← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 62

Sashe 19

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nadeeya uwar surutu take ta hau zuba tana surutu har da dukan da Safiyya ta Mata jiya ta sakata wanki

Naseer kuwa yace mata "uwar surutu fita waje kiyi Wasa daga zuwanki kin hau surutu".

Kofin shayin ta d'auka tayi waje.

Ni kuwa nasan dalilin dayasa ya koreta

Sai data fita na juyo Muka hada Ido
Na saki murmushi na gaishe shi bai amsa ba ya Ajiye Waleed dake hannunsa ya nufo wajena

Wai sai na tsinci kaina Kuma da Jin kunya Yara shidda Yana Abu kamar wani saurayi ko sababin Aure

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya rungumeni Nima rungume shin nayi Dan nayi kewarsa har ga Allah muna San junanmu Umma ce ta dage sai mun rabu

Mun dau tsawon lokaci a Haka sai danaga Yana neman wuce gona da iri na janye na koma gefe baa San Ransa ba ya koma bakin gadon ya zauna ya Kara d'aukar Waleed Yana "Ashe a garin Nan kike shine baki gayamin ba ai da tuni Nazo"

"Ai bazan so kazo ba sabida Kar Umma tagane Ina Nan din Dan nasan Idan tasan Ina kano Kai kanka bazaka samu kwanciyar hankali ba

Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya hau karewa ko'ina kallo Yana "Naeema kinyi kokari duk da Baki tafi da komai ba shine har Kika siyi kayan gida Haka Ina yaran nawa suke ganinki ma yasa na manta ban tambayesu ba"?

"Suna makaranta"

Washe baki yayi cikin murna Yana "Allah ya saka da alheri ya Kara bud'i naeema hakika ke matar rufin asiri ce Umma bansan Mai yasa ta kasa ganin haka ba.

Yanzu ma Naga engine dinki ma biyu anan har da shago a k'ofar gida

Gyada Masa Kai nayi na hau bashi labarin komai har gidan da muke ciki yanda na siya da kudin gadona.

Sosai ya ringa murna yanda Allah ya bud'amin yace "Ni kuwa ba irin wahalar da ban Sha ba Naeema Amma kudi yak'i samuwa aikin ginin ma da nakeyi wlh bai taka Kara ya karya ba Nima kudin da Kika ajiyemin naso Na juya Amma abin bai yu ba"

Murmushi nayi Ina "Karka damu Allah na sane dake watarana sai Labari insha Allahu ka cigaba da gayawa Allah"

Gyada min Kai yayi ya nuna min manyan ledojin daya zo dasu Akan na duba.

Bud'ewa nayi na hau fito da kayan ciki

Kayan sawa ya jiddowa Waleed su zahira ma Bai barsu a baya ba sai turmin zani da undies da ya siyomin nima.

Dagowa nayi da zumar nayi magana ya girgiza min Kai akan Kar nace komai.
Idan nace banyi murnar ganin mijina ba nayi karya Ido nake ta daukewa da naga Yana ta nunamin Yana bukatata Dan ban shirya tarben nasa ba haihuwa na Allah ne bana San nayi ciki yanzu kullum adduata ma Allah yasa haihuwa ta tsayamin kenan

Duk yanda naso Bijirewa sai da na barshi ya samu nutsuwan

Nayi sauri na fada bandaki nayi wanka na fito shi Kuma bacci ne yayi awon gaba dashi

Hakane yasa na dau Waleed muka bar d'akin na rufo Masa Kofa

Waje na fita na tarar da Nadeeya nata zuba ita da Isihu ga layin markade Nan suna jirana

Dan shagon ma a cike yake da mutane masu siyan Abu

Isihu na fama da mutane ahaka yake biyewa Nadeeya dake ta bud'e alewa tana Sha

Tsawa na daka Mata Akan ta fito Dan Nadeeya dai ba yarinya bace sosai

Engine na kunna nace ta hau markaden Dan wani zubin Tana Yi tsayine dai Bata dashi sosai Amma inta taka Abu shikenan

Sai danaga ta markada biyu

Naga Kuma ta markada yayi laushi.

