← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 62

Sashe 60

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe dai yata tana da rabon aure daurin Auren Zahira tamkar Kara samun lafiya yayi

Godiya sosai muka ringa yiwa mahaifin Abubakar bakin Abubakar a washe dan murna.

A haka muka nufi gida cikin farinciki tun a hanya na fara sadaka a Raina Ina Godewa Allah.

Umarnin mahaifin Abubakar nabi Dana Isa gida na fito da duka kayana daya ce Kar na sake sawa Kar Kuma na bawa wani dan zai iya cutar dashi.

Dan kayan nawa ma an yi asiiri a ciki.

Naseer da kansa ya Kona kayana.

Yarana sai.murna suke na warke.

Bamu fadawa Zahira an daura Aurenta ba.

Sati biyu da samun sauki na aka cigaba da shirye shiryen auren Nadeeya Abubakar har akwatin kayan sawa ya kawo min

Ranar 15 ga watan biyar shekara ta 2010 aka daurawa Nadeeya aure

Aka hada da bikin Zahira da itama bata sani ba sai a satin auren Nadeeya kukan farinciki kawai ta ringayi tana a Ashe tana da rabon aure.

Cikin rufin asiri akayi shagalin bikin yarana suka tare a gidajen mazajensu alhamdulillah

Calabar

A ranar da mahaifin Abubakar ya karya asirin da Hajara tayi daddare Hajara na kwance tana bacci.

Taji kamar Abu ya ruguzo Mata a jiki

Azabar data ji.yasa ta bud'e idonta.

Kasusuwan jikinta Suka ringa kaskas Kamar Ana karyawa

A firgice ta mik'e zaune data ga kashin jikinta na murdawa shi kadai kafin ta ankara sai gashi ta karkace gabad'ayanta gabanta ya koma gefe idan kana kallonta a madadin a tsaye straight sai ta karkace Fuskarta ta koma gefe

Ihu ta saka da iya karfinta mahaukatan dake zagaye da ita Suka sakata gaba suna kallonta

Masu wucewa Kuma idan Suka ganta sai su tsorata dan Basu tab'a ganin mutumin daya karkace haka ba.

Wanan shine farin Shigar Hajara wahala Mai tsanani Dan mutane tsoron ta Suka koma yi ko tayi baran bata samu.

(Har yanzu wlh Tallahi baiwar Allah Nan a karkace take a fadar Naeema ko accident mutum yayi Bata Jin zaiyi karkacewar da tayi
Allah ya tsare Mana imaninmu na dai kusa gamawa Dan Safiyya da Hajara na rayye Basu mutu ba ba kuma su tuba ba yanda Naeema ta bani labari haka Zan Baku sai dai Kuma idan wani Abu ya biyo baya nayi alkwarin rubutawa insha Allahu)

*TALLA*
_Mai talla shike da riba_

*Mg's herbal whitening black soap*

Idan akaji gangami to tabbas akwai labari. Ina Amare, Uwargida kai har ma da 'Yan mata masu tasowa, hakika mata da kwalliya aka sanmu, shin kuna so ku kara kyau fatarku tayi luwai luwai ki zama 'yan caras kamar madubi?

To ga dama ta samu, mun zo muku da Sabulun Mg's a kan farashi mai sauki, duk wacce ba tayi anfani da sabulun nan ba an barta a baya, domin duk masu korafin cewar sabulan gyaran jiki basa Aiki to ina so ku cire Mg's a ciki domin shi kankat ne wajen mai da tsohuwa yarinya. Ko yaushe Mg's sai sambarka dan haka ku hanzarta ku samu naku, siyan na gari maida kudi gida, Mg's sabulu ne daya tamkar da dubu.

