Sashe 21
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Naseer murmushi yayi ya kalli gidajen dake jere da gidansa Yana "Ai inaga Alhaji ba Nan Dan kazo ba ko kila a mak'otan namu akwai Mai sunan Safiyya Dan wanan gidan da kake magana gidana ne Kuma ban siyarwa kowa ba"
Duk maganar Nan da ake mutumin na cikin Mota abinda Naseer yace ne yasa ya fito daga cikin motar Yana "Bangane gidanka bane baka siyar ba kaga na maka Kama da Dan shaye shaye ballantana kace bansan Mai nake cewa ba wanan dai gidan da ka fito daga ciki shine gidana da nake magana akai wajen sati uku kenan da biyan kudin gidan na Basu notice din sati hud'u"
Murmushin karfin hali Naseer ya Kara zuciyarsa na balain bugawa har ya wuce misali
Cikin rawar Baki yace "Waye ya siyar maka da gidan"?
"Safiyya ce dai ta siyarmin da gidan ita da Mahaifiyata Dan Nima ban yarda da Safiyya ba sai da muka Shiga har cikin gidan na duba koina na tabbatar da gidan yamin na Kuma tambayi mahaifiyarta Anya gidan nata ne tacemin Kar na damu gidanta ne na siya gudun ma.irin Haka yasa nak'i Bata kudin sai data Nemo shaidu da nima nasansu suka shaida ta siyarmin Nima na bada kudin na karbi takardun shaidun gida ya zama mallakina Dan Haka"
Naseer Bai tsaya saurarensa ba Kamar Wanda ake turawa Haka ya nufi cikin gidan Yana Jin duniyar na juyawa dashi
Direct d'akin Hajara ya Shiga data kasa zaune ta kasa tsaye Yana Shiga d'akin ta mik'e da Sauri tare da juyawa Naseer baya.
"Umma dagaske ne Kun siyar min da gidan da ya ragemin a rayuwata Gidan da shi kadai ne rufin asirina Umma dagaske ne Kun siyar"?
Naseer yace Yana dafe kirjinsa dayaji Ya Masa nauyi Yana ta sukarsa.
"Kayi hakuri Naseeru akan Dole muka siyar da gidanan Dan na d'auka guduwa kayi banida Mai bani kudi idan ba Kai din ba nayiwa Safiyya kayan daki hakane yasa na siyar Dan na fita kunya Amma sauran kudin na Nan zai isheni mu"
Fad'uwar Naseer da tunda tace sun siyar yaji Kamar an harbe Masa kirjin da har yau daya tsuffa idan Ransa ya b'aci Haka yake fama da ciwon kirjin.
Sam Bata San halin dayake ciki ba dayake juya Masa baya tayi sai dataji karar fad'uwarsa ta juyo hankali a tashe tayi kansa.
Naseer sallati kawai yake Yana juya Kai hannunsa dafe da kirjinsa dayake ji kamar zai fashe.
Kuka kawai yake yana "Umma Mai na Miki Haka a rayuwa kin rabani da komai Dana mallaka Umma iya sanina ban taba Miki komai ba Dana cancanci Haka daga wajenki sau daya nayi kuskuren da har gobe nake nadamarsa na marinki danayi shima wlh Umma bansan lokacin danayi ba Umma iya biyayya Ina Miki kin rabani da matata kin rabani da yarana bance komai ba iya Haka Bai Isa ba Umma sai da kika rabani da gidan daya ragemin a rayuwata da nidake muke ciki Umma Akan kayan daki Kika siyar da gidana Umma yanzu Ina kikeso mu koma innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma kin kasheni"
Naseer ke fada Yana dafe da kirjinsa
"Ka kwantar da hankalinka Naseer ba duk kudin aka siyawa Safiyya kayan daki dashi ba akwai sauran da zai Isa ka siyi karamin gida har aure ma sai kayi Bari kiga"
Hajara race da Sauri ta daga katifar sama da ta b'oye kudin da Safiyya ta Bata.
