← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 62

Sashe 36

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk dauka mukayi bacci ne ya d'auketa hakane yasa muka Yi hayaki a office din da muka kwantar da ita

Yan aji uku wajen su shidda.muka saka su karatun Qurani a fili tunda duk sun sauke Dan duk mun yarda gamo tayi a band'akin

Wajen karfe Tara na safe ta kwalla wani irin ihun daya saka mu toshe kunnuwan mu Dan Kamar ba Dan Adam ne ya saki wanan karar ba fusge fusge ta hau Yi zata fita a guje muka riketa Gam sai dai abinda ya tsorata mu Bai wuce hallitar ta da muka ga Yana canjawa ba idonta kuwa kamar sunyo waje wuyanta ma ya kumbure duk da Bata da jiki sai Muka ga Kamar Naman jikinta ramewa yake kasusuwanta na fitowa na hallitar jikinta har d'auke hannunmu mukeyi sabida azabar zafin da jikinta ya d'auka kanta kuwa kamar baa Jikinta ba sabida zafi

Hankalinmu tuni ya tashi.mukayi asibiti da ita sai da tayi sati biyu a asibiti Ana Bata taimakon gaggawa Amma a amadadin taji sauki.ma sai azaba take Sha hallitarta na Kara canjawa likita da kansa yace mu nemi na gida larurarta bana asibiti bane muna tsoron dawo Miki da ita Haka hakane yasa muka nemi mallami a can shima yayi iya kokarinsa Muka ganin Abun kamar Kara girmama yake Kar tazo ta mutu a hannunmu batare da kunsan halin da take ciki ba yasa muka yanke dawo da ita Dan tabbas abinda ke damunta bana asibiti bane kamar dai jinnu ne.

Girgiza kaina kawai nake Ina rungume da Zahira da zafin jikinta ke Kona min jiki cikin ihun kuka na Dago da yata da ta tashi daga siffar mutane ta zama wani hallita daban Ina "Mai na muku Haka Umma Mai Zahira ta muku Umma Dan Allah kuyi hakuri da laifin Dana muku ku kyallemin yata Bata muku komai ba Umma Ni na muku laifi na tuba Umma ku cikamin yata da Bata ji ba Bata gani ba Umma Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Naseeru Zo kaga yanda Zahira ta dawo Naseeru kana Ina kazo ka kawomin agaji.kar Yata ta mutu"

Kuka nake sosai Ina surutai mallaman kuwa sai Baki suke bani jameela kawarta da mallamar su mace da daya yarinya sai kuka suke suma

Horn din da ake musu a waje sabida da motar makaranta aka kawo su.

Yasa Suka hau min Sallama suna ajiyemin kudi

Jameela kawar Zahira kuwa data ci uban kuka ta rik'e hannun Zahira daya Zama tamkar Kara tana "Allah ya Baki lafiya zahira idan mukayi hutu Zan Zo na duba ki ya Allah ka kawowa zahira Agaji ka Bata lafiya"

( Wlh Allah indai Zan tuna labarin wuyan da baiwar Allah nan ta Sha sai nayi kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Allah ya Miki sakayya duk da ya wuce wlh Ina rubutu Ina kuka)

Haka suka fita Suka barni da Zahira da har lokacin idonta Dake warwage take kallona dashi hawaye na zubo Mata Haka na d'auketa kamar ba mutum ba sabida rashin nauyi na kaita d'akina Ina kuka na shimfidar da ita Akan gado na cire Mata rigar jikinta ko no-nonta ma.shafewa yayi a kirjinta sai kasusuwa kawai kankara na dauko na zuba a katon roba da ruwa na dauko zani na na hau Danna Mata jikinta da ruwan Dan jikinta yyai zafi da yawa da kanta gani nake zata ji dadin Jikinta idan Ina matsa Mata ruwan sanyi a jikinta sai surutu nake kamar mahaukaciya kamar ma har sabo nayi Ina "Allah Mai na maka ka jarrabceni Haka Allah duk addua Nan da nakeyi nake Hana idona bacci sabida Kar wani Abu ya Samu yarana Kar wani Abu ya Samu Zahira Allah sai da Umma suka ci Galaba akanta Allah kaga yanda Zahira ta dawo Allah kaga yanda idonta ya firfito waje"

Maganar da Zahira tayi yasa kukana tsayawa cak muryarta ya dawo na Yara sosai.

