← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 62

Sashe 8

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nikam a wanan gabar sai dai nace Alhamdulillah Dan kudi ko ta Ina shigomin suke abinda yake damuna Bai wuce kewan yarana danake kwana Ina mafarkinsu ba wani zubin a mumunan yanayi wanan Abu shi yake hanani sukuni ko abinci bana iya ci.gashi dai komai na samu cikin rufin asiri Amma tunanin yarana ya Sakani balain Rama Nafi tunanin Zahira Dan jikina na gayamin tana Shan wahala a hannun Umma da Safiyya Koda kuwa Naseer na nan.

Sau uku Ina zuwa unguwar da likkaf na tsaya a k'ofar gida Naga ko Zan ga wani ya fito daga gidan a cikinsu sai dai bana ganinsu sai dai Naga Naseer daya balain Rama ya fita hayyacinsa sosai yake karyamin zuciya idan na ganshi ahaka zan karaci tsayuwata idan na gaji na karasa gidan Aunty tacemin Kar na damu dazu ma tagansu lafiya Lau suke ba Abunda ya samesu har tambayar Zahira tana yi dake da balain zurfin ciki tace mata ba komai.

Ahaka Zan dawo da tunaninsu a Raina Nima rashinsu kusa Dani ne ya saka Ni mugun Rama Dan Sana'ar tawa Dan hassana na rik'ewa ne da bazan iya tab'uka komai ba a yanzu da aka tafi wata uku rabona da yayana naji bazan iya jurewa ba Ina bukatar ganinsu ko ta halin Kaka hakane Yasa na yanke zuwa gidan aunty idan sun zo islamiyya nagansu Koda daga nesa ne.

Naseer..........
[7/1, 10:14 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 37*

*Naseer*

Tijjani cikin tsananin murna ya rik'e Hannun Zahira da Nadeeya yace su Shiga daga ciki

Naseer ya girgiza Masa Kai Akan bazai shiga ba ya dai Shiga da yaran ciki su gaida Murjan

Tijjani girgiza Kai yayi Yana wlh sai ya shiga ciki Taya ma zai Zo gidansa Bai Shiga ba

Akan dole Naseer ya yarda suka shiga ciki Tijjani sai washe baki yake cikin murna.

A tsakar gida Naseer ya coge.

Tijjani kuwa sanin halinsa yasa ya dau babbar tabarma ya shimfida Naseer ya zauna shi ma ya zauna ya hau kwalawa Murja Kira Su Zahira kuwa sai kalle kalle suke suna daga gefensa hannunsa cikin Na Nadeeya.

Yana tambayarsu Makaranta

Murja fitowa tayi tana Hamma da cikinta da baifi na wata biyar ba ta tsani tana bacci a tasheta ko kad'an batasan da zuwan su Naseer ba hakane yasa ta fito da Daurin kirji

Ganin Kuma Naseer Bai saka ta koma ba illa yatsina fuska da ta farayi tana karewa Su Zahira kallo da Tijjani keta washe baki yana cigaba da Jan su Zahira da Hira Naseer kuwa kansa a sunkuye yake so yake idan matar gidan ta fito su ka gaisa sai su fita da Tijjani waje suyi magana dake tafe dashi.

Tijjani kuwa sai daya d'ago yaga Murjan ta daga labule daga bakin kofa ta toge

Daga yanayin ta yasan Yan rashin mutunci ne Suka motsa hakane yasa ya mik'e ya Shiga ciki tare da Jan Murja su koma ciki yayi kasa da murya Yana "Ya Ina kiranki kizo ki gaisa da yayana zaki kame daga bakin kofa shine fa yayana Naseer danake baki labari wadanan yayansa ne Dan Allah ki Sako hijabi kizo ku gaisa

Bata ce komai ba ta koma daki ta sako hijabin a rayuwarta ko kad'an Bata so wani ya rabesu har Tijjani ma bataso.taga Yana muamalla da mutane Dan ko abokaina ma cikin makirci take rabasu.

Idan kaga wani a gidan toh danginta ko kawayenta ne Amma Tijjani kam bataso wani nasa yazo wajensa hakane yasa ta Sha mugayen alwashi idan tsautsayi ya sa su Hajara suka Kara dawowa gidanta sai ta musu abinda har su koma ga Allah bazasu manta da ita ba.

Tijjani kuwa Yana fitowa Bai tsaya jiran fitowar Murja ba Dan ya Riga da yasan halinta ruwa da abincinsa ya d'auko yazo ya Ajiye a gabansu Naseer Yana yayi hakuri yanzu murjan zata fito yasan halin masu ciki.

Daga Nan ya dau plate ya bud'e flask din ya hau zuba shinkafa da wake da akayi jollof dinsa da bushashen kifi

Murja kuwa har wani turus tayi dan bakin ciki Dan tana da balain rowa ko wani ne ma yazo daga gidansu Haka zai karaci zamansa ya tafi batare da ta Masa tayin abinci ba ko da kuwa Tana cikin girkin kazo zata iya gwammacewa ta zauna da yunwa har sai ka tafi.

Dak'yar ta saki Fuskarta
Ta tsugunna daga bakin kofa ta hau gaida Naseer cikin faraa

Naseer kuwa ya d'ago ya amsa cikin sakin fuska Yana Dan karantar yanayin Murja a fuska dai Kamar babu ruwanta zatayi saukin Kai hakane yasa ya Dan ji sanyi a Ransa

Bayan sun Gama gaisawa ta koma ciki ta lab'e a jikin labule tana kallon

Zahira da Nadeeya dake ta zabga Loma Sabida yunwar da suke ji Dan uniform kawai suka cire Hajara ta Dora musu talla Bata Bari sun ci abinci da Naseer ya boye musu a daki ba dan waje na musamman Naseer yake boye musu abinci a d'akin da iya su zahiran ne kawai zasu San abinci ne a wajen sabida Kar ma Hajara ko Safiyya suzo d'akin su dauke

Kamar ta fashe Dan bakin ciki shi kuwa Naseer ture abincin da Tijjani ya ajiye daga gabansa yayi ya gyara murya ya Dan fara bawa Tijjani labarin duk halin da yake ciki da tafiyar Da Naeema tayi Sabida masifar Mahaifiyarsu da yanda itama Safiyya take cin zalin yaransa har zuwa Kan tallan da Mahaifiyarsa take dorawa yaransa da yasa ya zarto gidansa dasu.

