← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 62

Sashe 45

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Oban kayi min wannan k'ok'arin ni Kuma duk abinda kakeso Zan maka tunda har 'yata hauwa haka Zan ringa ganinta zuciyata na ciwo inaso zuciyar Naseer da Naeema yayi bindiga bana San aikin Kuma ya karye duk Inda zasu Kai ga neman taimako"

Mugun dariya Oban ya kwashe dashi ya d'auko wasu allurai da kwarya ya Bawa Safiyya yana ta jejjera alluran a ciki ya d'auko wani Abu kamar bby na namiji da mace yace ta binne akwai Wanda zaiyi daga Nan indai ta binne aikin gama ya gama Amma fa idan har akayi nassarar karya asirin duk wani Abu da zai biyo baya tayi kuka da kanta.

Batare da tunanin komai ba tace ta amince sabida mugunta tace sauran yaran naeema ma a tab'a su.
Sai da ta kwana da Oban ya ci ubanta yanda ya kamata ta dawo gida tayi zazzabin sati guda kafin ta samu karfin neman abinyi tunda ado ya gudu

Ta dai saka Oban ya Mata aiki Dan ya dawo.

A Haka ta samu ado ya dawo ya Kuma biya Mata haya.

Halin da take ciki da hauwa da ita Gata kamar dabba Kamar mutum yasa ta nemi kudi taje unguwarsu Umar tsohon mijinta a lokacin data Isa Bata sameshi ba sai Hafsa.
Yaranta duk sun tafi makaranta,Asmau da Safiyya nata zuba aiki kamar jakai yaran nata sun girma Masha Allah Kuma kyawawa kamar yanda taso ganinsu.

Sai dai kana ganinsu kasan a wahalce suke dan Hafsa ba k'aramin azaba take gana musu ba.

A takaice Hafsa k'in bari tayi ta kwashe yaran sai da suka ci uwar dambe Safiyya ta Sha kasa dak'yar da kyar Umar daya dawo ya samu Hafsa ta Bari Safiyya ta tafi dasu dan shima kasan tausayin yaran yake ji uwarsu ya tsana Amma Yana san yaransa tausayin yanda hafsa ke gana musu azaba yasa yaji dadin zuwan da Safiyya ta yi dan ta tafi dasu at least zasu samu yanci a wajen Mahaifiyarsu.

Safiyya sai da umar ya Bata kudi Kafin ta yarda ta tafi  da yaranta da takejin zuciyarta fari Kal da dawowarsu gabanta.

Hajara

Sosai take Shan wahala da kosai da take siyarwa Bata da burin daya wuce ta samu kudi ta fara tab'a Safiyya da take Shan alwashin ganin bayanta ba ranar da zata wuce Bata tsinewa Safiyya ba takan Yi kuka idan ta tuna  irin korar Karen da Safiyya ta Mata Wai ace Yar cikinta data fi so duk a cikin yaranta itace ta daketa har ta koreta daga gidanta yau badan usaini kaninta ba da Bata da wajen da zata zauna lami ma Mai taimaka Mata kad'an kad'an itama ta bar garin calabar.

Mai taimaka Mata a cikin yaranta Kuma Naseer ne shima Naeema ta kwace shi ya Fifita Naeema akanta

Shiyasa a rayuwata ta tsani Naeema takejin itace duk ummul abaisin daya saka ta tsinci kanta a cikin wanan halin dan da ta rabu da Naseer cikin sauki da bata kai ga aikatawa Naseer Abunda ta aikata Masa da har yazo ya shafeta tafi Shan wahalarsa ba tunda da ace Naseer nada kudinsa da yanzu Yana da gidaje ya Kai uku tunda ada din ma ya mallaka Mata gida biyu.

Ba abinda Naseer baya Mata Amma Naeema ta Mallakeshi ta rabata da danta

Tijjani kuwa dama kullum cikin yi masa baki take tunda har ya Fifita Murja a kanta a wajenta Kam yaranta biyun Nan Tijjani da Safiyya idan tana da dama sai taga bayansu ba ma kamar Safiyya da take Jin da tana da dama kasheta zatayi tsaf abinda ke take Mata birki kawai shine kudin da bata dashi.