Da sirirrin hannunta ta rik'e hannuna tana "Umma Dan Allah kimin addua mutuwa Umma indai kina kaunata kimin addua mutuwa Dan Allah Umma jikina kamar an hura mun wuta Umma"

(Gaskiya bazan iya cigaba da rubuta wajen Nan ba Allah yasani kuka nakeyi ku Bari na tsallake kawai nayi shi a takaice)

Jawota nayi na rungumeta cikin ihun kuka Ina "Bazan iya Miki adduar mutuwa ba Zahira sai dai na Miki adduar Samun lafiya yata da ki mutu gwara Ni na mutu Zahira Zahira ke yarinya ce Mai biyayya Mai tausayin iyaye albarkar annabi Muhammad Saw Zaki samu lafiya zahira Ni na musu laifi bake bace Baki musu komai ba Bai Kamata su tabamin ke ba wayyo Allah ka dubi halin da yata take ciki ka kawo Mata agaji ya Allah ban hada bautarka da kowa ba Kai kadai nake Kira nake kaiwa kukana bansan boka ba bansan Mallam ba Kaine mallamina Kaine Mai sharemin kukana Allah ga zahira Nan ka sasauta mata wuyan da take Sha ya Allah ka dawo da ciwonta jikina"

Kuka nake sosai Kamar Zan shidde ahaka su Nadeeya suka dawo daga makaranta

Suka shigo har cikin d'akina suna shigowa Naga duk sun ja da baya a tsorace cikin tashin hankali da ganin yanda Zahiran ta dawo

Zahira kuwa hawaye na zubo Mata ta ringa binsu da Ido a karshe ta tsayar da idonta Akan Nadeeya tana mik'o Mata siririn hannunta cikin muryar yaran tana "Nadeeya Zo gareni"

Nadeeya kallonta kawai take jikinta na rawa tana "Aunty Zahira Mai ya samu idonki Haka Mai ya Sameki Haka "?

Hannu kawai Zahira ke mik'a Mata hakane yasa ta Isa wajen Zahiran.

Tare da Kama hannun da take Mika Mata ta zauna a gefen gadon tana fashewa da mugun kuka Zahira kuwa tace "Nadeeya kimin addua mutuwa kinji Umma tace bazata min addua mutuwa ba Nadeeya jikina konamin akeyi wuyana ma kamar garwashin wuta aka sakamin Nadeeya kimin addua mutuwa kinji"

Ihu Nadeeya ta saka duk da zafin jikin Zahira Haka ta rungumeta tana "bazaki mutu ba aunty Zahira bazaki tafi ki barmu ba aunty Zahira waye ya Miki Haka Mai ya Sameki Haka"

Tuni.kannenta suka zagayeta suna kuka

Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na Dora alwala na dauko sabon doguwar rigar da ban taba sawa ba na zura a jikina na dauko sabon hijabina fari Kal shima na saka na na shimfida Sallaya a madadin na tada sallah kamar yanda nayi niyya sai na fashe da kuka na d'aga hannuna na hau rokon Allah akan ya kawowa zahira Agaji kuka nake akan Sallaya sosai goshina a kasa Ina rokon Allah ya kawomin d'auki halin Dana tsinci kaina a ciki.