Tijjani shima labarin irin zaman da sukayi da ita ya bashi a karashe da "Wlh Naga bazan iya ba nace su tafi Dan wlh bazan iya jure abinda kake iya jurewar ba Umma a madadin ta ringa rike girmanta tana kwantar Mana da hankali sabida halin da muka tsinci kanmu na babu wanda duk ita ta jawo Mana fa hakan Bai isheta ba sai ta daga Mana hankali ba irin surutan da bata yimin Akan na rabu da Murja ba daga Aurenmu fa Ni ban taba ganin Mai irin Halin Umma ba wlh ita Kuma shegiya Safiyya a madadin ta ringa Gaya Mata gaskiya shine take tunzurata kamin daidai da ka Hana ta dorawa su Zahira talla Dan nikam bama Zan iya da ita ba Dan da nine ma wlh siyar da gidan zanyi na gudu da yarana k'arfi da yaji kana zaune kalau da matar rufin asiri ta rabaku toh Yaya yanzu wane aiki kake yi Taya zaka ringa aikin lebura dake da wahala nawa ma kudin yake da zai isheka ka kula da yaran nan.mai zai Hana ka nemi aiki wani wajen ko Allah zai saka ka Dace Kamar yanda Nima Allah ya taimakeni na samu aiki a wani company robobbi a sharada duk sati suna bamu Dubu biyu karshen wata Kuma su biyani Dubu goma da zaka samu irin wanan aikin Yaya nakega da yafi nima wani ne ya nemo min aikin Zan Masa magana idan Allah yasa. An Dace sai Kai ma ka ringa zuwa da Wanan aikin wahalar da kakeyi.

"Tijjani Ina neman aikin samun ne dai banyi ba bazan iya kirga guraren Dana Kai takarduna ba Amma har yanzu baa Dace ba ya zanyi dole na ringa leburancin mu samu na abinci.

Yanzu dai abinda yasa nazo wajenka so nake ka taimaka min Dan Allah Yaran Nan su zauna a wajenka zuwa Dan wani lokaci kafin na Shawo Kan Umma Dan wlh bana San tallan Nan duba kaga Zahira ta girma dan ma Bata da girman jiki Amma kana gani kasan ta fara Zama budurwa Taya Zan yarda a ringa Dora Mata talla Zahira da Nadeeya Umma tafi takura wa hakane yasa nace Bari na kawo su wajenka su zauna Ni Kuma yanzu idan na koma Zan nuna kamar bansan Inda suke ba kaga idan an kwana biyu sai nazo na daukesu Kamar angansu ne inaga hakane kawai zai saka Umma ta hakura da tallan da takeso suyi na k'arfi da yaji.

Naso Naeema data tashi guduwa ta tafi da ko iya zahiran ne Ni Kuma bana San bin Bayan ta sabida Naeema tayi.hakurin da Umma koni bazan soma bin bayanta nace ta dawo ba gwara ta huta idan an kwana biyu sai na Kai Mata yaran intaga zata rikesu shikenan idan taga bazata iya ba sai mu dawo

"Yaya ba sai ka hadani da Allah ba yaran Nan nima yayana ne Nan ma gidansu ne sauran ma idan kana ganin Umma zata takura musu ka kawo su wlh Zan rik'e su yanzu Ina cikin rufin asiri abinda zasu ci bazai gagareni ba insha Allahu Umma Kuma Allah ya shiryeta sai dai makarantarsu ne bansan ya zaayi ba tunda kace Zahira na primary 4 Kuma 3rd term

"Hakura zasuyi na Dan lokaci kafin komai ya warware zanje makarantar da kaina Tijjani Nagode sosai da taimakonka a gareni Zahira da Nadeeya kawai nakeso su zauna anan Dan su tafi matsawa gobe zan dauko musu kayansu a boye na kawo musu insha Allahu sai dai ka taimaka min Kar su zauna haka su ringa zuwa islamiyya Dan Naga kamar akwai makarantun islamiyya a layin naku

"Haba Yaya wlh bazan iya biyanka alherinka a gareni insha Allahu baka da matsala Kaya ka barshi Zan siya musu Koda gwanjo ne basai ka wahalar da kanka ba Zan Kuma saka su a islamiyya Ina samu kudi har bokon Zan iya saka su insha Allahu"

Dafatan matarka bazata damu ba Dan bana San na takura ta

"Haba Yaya wlh bazata damu ba ai Tama samu Yan tayin hira tana da san mutane sosai"

"Tabdijam"

Murja tace bayan ta Gama Jin duk abinda sukace

Ta nufi d'akinta a fusace

Naseer kuwa yayi ta yiwa Tijjani godiya

Ya mike akan zai tafi ya Kira Murja ya Mata sallama.

A daki ya tadda Murjan tana kad'a kafa ko lura da Fuskarta baiyi ba yace ta fito suyi Sallama yayansa zai tafi

Daga hakanya saki labulen yayi waje

Murjan ta bishi a baya tana kakalo faraa tana fitowa tayi kasa da Kai tana "Har zaku Tafi"
Chapter 8 · 0% Book details