Da zata iya samun damar da zata Shiga  wani  kungiya da ta  Shiga  dan ta samu cikar burinta da ta  saka an maidawa   Naseer arzikinsa.

Ta rabashi da Naeema ta azabtar da ita da Zahira ta wahalar da Safiyya Murja da Tijjani a rayuwa sai dai ko kudin arziki Bata dashi kudinta ma yanzu na cinikin kosai a magani yake tafiya Dan fama take da wani irin ciwon kafa dake hanata bacci ta Rasa Mai ya haddasa Mata ciwon kafa.

Tijjani

Talauci da tsananin rayuwa yasa baya iya neman Naseer yanzu Dan wayar gari yayi aka koreshi daga aiki duk Kuma buga bugan da zaiyi baya iya samo ko sisi.

Sai Murja ce ke dan iya rike gidan shima cikin wulakanci Sam Baya lallaba murjan tana Masa iskanci ko gori zai nada Mata na jaki ya Kuma bar Mata gidan

Yanzu haka yaransu hudu duka Mata bayan yarsu ta fari ta Kara haihuwa uku da kusan kansu daya gwanin shaawa yaran

Murja ko kuda Bata so ya tab'a Mata Yara Allah ya jarrabceta da balain San yaranta shiyasa duk Inda kudi suka shiga tana k'ok'arin nemowa dan ta farantawa yaranta Rai.

Mahaifiyarta Rabi a haihuwa yarta ta uku Allah ya Mata rasuwa ta hanyar Hatsarin mota sosai Murja tayi kukan rashin ta.

Yaranta kawai da take gani ke faranta Mata rai ko  a makaranta aka tab'a Mata su sai taje tayi masifa tayi balai ko yaran makota ne Suka tab'a Mata Yara sai ta Rama musu.

Yarta Murja data ci sunanta  nada shekara goma  Mai bi Mata Ramlat nada shekara takwas  Fareeda na shidda sai ummi nada hud'u.

Tashin hankalin da Murja ta fara fuskanta a rayuwarta Bai wuce rashin lafiyar da yaran nata suka fara lokaci guda ba

Kamar ta zauce sabida tashin hankali
Banda Murja takwararta

Ramlat ce ta fara amsa Kiran Mahallicinta Inda Murja sai da aka dangana da kaita asibiti sabida sumewa tayi tayi

Sati biyu kafin ta Gama dawowa hayyacinta  fareeda itama tabi Bayan Yar uwarta hauka tuburan Murja ta kusa yi sai da Karfin adduoi ta dawo daidai

Fareeda itama satinta uku ummi tabi bayanta.

Rasuwar yaran Murja uku yasa Murja ta dan samu tab'in hankali kad'an Amma ba sosai take tab'a haukan ba takan Yi Abun marasa hankali

(Inaso na Dan bada labarinsu Suma gajerce Dan wlh na gaji Bai xama lailai na Kara tabo bagarensu ba Dan yanzu Haka ma daga Naseer har Naeema ba labarinsu sukeji ba tunda suka je suka nemi yafiyar Naeema dasu Zahira.)

Bayan yaranta uku sai data Kara haihuwar biyu sai sun girma ta shaku dasu sai su koma ga Allah a irin haka yasa daga Tijjani har Murja Suka bazama neman taimakon Mallamai anan wani ke cewa Murja taje ta nemi yafiyar yaran data zalinta a baya sai ta nemi yafiyarsu zata ga daidai

(Ba fiction a labarin zalincin da Murja tayiwa su Zahira da Kuma jarrabtar da Allah ya Mata a rayuwa na rasa.yaranta idan ta haifesu bamu sani ba ko ta Kuma haihuwa Dan tunda sukaje suka nemi yafiyar Naeema baa Kara Jin labarinsu ba)

Naeema

Samun saukin da Zahira tayi Yana cikin Abubuwan farin ciki da suka sameni da bana mantasu

Haduwa da Inna Amina danake Mata
Kallon Mahaifiyata dagani har Naseer shima Yana cikin Abubuwan da har gobe bana mantasu.

