Sashe 47
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina jinta a raina sabida yanda take damuwa da damuwata ko Yaya nake cikin damuwa tana ganewa
Sai dana share hawayen daya zubo min nace "Mama Waleed a yan kwanakin nan naga ya canja min Kamar ba Waleed Mai sanyi hali da ladabi da biyayya ba
Mama kema shaida ce a dan zaman da kikayi nasan zaki fuskanci halinsa yarone Mai gudun fushina
Mama wai yau ni yaron nan yake yiwa rashin kunya har Yana Kar in takura masa bazai je makaranta ba iya wanan bai Isa ba sai daya galla min harara Mama Kamar ba Waleed Dina ba ya canza gabad'aya"
Na karashe Ina fashewa da kuka
Mama cikin damuwa ta hau kwantar min da hankali tana "karki damu mama na kila ya fara haduwa da mugayen abokanai ne ko Kuma wani abu ke damunsa bamu sani ba ki share hawayenki ki bar damuwa idan ya shigo Zan Masa magana ai bai tab'a Miki haka ba ki bari mu bincike shi a hankali muji mai ke damunsa"
"Mama ko shima Aljannun ne Suka shige shi wlh ba haka Waleed yake ba Zahira ma mama Kinga tunda Suka bar jikinta bata koma yanda take ba itama yanzu wani irin hali ta koya kina cemin mu bita a hankali,mama Ina tsoron wani abu aka yiwa yarana
ba abinda umma da Safiyya baza su iya aikata min ba bare idan sunga alamar anyi nassarar cire Aljannun daga jikin Zahira"
"Karki damu Mamana ita Zahira dama sai a hankali zata dawo daidai indai na samu tana Shan ruwan adduoi da nake baki da turaren wuta zata dawo daidai
Shi dai babana nake so ki bari mu bincika abinda ke damunsa wlh duk abinda Kika ga ya samu bawa rubutacce ne daga Allah wayanda kike tunani basu Isa su Miki komai ba sai idan Allah ya hukunta dama hakan sai ya faru tunda mumuni dole ya yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka alhamdulillah daga labarinki Allah na kaunarki mamana tunda duk Kika iya tsallake duk wani sharri da aka nufeki dashi Allah daya jarrabceki yana ta kareki ba hanyar da basu bi ba dan su ga bayan ki Amma da ikon Allah gaki nan a rayye ba abinda ya Sameki insha Allahu yaranki ma Allah zai karesu burina kawai ki dogara da Allah kiyi ta yiwa yaranki addua gabadaya.
Da nasihar Inna Amina naji sausauci a zuciyata na fito na Kai Mana abin karyawa Muka karya a tare duk da zuciyata cike take fal da damuwa.
Ko Ina Waleed din yayi yanzu Zahira dama tun safe bata tashi daga bacci ba Ina mamakin sababin halayyen da nake gani a tare da ita bansan na saka damuwa a raina hakane yasa muna gama karyawa da Inna Amina na d'auko qurani na dan ta karamin sosai nake Kara amfani da damar da na samu wajen Kara neman ilimi Kuma alhamdulillah Ina fahimta.
Karatun da mu kayi tare ya sanyaya min zuciya sosai wajen Sha daya na fito daga d'akinta ita Kuma tace min zata dan kwanta tayi bacci tunda bata fiye baccin ba ta Kan rayya daren itama.
Ina fitowa naci Karo da Zahira ta fito da Kofin kunu da alala ko kallona ba tayi ba ta fara k'ok'arin wuceni
Haka kawai na kasa yarda wai Zahira ta ce ta dawo haka Koda lokacin da Aljannun Suka fice a jikinta magana ne kawai naga Bata yi ta zama shiru shiru,amma tana nan da sanyi halinta da ladabi da biyyaya na kasa gane Mai yasa kwanankin nan ta kara bijiro da sababin halayye da na kasa ganewa
"Zahira baki iya gaisuwa bane wai Mai yake damunki ne"?
Ciki ciki ta gaisheni ta shige daki ba Kuma tsayawa tayi ta gaisheni ba Sam ban yarda abinda suke shigeta suka fita ke saka ta haka ba dan da suka fita ma ta dawo min yanda take magana ne kawai bai dameta ba
Kaina dana ji ya fara min ciwo yasa ban tsaya takura kaina da tunani ba na hau aikace aikacen gida da kafin ta Kara canjawa tana Tayani
Hankalina Sam baya jikina Yana wajen Waleed daya fice bai dawo ba dan baya yawo daga gida sai makaranta abokinsa guda ne dan yadikko Abubakar a iya sanina ma dashi sai dai abubakar din ya zo wajensa bai fiye zuwa ba har tsokanar sa su Nadeeya keyi akan ko dan ball dinan da aka San maza nayi shi baya yi Yana nanike dasu Yana koyan jajjage da yanka albasa.
A haka na gama girkin Rana.
Ina zuba idon dawowar yarana har da Waleed da hankalina yafi karkata wajensa.
Sai dai har Suka dawo suka ci abinci Waleed bai dawo ba.
Sai tambaya ta suke Ina yaje nace musu bansani ba su dai dubo min gidan yaddiko ko Yana can wajen Abubakar.
Dawowar Humaira aguje tana hakki tare da cewa "Umma Kinga Waleed can a tsakiyarsu shagari Yana ta Wasa da Kare nace kina kiransa ko kulani baiyi ba Umma shagari fa dan gidan dan kwaya"
Tunda ta ambaci shagari yaron daya addabi Yan unguwar da fitina naji gabana ya yanke ya fadi sallati na hau yi
Nadeeya ta mik'e da sauri tana "Humaira kina da hankali kuwa Waleed din Kika gani da shagari"?