Masu bukatar fatarku tayi haske to Sabulun Mg's herbal whitening black soap ya waratar daku, jikin ku zai yi kyau da sheki da kamshi. Kayanmu baya bleaching organic ne, zai fiddo muku da ainahin natural beauty dinki ne, dan haka duk wanda ya gwada shi ne zai bada labari. Amare da sauran Mata kuyi kokari ku mallaki Mg's domin ba ruwanku da zuwa a dirje muku jiki zaku ga yanda fatarku zata dinga walwali. Ina masu.

Pimples
Tabo(spot)
Sunburn
Nankanwa
Dama duk wani matsalar fata kuyi kokari ku nemi soap din Mg's, insha Allah before 2weeks zai share muku hawaye, ku zama abun kwatance.

You have to try it and see for yourself 100% tested and trusted.

Soap price: 3k
Location: Kaduna
Muna turawa ko ina, amma delivery is not free

Mai so kindly WhatsApp message to 08062991549 or
Call 08064532391

_Note: Yan sauran state Babu in da zaku sami mg's herbal whitening black soap sai a number din nan, now Akwaisu available_yan kd akwai shops da zakusami sabulu ynx kuyi mgn 08062991549 abaku address
Masusan suzama distributors a other state uw kindly drop a message via 08062991549🤭

we can't wait to be a part of your beauty story😍
[8/26, 9:42 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

Page 64

Duk masifar da ta Shiga da b'acin rai bata taba tsintar kanta a farinciki kamar lokacin da Oban ya haska Mata rashin lafiya da Naeema ke fama dashi ba

A karyar Oban ce mata yayi shi yayi aiki akan Naeeema tayi ta rashin lafiyar har ta mutu.

Kamar wacce aka yiwa kyautar hajji da umara haka Safiyya ta ringa ji.

Da kuwa Naseer ya siyar da gidansa akan rashin lafiya Kamar ta taka rawa Bata da burin daya wuce har daya gidan su siyar su koma ba suda gidan kansu kamar yanda itama bata da gidan.

Idonta na Kan komai dake wakana dasu Naeema har irin wahalar da ake sha akanta.

Abubakar data ga Yana San Zahira Yana Kuma taimaka.musu yasa ta roki Oban akan ayi ta tsorata shi idan har yak'i janyewa Oban ya kashe shi

Haka kuwa akayi Oban ya hau tura Aljannu dan su tsorata Abubakar sai dai duk tsorata shi da suke ko gezau Abubakar baya yi daya tashi ma Kona Aljannun ya ringa yi yayi wa Oban barna sosai ta hanyar lalata Masa wasu kayan aikin nasa da Karfin Addu'a.
Duk yanda Suka so yin aiki akansa hakan baiyi tasiri ba har aka daura auren Zahira da Abubakar da yasa Safiyya tayi karamin hauka tana sumbatun tsinewa Naeema da ita rayuwar yaranta gashi a watse Amma Zahira tayi aure.

Dan Safiyya itama ta santalo Mata jika shegiya ga budurwar Bashir itama d'auke da ciki.

Duk an cike mata gida da shegun yaya

Gabadaya rayuwarta ta wulakance ta lalace ita da yaranta

Amma gashi zahira ta samu tayi aure kenan ma Naeema taci riba akanta

A hauakacen ta sa Oban ya Mata aiki akan Umar saurayin Nadeeya akan ya fasa auren Nadeeya sai dai tana ji tana gani aka daura aurensu.

Bakin ciki yasa ta roki Oban akan a kashe mata Umar dan da alamu Abubakar yafi karfinsu dan duk abinda suka ringa tura Masa baya tasiri akansa Nan kuwa basu San mahaifinsa ba karamin aiki yayi akansa ba ba iya shi ba har su Naeema.

Ba yanda ba suyi dan suga sun tab'a Zahira ko Nadeeya Amma Allah bai basu iko ba

Hakane yasa Safiyya ta so maida Nadeeya bazawara a washegarin da Nadeeya ta tare a gidan ta.

Wani Abu Oban ya bata Akan taje ta binne a tsakiyar titi kafin ta binne ta Kira sunan Umar sau uku

Indai Umar a ranar ya hau mota ya hau kan kwalta sai yayi mumunan hatsari.