Ras gabanta ya Fadi a lokacin data ga ba kudin sai Yan dari bibiyu guda goma.
Cikin tashin hankali tayi wurgi da katifar ta hau duba koina tana ta Shiga uku ta lalace ba Inda Bata duba ba Amma Bata ga kudi ba
"Na Shiga uku Yarinya Nan ta cuceni shegiya tsinanniya Allah dai ya tsine Miki albarka Naseer ta bani kudin Kuma ta kwashe na Shiga uku na lalace
Hajara tace Tana fashewa da kukan bakinciki tare da zaman dirshan tana tsinewa Safiyya albarka.
Naseer kuwa ko kallonta baiyi ba ya mik'e hannunsa dafe da kirjinss dayake ganin Yana saki zai iya fadowa jiri na dib'arsa Haka yaje ya kwanta a d'akinsa ya hau kuka Kamar karamin yaro Dan gani yake kukan kawai shi zai saka yaji kirjinsa ya rage nauyi.
Hajara itama kukan taci ta koshi bakinta sai tsinewa Safiyya yake tana Shan alwashin samun kudin mota taje har calabar taci uban Safiyya.
Taya ma akayi ta biyewa Safiyya ta siyar da gidan da itama kanta shine rufin asirinta yanzu idan Mai gidan ya koresu Ina zata koma data ita har Naseer Bata tab'a sanin Haka Safiyya take da San Kai ba sai Yau.
Ya Zama Dole su San nayi kafin a koresu bakin cikinta ma shegen Dubu biyu da Safiyya ta ajiye Mata da ba abinda zai iya Mata.
Wajen karfe hudu na yamma ta fito daga d'akin tashin hankali da take ciki Bai Bari taji yunwa ba.
D'akin Naseer ta nufa tana zuwa ta iske jikinsa na wani irin rawa sabida zazzabin da ya rufeshi lokaci guda.
Ihu ta saka ta fada d'akin tana tab'a jikinsa ta d'auke da Sauri tana "Haba Naseeru Mai yayi zafi haka kayi hakuri bansan Safiyya Haka take ba da ban Soma biye Mata ba sam banyi tunanin yaudarata take ba kayi hakuri ka tashi kaji"
Ganin Naseer Kamar Bai ma San Inda kansa yake ba yasa tayi waje tana dora mayafinta aka.
Wani chemist taje dake kasan layinsu.
Dayake su biyu ne a chemist din ahaka ta roki dayan ya biyota har gida ya hau duba Naseer.
A takaice sai da Naseer yayi kwana uku a kwance ba lafiya a kwana na hudu yaji sauki saukin jikinsa kirjinsa ne dai har lokacin ya Masa nauyi.
Hajara ce ta ringa dawainiyya dashi Dan Dubu biyun dashi ta siya Masa magangunan
Har da girki ita ta ringa Masa wai duk Dan Naseer ya ji dadi.
Naseer kuwa ko San ganinta baya so yayi Dan shi kadai yasan Mai yakeji a kirjinsa idan ya tuna Wai wanan kantamemen Gidan nasa Mai part biyu da zai iya zama a bangaren da su Hajaran suke wanan Kuma ya zuba Yan haya ya samu kudi.
Ahaka ma filin tsakar gidan da girmansa da zai iya tasar daki biyu a ciki Amma ahaka mahaifiyarsa ta siyar masa da gida sabida kawai tayiwa kanwarsa kayan daki.
Hawayene suka zubo Masa ya runtse idonsa Yana Jin yanda kirjinsa ke Bugu a duk abinda mahaifiyarsa ta ringa Masa wanan yafi Masa ciwo Dan yanzu bashida komai a rayuwarsa.