Na koma kitchen na fara had'a hadan girkin Rana

Yanda dai na Saba Miya Mai yawa anan ma Haka nakeyi Dan nafi ganin aukin kayan miyan idan na siya da yawa ganin inada miyan yasa na Dora Mana shinkafa.

Na fito wajen Isihu na bashi dari biyu ya siyomin naman Miya

Wanda a lokacin Naman dari biyu Mai balain yawa ne

Sosai na tsinci kaina cikin farincikin ganin Mijina da kuma iyalina guri daya yanda nakejin kadaici tunda na dawo gidanan

Zuwan.naseer yau yasa naji na daina Jin kadaicin

Inama mu dawwama Haka Astagafurullah a wanan lokacin har sai danace inama Umma ta mutu mu samu kwanciyar hankali Dan itace babbar matsalar mu.

Naseer kuwa baccinsa yake Sha Mai dankaren dadi daya Dade baiyi irinsa ba.

Dawowarsu Zahira daga makaranta da ihun murnar ganin Nadeeya yasa ya farka daga baccin daya daukeshi.

Mik'ewa yayi zaune Yana murmushin Jin dadi Dan har ya fidda rai Kara kasancewa da iyalinsa waje daya rigarsa ya saka ya fara k'ok'arin fitowa.

Su Zahira suka Fado dakin gabadaya suna ihun murna Nadeeya tace da abbansu Suka zo

Naeema kuwa duk yanda taso hanasu Shiga d'akin ko sauraranta basuyi ba Suka fada d'akin

Cikin murna duka Suka rungumeshi.

Shima Naseer cikin tsananin farinciki ya rungumesu sai dayaga suna neman kayar dashi ya janye jikinsa ya zauna a gefen gadon hannunsa cikin Na Raheema dayaga har wani kib'a tayi sabida kwanciyar hankali

Binsu ya ringayi da kallo cikin tsananin farinciki ganin yanda Suka canja gabadaya sunyi fes dasu ba Kamar lokacin da suke can wajensa ba

Zahira har canjawa tayi a idonsa ta zama budurwa Dan ita Bata Yi haukan da taga kanenta nayi ba inama ya dauwaama Haka daga shi sai iyalinsa da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi duk Wanda ya tsinci kansa da karayar arziki irin nasa mutum.kan dauwaama bashida wani buri daya wuce kudin su dawo wajensa kota halin k'ak'a ne Amma shi karayar arzikinsa Bai dameshi Kamar yanda rabuwa da iyalinsa ya dameshi ba.

Da tarin kudi gwara ya dauwama da iyalinsa cikin rufin asiri.

Sai da Naeema ta shigo d'akin ta koresu kafin Naseer ya samu ya Shiga wankan ya dauro alwala

A palon gidan yajasu Sallahr azahar.

Suna iddarwa Zahira taje kitchen ta d'auko musu abinci har da zobon da Naeema ta had'a.

A faranti daya sukaci abincin gabadaya duka fuskarsu dauke da farinciki Naseer da Naeema ji suke.inama su dauwaama Haka ba abinda zai sake rabasu.

Su kansu kasancewarsu waje daya yasa yaran cikin tsananin farinciki sai cewa suka Abba Dan Allah ka zauna anan Kar.ka Kara komawa.

Yinin bikin da Naeema Bata je ba kenan

Bayan tafiyar yaran islamiyya har da Nadeeya

Hira Naseer da Naeema suka.hau yi Inda Naseer Duk yake Bata labarin halin da yake ciki da Hajara da yanda ta matsa Masa yayi wa Safiyya kayan daki.