Inna Amina tsohuwa ce Mai tarin ilimi dan Zan iya cewa har tafi Naseer ilimi shigowarta rayuwarmu yin Allah ne dan ta silarta na Kara samun warwarewa wasu matsalolinmu  ba iya ni kadai ba har Naseer.

Satinta uku a gidanmu bayan tafiyar su Nadeeya makaranta muka Shiga wajenta dan mu gaisheta

Zamanta a gidanmu yasa nake Jin kamar ita din wata garkuwa ce a garemu gabadaya

Dan tace Mana zama Bai Kama mu ba makiyanmu zasu cigaba da bibiyarmu da sharri Addu'oi ta bani da Naseer take akan mu ringa yi daga mu har yaranmu.

Zahira kuwa sabida ramar da tayi da kuma shiru shirun da takeyi yasa Inna Amina tace mu bari ta dawo daidai sosai ta samu wata uku tana Shan magungunan data had'a Mata kafin muyi tunanin Mai data makaranta.

Hakane yasa muke kula da Zahira dagani har Naseer muke ririta ta.

Nidai gani nake duk da sun fita kamar yata Bata dawomin yanda take ba Kamar  da da   nayiwa Inna Amina magana cemin tayi kar na damu zata dawo daidai mu dai cigaba da Bata maganunanta

Koko da kosai da take Sha a lokacin da muka Shiga d'akin nida Naseer tana ganinmu ta saki murmushi muka zauna akan tabarma ita Kuma tana daga Kan katifa

Sai data karasa kokon  ta ajiye kofin muka hau gaisheta

Cikin faraa ta hau amsawa tana saka Mana albarka Kamar yanda ta Saba wanan albarka da take sa Mana da gamawa da duniya lafiya da take mana adduarsa ba karamin faranta mana Rai yake ba

Sai da ta Gama saka Mana albarkan cikin murmushi ta kalli Naseer tana
"Babana yaushe zaka koma wajen aikin naka ne kasan zaman Haka bazai yiwu ba"

Murmushi Naseer yayi cikin Jin dadin kulawarta inama baiwar Allah nan ce mahaifiyarsa

"Mama Abunda yasa bazan koma ba nasan Indan na koma ma korata zaayi dan na kusa shekara Kinga banje ba Batare da na Kuma Gaya musu dalili ba hakane yasa nake neman aikin anan ko Allah zai saka na Dace na samu idan ma ban samu ba Zan ringa aikin ginin da nake yi abaya"

"Karka damu ka koma insha Allahu ba Abunda zai faru kana tare da Addu'a ta daukaka ma zaka samu"

"Zan koma.insha Allahu mama ngd"

"Mamana ke kuma wane sana'a zakiyi kinsan zaman haka ba dadi"?

"Nasani mama kudi nake nema wuyanta na samu kudin bazan rasa sanaar da zanyi ba"

"Allah ya dafa muku ya muku albarka ya yiwa yaranku albarka yanda Kuka taimaka min Allah ya taimake ku"

Cikin farinciki muka hau amsawa da ameen sosai adduar da take Mana ke Mana balain dadi a zuciya.

Washegari kuwa Naseer ya nemo kudi ya hada kayansa da zumar washegari zai tafi

Muna zaune gabad'aya mu da yamma muna Hira da yaranmu a can gefe Kuma Inna Amina na zaune.

Waleed nadaga Gefen Abbansa Yana Masa Magiyar ya tafi dashi Abujan gobe.

Hannayen Waleed ya ruk'o cikin so da kaunarsa sosai yake Jin kaunar Waleed a Ransa sabida hankali da tarbiyya da Naeema ta bashi ga tausayi kamar me a islamiyya da Boko shi yake zuwa na daya

Yan unguwar kuwa duk sun San Shi sabida sharan Massallaci Haka suke saka Masa albarka.

"Idan ka bini Waleed ya zakayi da makaranta kayi hakuri idan ka Gama primary sai na nema maka secondary acan sai muyi zamanmu ko"
Chapter 45 · 0% Book details