Hajara dake zaune agabansa tana hada Masa shayi ganin hawaye na zubo masa ta hau magana tana "Haba Naseer Kayi hakuri Mana wlh Nima bansan yarinya Nan iskancin data min ba kenan da ban Soma biye Mata ba Dan Allah ka daure ka Zama namiji insha Allahu zaka samu fin wanan ita Kuma Safiyya wlh Bari na samu kudin mota har can zanje na kwashe Kayanta na siyar na kawo maka kudin shegiya tsinaniya uwar San zuciya kayi hakuri kaji Naseeru na maka ba daidai ba ka daure ka Sha shayin Nan tunda ka kwanta baka sa komai a bakinka ba ka taimaka ka Sha musan nayi Dan Naga Mai gidan Nan har ya fara kawo kayan gyaran gidan Jiya ma sai daya zo da alama bashida mutunci"
Naseer Bai ce Mata komai ya tashi ya shige bandaki.
Ya daura alwala yazo ya tadda sallah Yana ji kamar iska zata d'auke shi sabida rashin kwari.
A sallah ma sai dayaci kuka ya gayawa Allah halin dayake ciki yayi adduar ya shafa Hajara na zaune ta buga tagumi tana kallonsa.
Shi kuwa mik'ewa yayi ya fita batare da yace Mata komai ba duk da tana Masa maganar Ina zaije.
Daya fita ma opposite din gidansa ya zauna Yana karewa gidansa kallo ji yake inama mafarki yake ba dagske ya rasa wanan tangamemen gidan nasa ba daga Ina zai fara yanzu.
Abinda Umma ta Masa ba shi kadai ta cuta ba har kanta ta cuta sani ne batayi ba.
Mik'ewa yayi ya fita har bakin titi wajen wani dilali Mai siyan Kaya fairly use ya Masa bayanin Yana da kayan siyarwa na gida ya lissafa Masa Abubuwan gidansa Kama daga gadon da Hajara ke kwana har cokali Dan so yake yayi gwanjon komai ya siyar na gidan Dan Bai San Ina zai Kai kayan gidan ba tunda bashida gida yanzu.
Har gida suka zo yaga duk kayan ya musu kudi Wanda duk kayan ma tayin wulakanci ya Masa Amma ba yanda zaiyi ahaka ya siyar da kayan gabadaya ya kirga kudinsa ya bashi ya tafi tafiyarsa da minti ashirin sai gashi ya dawo da mai kurkura suka hau fita da kayan Naseer kuwa ya hade kayanshi Dana su Zahira a bako biyu jiri ke dib'arsa Amma ahaka ya hade kayansu ya fito dashi Bayan ya kwashi duk wani Abu nashi Mai mahimmanci
Hajara kuwa hankali a tashe ta hau tambayarsa ya taga Ana fita da Kaya Ina zasuje.
Tunda ya kwanta sai a lokacin yayi magana Yana "Umma duniya Zan Shiga na nemi kudi Dan kin rabani da komai banida gida banida komai Dan Haka Nima zanje na nemi shagon da Zan ringa kwana tunda banida gida yanzu"
"Naseer Mai kake cewa haka ni Kuma fa wajen wa zani Haba Naseeru yanzu Ni Kuma a wajen wa Zan zauna nidai na Shiga uku na lalace Dan Allah kayi amfani da kudin nan na hannunka ka Kama Mana haya Naseer kasan banida Inda zan zauna ko na koma calaba Naseer"
"Ki koma gidan Safiyya Umma Dan da duk kinyi wanan tunanin da Baki siyar da gidnan ba kin siyar Dan ki farantawa Safiyya Rai da ba ko sisinta a ginin gidanan Bata San da yanda na samu kudi na Gina gidana ba Umma toh gashi kin rufa Mata asiri tana gidan mijinta namu ya tonu Dan Haka Umma babu yanda zanyi dake Dan Nima shagon abokina zanje na ringa kwana Kinga bazai yiwu na tafi dake shagon abokina ba"
"Naseer nayi nadamar biyewa Safiyya kayi hakuri Ni nasan Kai Dan albarka ne bazaka Bari na tagayyara ba ka taimaka ka sama Mana wajen da zamu zauna"