zawarawa har da Yan bariki ma ahaka suke.gwamutse a gida daya.

Sati d'aya kawai da sukayi a gidan suka fahimci mutanen gidan basuda mutunci ko kad'an kowa ta kansa yakeyi

Ga balain Sa Ido da munafirci da suke dashi.

Amma ahaka Safiyya ke fito da tabarma bakin kofar d'akinsu tayi ta kallon mutane dake gidan tana musu shishigi tana Shiga abinda Bai shafeta ba a cikin kwana goma ta Gama Gane matan da suke da aure da zawarawa da Kuma Yan barikin

Akwai wata Iyyatu da hankalinta yafi karkata wajenta matar aurece Mai Yara biyu hatsabibiya ce lamba daya data maida mijinta tamkar yaron cikinta Dan mijinta shi yake Mata wanki ya Mata girki komai dai daya Kamata ace ita takeyi mijinta keyi ita kuwa Iyyatu tana zaune tana karkad'a kafa tana zuba mulki hakane yasa Safiyya fara shishige Mata Amma Iyyatu na shareta
Sai data Sha kwandunan wulakanci a wajen Iyyatun kafin ta fara sakar Mata fuska suna Hira sama sama ahaka har suka Saba Safiyya fa fara bugar cikinta Tana gaya Mata yanda ta mallaki mijinta ta hanyar wani kungurmin boka dan kafin ta aureshi Yana da Mata daya da Yara biyar daga shigowar ta gidansa ta asiriceshi ya saki matarsa ya Zama Kamar bawanta

Safiyya kuwa kamar ta Kama rawa take ta hau rokon Iyyatu ta sadasu da bokan.

Cikin kwana uku Hajara ta bawa Safiyya kudin mota itama zuciyarta cike da farinciki Dan kosai ma da ba wani ciniki take ba a kudin ta bawa Safiyya kudin mota akan taje.

Yanayin zaman munafirci da ake Yi a gidan yasa suka Gane Safiyya da Hajara basa sallah wanda take suka.hau kirnsu da basa sallah aka hau ma kyamatarsu Akan Dole Hajara da Safiyya suka hau sallah Dan su samu mutanen gidan su so su.

Safiyya kuwa Basu dawo
Gidan ba sai wajen Goman Dare.

Jiki a sanyaye Hajara ko Zama bata bari Safiyya tayi ba ta hau tambayarta ya sukayi.
Chapter 26 · 0% Book details