Cikin mugunta ta binne kamar yanda ya umarceta

Ta koma gida tana murna bakin cikin da Naeema zatayi har Naseer idan suka ga kwana daya da tariyar Nadeeya mijinta ya rasu

Tana komawa gida ta iske Bashir a tsakar gida a zaune ya balain nutsuwa kamar bashi ba.

Sannu da zuwan da ya mata yasa ta daskare waje daya tana murza idonta dan ta gaskata Bashir danta dai take gani ba wani ba

Murmushi ya Mata Yana ta daina mamaki shine sati biyu da yayi baya nan Allah ya shiryeshi ya Kuma Gane duk abinda yakeyi ba daidai bane daga Yau ya daina.

Safiyya tsabar farinciki kuka ta saka tana shiwa Bashir albarka

Fadar farinciki da take ciki ma Bata bakine Ashe Bashir dinta zai tab'a nutsuwa haka har ya dawo hayyacinsa

A takaice hirane ya barke tsakanin Safiyya da bashir

Safiyya ta ringa ji kamar ta goyashi dan farinciki tuni ta hau tsare tsare a Zuciyarta.

Murna da take ciki yasa tace Masa Bari ta Shiga daki ta yo musu cafene

Bashir kafewa yayi ta bar kudin shi zai yo Mata cefanen.

Safiyya da kallo ta bishi har ya bar gidan Kaunar Bashir na balain mamaye Mata zuciya kaf yaranta ba Wanda takeji a ranta kamar Bashir.

Fitarsa da minti goma taji hayaniya a waje.

Kafin ta gane Mai ke faruwa har mutane sun duru cikin gidanta suna zabga sallati
Hankalinta a balain tashe ta fara tambayar me ke faruwa

Sai dai baa iya bata amsa ba in Banda wani daya hau Jan hannunta.

Kamar sokuwa haka tabi bayansa gabanta na fad'uwa.

Mutanen da suka cika titin da ta binne abinda Oban ya bata yasa gabanta tsananta fad'uwa dak'yar ta suka bata hanya

Bashir ne kwance cikin jini male male

Idonsa a bud'e Yana kallon sama kana ganinsa kasan rai yayi halinsa.

Wani razanannnen ihu ta kwalla ta zub'e a kasa.

Bata Kara sanin Inda kanta yake ba har aka yiwa bashir sutura aka binne shi

Ranar sadakar uku ta farfado Ta na ihun Kiran sunan Bashir ta fara k'ok'arin yin waje

Sai sumbatu take tana ba Bashir tace ya mutu ba mijin Nadeeya tace Oban ya kashe Mata.

Tab'in hankali da ta dan samu yasa ta hau tona wa kanta asiri tana Naeema ta cuceta Oban ya cuceta.

Dak'yar aka Mata alluran bacci dan fusgewa take zata fita waje.

A takaice sanadin dan samun tab'in hankali Safiyya kenan

Dan har gobe bata cika hankali ba ita kadai haka za tayi ta zuba surutu tana fadar Abubuwan da tayi idan haukan ya motsa mata .

Oban da take shuka tsiyar dashi data koma wajensa a kwance ta sameshi ya kumbura yayi himmm Yana zabga wani irin doyi

Ita kanta Safiyya baka Isa tsayawa kusa da ita ba sabida warin da takeyi

Wata daya da rasuwar Bashir

Tana zaune ta zubawa waje daya Ido

Hankalinta ya dan dawo jikinta yaranta duk take bi da kallo da jikokinta.

Ita bata ga ma ribar da taci a rayuwarta ba Bashir danta namiji tilo Daya fi soyuwa a gareta ya tafi ya barta a lokacin da hankali ya fara zuwar Masa ya Shiryu

Yaranta biyu daga mahaukaciya sai Mai bin maza
Chapter 60 · 0% Book details