Sallah danayi ma bazan iya cewa a nutse nayi ba ahaka na shafa na nade Sallaya na nufi wajen Yata da buta a hannuna na Mata alwala na zura Mata hijabi na jinginarta a jikin gado Ina "kiyi sallah Zahira a zaune ki roki Allah Yana jinki Yana Kuma ganinki"

Bata cemin komai ba Naga ta rufe idonta da Kamar Kara waje sukeyi

Bansani ba tayi Sallah ko batayi ba dak'yar na Kora kannenta waje na saka Nadeeya Dora musu abinci Dan kuka take sosai Kamar ma zahiran ta mutu

Yarana ba Wanda ya cin abinci har Waleed dake karaminsu danaga Yana buya a bayana idan Zahira ta kalleshi sabida idonta Dake bashi tsoro

Duk yanda naso taci abinci ko bud'e Baki batayi yi Banga ta zama ba hakane yasa na bazama nemo Mai taimaka min

Gashi lokacin farkon shigowar wayane ba mu Kai ga mallakar waya da har Zan samu hanyar da Zan sanarwa Naseer halin da muke ciki

A takaice wajen Mallam naje mijin aunty Ina kuka na sanar dashi halin da muke ciki mutanen arziki daga shi har aunty da wasu daga cikin Dalibansa Haka Suka biyoni gida

Duk wanda yaga Zahira sai ya girgiza da yanda ta dawo.

Mallam kansa hankalinsa ya balain tashi shima dayake Yana da ilimi tuni yasa na fito da Zahira na shimfidar da ita a tsakar gida Suka daura alwala shi da Dalibansa sun Kai goma suka hau karatun Qurani

Sai dai ba alamar Wai akwai abinda zai fito daga jikin Zahira

Hakane yasa ya d'auko kwanun Sha Naga Yana ta tofa adduoi daya shafe awa guda Yana Yi sai daya Gama ya bani Akan na shafa Mata a jiknta ko zamu samu jikinta ya rage zafi

Cikin Ikon Allah kuwa Ina fara shafa Mata jikinta ya hau rage zafi kanta ya shima Haka take Naga yata ta sauke ajiyar zuciya bacci yayi awon gaba da ita Ashe tunda ta hadu da Wanan masifar Bata bacci

Ko a fuskarta zaka ga alamar taji dadin Jikinta kamar wacce har ta samu sauki na hau Godewa Allah Ina Godewa Mallam Basu suka bar gidan ba sai wajen Sha daya har lokacin zahira na bacci

Cassette din Qurani na kunna Mata a gefen kanta daga Ni har Nadeeya bamu iya bacci ba Haka muka sakata a tsakiya muna kallo wajen daya naje na daura alwala na Zo na hau Kan Sallaya na tadda sallah

Nadeeya kuwa bacci ne ya d'auketa a Gefen Zahira

Wajen biyun dare Ina Jan carbi Ina kuka Naga ta bud'e Ido ni kuwa na zuba Mata Ido Ina kallon yanda ta zama kwarangwal Dan ba yanda ma zaka yarda itace
tashi tayi zaune tana wurga manyan idonta daya Sakani runtse Ido Dan sosai idonta yayo waje Kamar fitilar kwai

Ta zuro siraran kafarta kamar Kara Naga tayi waje Kamar iska zai d'auketa tsaf zaka kirga.kasusuwan jikinta

Ni kuwa na mike da Sauri Dan nabi bayanta sai dai Ina fita banganta ba hakane yasa na hau nemanta hankalina a tashe Ina kwalla Mata Kira

Nishinta danaji a Bayan fridge Dina dake Palo yasa na nufi wajenta da Sauri a tsugunne take a Gefen fridge din tana Kashi

Bance Mata komai ba na Bari ta Gama na Kamata ma kaita bandaki na wanke Mata Ina "ya Kika baro bandaki a tsakar gida Kika zo Palo kina Kashi Zahira Bata cemin komai ba har na kwantar da ita na koma palon na kwashe kashin na goge wajen
Chapter 36 · 0% Book details