Sosai nayi murnar da auren da Safiyya zatayi Dan gani nake Rabin matsalar mu ya k'au sai dai Yar muryar da Naseer kemin akan idan inada kudi na bashi ya Basu zai bani idan ya samu yasa na hade girar sama da kasa nace Masa banidashi Naga duk halin da muke ciki su suka jawo Mana ko Naman jikina nake yanka musu ba burgesu nake ba Dan Haka ko sisina bazan iya bayarwa ba

Naseer Bai ja zancen ba dayaga yanda na hade Rai muka cigaba da Hira da aka fara kawo markaden yamma kuwa shi yaringayi Ni kuwa na Dora Mana girkin dare

Dan inaso ya cika cikinsa kafin ya tafin nasan yanzu tunda yasan gida zai na zuwa ganinmu akai akai hankalina yanzu a kwance yake.

Sai dai me a lokacin da muka ci abincin daren da nayi tunanin Naseer zai tafi k'in tafiya yayi yacemin kwana zaiyi na Bari ya Dan samu kwanciyar hankali na kwana biyu Dan idan ya koma gidan ma yasan bashida kwanciya hankali Umma Sako shi zatayi a gaba.

Ni kuwa.dage Masa nayi ya tafi Dan idan Bai tafi ba Umma zata xargi Yana wajenmu kafin kaceme zata gano Inda muke.

Ba yanda banyi ya tafi ba yak'i dayaga ma na dameshi sai ya shige daki ya barni dayake a tsakar gida muke Zaune.

Ba yanda na iya ahaka na hakura yarana Suka kwana a d'akin da hassana ke kwana nikuma da Naseer da Waleed muka kwana a nawa d'akin

Namiji a gida ma wani abune Dan a ranar ko juyi banyi ba har gari ya waye Ina rungume a kirjin mijina.

Har makara nayi Dan sai wajen bakwai da rabi na farka.

Agurguje nayi Sallah na fito sabida Na Dora musu abinci su karya su tafi makaranta.

Sai dai Ina fitowa ma na tarar suna cin abincin sun ma saka uniform sosai naji dadi Dan yanzu Zahira duk ita kemin komai tama Riga da tasan duk abinda nakeyi da safe Inda yarinya ta Kara kwanta Min arai fiye da sauran kanennta kenan.

Nadeeya ce kawai Bata saka uniform ba hakane yasa na Shiga na koma d'akina na dauko uniform dinta na Bata Dan Dama an bani uniform dinta littattafai ne ban siya Mata ba

Sai da suka shirya tafiya na koma daki Naga har lokacin bacci Naseer keyi Bai tashi ba
Tashinsa nayi na fito na raka su har makaranta na karbawa Nadeeya text books Dan na Bata littattafai da pencil

Primary 4 aka Kai Nadeeya da aka Mata gwaji.

Sai da duk suka Shiga aji na dawo.

A takaice tun Ina damun Naseer akan ya koma sabida Kar Umma ta gano muna tare k'i yayi akan Dole na hakura ya Mana sati daya

sati dayan da naji inama mu dawwama Haka batare da ya Kara Mana nisa ba inama Umma ta Sanya Mana albarka Naseer ya ringa Zama a shagon k'ofar gida.

Ni Kuma na ringa markade Ina kananun Sanaa a gida da nakeyi yanzu kudi na shigomin da nasan sai munfi kowa farinciki tunda munfi karfin ci da Sha alhamdulillah

Shima Kamar bazai tafi ba sai Dana karfafa Masa gwiwa akan ya tafi idan yaje yace Abuja yaje neman kudi na Kuma bashi Yan kudaden dai da Bai taka Kara ya karya ba.

Dan sati dayan dayayi har Dan murmurewa yayi.

Sai daya hau taxi na dawo gida duk jikina ba dadi

Dan nasan yau sai dai na rayya Daren dadin ma.danaji yace zai na zuwa ganinmu kullum idan Bai zo bama kullum xai na zuwa akai akai

Safiyya

Sosai ta Sako Hajara a gaba da kananan koke koke Akan Aurenta na matsowa Anki a Mata kayan daki
Chapter 19 · 0% Book details