" wlh Aunty Nadeeya Waleed na gani har na Masa magana ya shareni"
"Nadeeya bata iya magana ba daga ita sai doguwar rigarta tayi waje da Sauri"
Nima tsintar kaina nayi da binta a bayan Ina sallati
Shagari sa'an Waleed ne karamin yaro da bazan iya kirga sau nawa aka Kai shi a ka kulle ba sabida rigimamme ne na tashin hankali har d'auke d'auke Yana yi ga dukan Yara fitinanne ne na karshe shaye shaye ne kawai bamu sani ba Yana Yi ko baya Yi
A zaune yake a tsakiyar su shagarin Yana ta Wasa da karnukan
Nadeeya a tsawace ta Kira sunansa tana yazo nan
Waleed yarone Mai girmama na gaba dashi dan daidai da Raheema da yake bi aunty Sama aunty kasa yake ce mata ga mamakina ko dagowa baiyi ba ya kalli Nadeeya
Data ishe shi ma sai cewa yayi "mallama karki takura min idan Kuma Zaki iya daukana zo ki d'aukeni"
Nadeeya sakin baki tayi tana kallonsa ta juyo ta kalleni......
*A yi maneji wlh abubuwa sun Sha kaina a ringa hakuri dai Kar ayi rushing Dina Ana rushing Dina zanyi a gurguje wlh alhalin labarin Bai Kai a Gama ba yanzu nan nayi typing dan karku jini Shiru Ina samu sarari gobe xaku jini idan ban samu ba ayi hakuri jibi na bada Mai yawa*
[8/13, 6:47 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Thanks all for d bday wishes and prayers I appreciate wanan Shafin na kine Ayshatfareeda tnks for d gift am greatful*
Page 58
Sosai na rik'e kaina na tsaya akan kafafuna sabida rawar da jikina keyi jiri na d'ibana
Ban saurari Nadeeya da itama ta daskare a tsaye ta juyo tana kallona ba sabida mamakin abinda Waleed yayi.
Duk da inada tsoron Kare haka na daure na isa wajensu
Waleed bai ji dar din ganina ba sai ma shagari da sauran abokanan sa ne Suka dan sunkuyar da Kai suna gaisheni dan ni nasan Ina dan musu kwarjini.
"Waleed zo ka wuce mu tafi gida"
Jim yayi kamar bazai tashi ba har sai da shagari ya Masa magana ya mike Yana wani fufusgewa yayi hanyar gida
Na rik'e hannun Nadeeya data kasa katabus sabida mamakin abinda waleed yayi.
Ni kadai nasan mai nake ji a Zuciyata "Umma Mai ya samu Waleed haka? Mai ya canza shi lokaci guda"?
Ban samu zarafin yiwa Nadeeya magana ba muka cigaba da bin Waleed a baya har muka Isa gida.
Butan dake tsakar gidan ya fara ball dashi kafin ya karasa dakin
Minal kuwa ta kasa hakuri ta bi bayansa tana "Kai Waleed kana da hankali kuwa?Mai ya had'aka da shagari dan iskan yaron nan"?
"Karki Kara cemin banida hankali mallama"
Waleed yace Yana wani hucci kamar sa'arsa
Da yake bai Saba da musu rashin kunya ba Sam haka ne yasa abin ya musu wani banbarakwai.
Nadeeya ta fada d'akin a zuciye kafin na hanata ta wanke shi da Mari
Minal kuwa ta hau zaginsa ita da humaira.
"Wlh duk wacce ta Kara zagina sai na rama duk wacce hannunta ya Kara tab'a jikina wlh sai na rama"
Waleed yace yana zuba musu harara.
Daga yanda yake nasan zai aikata zuwa lokacin na yarda Waleed ba'a hayyacinsa yake ba D'ana an tab'a min shi dan ba haka yake ba tunda na haife shi bai tab'a gwada rashin kunya da naga Yana yi ba yau.
Ina tsoron Umma da Safiyya suna cikin hannu a canzawar Waleed D'ana guda tilo da nake alfahari da hankali da tarbiyya dana bashi,idan har zasu iya yiwa Zahira turen bakakken Aljannun Mai zai hana su tab'a min Waleed tunda sun San namiji ne zuwa yanzu nasan sun gane an raba Zahira da Aljannun hakane zai saka su ce bari su dawo Kan Waleed na fahimci sun San rauni na akan yara na ne bana iya jure abinda zai tab'a su kila shiyasa Suka kara tab'a min Waleed.
Tuni na tsayar da tunani na akan Waleed ba'a hayyacin sa yake ba duk Abunda yake yi yanzu kila ba a hankalinsa bane
Da wannan tunanin na fara k'ok'arin tsawatarwa su Nadeeya da fad'a ke neman kaure musu suna neman dukan Waleed dake ta zuba musu rashin kunya da yake Yana da jikin girma Zahira da Nadeeya ne kawai zasu gaya masa tsayi Amma duk yafi su Humaira tsayi
Zagin sa da humaira ta yi ya rama a take yasa suka rufeshi da duka
Kafin na Isa wajensa ya watsar dasu ya cakumo humaira ya hau zuba Mata naushi daya daga min hankali
Nayi wajensu a guje duk yanda muka so raba Waleed da Humaira kasa wa muka yi karku manta sai da aka haifi Raheema kafin Waleed akwai tazaran shekaru a tsakaninsu.