← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 62

Sashe 40

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai yamin yace mafarki ne kawai Kar na damu kaina

Ban dai iya cire mafarkin a Raina ba a ranar

Wajen Sha daya bacci ya Kara kwasata na Kara irin mafarkin sak

Kai Wasa Wasa sai gani nayi mafarki ajere cikin kwana uku Ana kwana ukun naji mahaifiya ta na cewa yaran "Sadaka maganin masifa"

Kalmar Nan Haka na haddace shi a kaina har na tashi.

Abinda ban Gane ba ko mahaifiyata Kara tuna min take Dana dage da sadaka toh Naga Ina yin Sadakan Nan.

Haka mafarkiin ya tsayamin a raina na hau yiwa yara sadakan alewa ina rabawa Ina cewa kuyiwa Yata addua Allah ya bata lafiya take kuwa zasu hau tsalle tsalle suna yiwa Zahira addua cikin murnar alewar Dana Basu.

Ban kawo komai ba kwatsam Ina zaune yaddiko ta shigo duba Zahira Dan takan Dan duba ta akai akai.makociyar arzki ce itama bana manta ta a rayuwata

Muna cikin hirar sama sama kwatsam na tsinci kaina da Mata tambaya.

"Ni Kam akwai tsohowa a unguwar Nan Haka da kike tunanin tana bukatar taimako haka"?

"Kai akwai sosai ma ai suna da yawa.

Amma akwai wata matar Mallam Amina Nima zuwa nayi na tarar da ita a unguwar Nan a can kasa layi take mijinta shekara goma kenan da rasuwa Bata tab'a haihuwa ba har ta tsufa mace ce Mai addini da tsoron Allah Kamar yanda na samu labari

Rasuwar.mijinta yasa ta Dan siyar da gidan take juya kudin ta Kama haya toh shine wasu azzalluman Yan fashi suka dirar Mata suka.kwace komai a hannunta shine fa ta hau bara tana samun na abinci

Shekara biyu da suka wuce mota ta bige ta shine ta daina fita baran sabida ciwon kafa da take fama dashi

Ahaka Mai gidan hayan dayake Yana da Dan tausayi ya bar Mata daki daya a gidan

Wayanda Suka San halin da take ciki sukan Dan taimaka Mata ko Ni Ina samu sarari Ina Mata Aiken abinci"

Sosai naji hankalina yayi wajen matar da naji sunan Mahaifiyata gareta bandai nunawa yaddiko komai ba nace tamin kwatance Gidan tana min kuwa nagane.

A Haka muka Dan Kara tab'a Hira ta tafi

Washegari kuwa da sassafe na shirya abinci a kula.
Na dibi danyen abincinmu na dauko xannuwa na guda biyu duk da Nima banida suturra na hada da sabulu na nufi gidan matar kamar yanda aka kwantan tamin

Dana Isa gidan inata Sallama baa amsa ba hakane yasa na Shiga d'akin Dana gani a bud'e

A kwance na tarar da ita tayi Kashi ma a jikinta ga kafarta a kumbure kamar rashin kudi yasa Bata iya Kai kanta asibiti

Sosai naji tsigar jikina ya tashi

Na ajiye kayayakin hannuna na Isa wajenta Ina "Sannu mama"

Da Ido ta ringa Bina ban ce Mata komai ba na dagata na fita Waje tausayinta na balain rufeni dak'yar na samo ruwa na wanke Mata Jiknta batare da naji kyankyaminta ba na duba tsumokaran Kayanta Naga duk ta batasu da Kashi da fitsari

Hakane yasa na dauko zanina Dana Zo dasu na daura Mata daya sosai naji kamar itace matar da nake ganin Mahaifiyata na taimakawa akwai dalilin dayasa nake mafarki da mahaifiyata kila matar Nan ke bukatar taimako.

Yanda take kallona hawaye na zuraro Mata yasa na dauko Kular abincin Dana Zo dashi

Sai dai Ina Isa wajenta jiki na rawa ta fusge abinci rashin k'arfi yasa ta kasa bud'ewa Ni kuwa hawayen tausayinta ya zubomin na bud'e Mata jiki na rawa kuwa ta hau ci da Sauri da Sauri tuna Nima halin Dana tsinci kaina a ciki kwanakin baya na azabar yunwa yasa na hau kuka

Sai data ci na Bata ruwa.
Ta sha ta fashe da kuka tana "Baiwar Allah daga Ina ya akayi kikasan Ina bukatar taimako yanda Kika ciyar Dani Kika shayar dani rabbi ya faranta Miki ya biya miki bukatunki na alheri nafi sati rabona da abinci

Bana iya tashi idan Kashi ya matseni ko fitsari sai dai nayi daga kwance sabida ciwon kafa banida kowa sai Allah banida d'a banida jika bansan dadin haihuwa ba ballantana na samu Mai taimakamin

Ngd yarinya Allah ya faranta Miki"

Ameen mama Nima banida uwa banida uba dafatan Zaki zama mahaifyata

Kalmar Nan ne yasakata kuka ta hau shimin albarka Nima dadin kalmar albarkar da take sakamin ya sakani kuka

Tuni na tattaro zannuwanta data Bata na wanke Mata su na gyara daki dayan

Ina kallo ta daga hannunta tana Godewa Allah daga adduoin da take nasan macece Mai ILimi da baiwa sai dai jarrabata da Allah ya mata hakane kuwa yasa na Sha alwashin faranta Mata har tsawon rayuwtaa

Sai uku na koma gida Naseer Bai tambayeni Ina naje ba

Nadeeya na Gama girkin dare na Kara zubawa a kula na saka hijabina na cewa Minal tazo mujr taga gidan

A takaice tunda ga ranar na dauke Mata cin safe Rana dare

Nakanje wajenta muyi hira sosai nake jinta Kamar mahaifyata

Ko ban samu zuwa ba nakan sa yarana suje gidanta su Dan Mata gyare gyare su dawo.kuma.wani ikon Allah ban Kara mafarki da mahaifiyata ba

Sabon da nayi da Inna Amina yasa na fara sakin jiki da ita Ina Bata labarin kaina har na Zahira da halin da take ciki

Sosai hankalinta ya tashi tace na kawo Mata Zahira ta gani

Washegari da yamma na goya zahira mukaje

Sosai ta kad'u da ganin zahiran

Tacemin zata taimakamin insha Allahu akan Zahira Allah ya Bata wnan ilimin ita da margayi mijinta

Ko.kadan maganarta Bata shigeni ba lura da macece ita Kuma.manyan mallamai sun Yi iya k'ok'arinsu Basu iya warkar da Zahira ba

Abubuwa ta lissafamun akan na siyo Mata har da su ruwan zam zam Jan miski ganyen magarya

Wasu Abubuwan dai na manta su na dai siyo Mata ne kawai ba Dan na yarda ba

A Haka tace na ringa kawo Mata zahiran tana Mata Addu'oi.

Banki tata ba Dan bansan baiwar da Allah ya Mata ba na Kuma ga tabbas tana da ilimin

Dakaina nayiwa zahira alwala itama da alwala a jikinta sai ta sa na samo kasko ta zuba wani turare data hada

A.farkon ranar da tayiwa Zahira turaren

A ranar Naga tashin hankali Dan sosai Zahira ta ringa ihu tana murya kala.kala tana rantsuwar kashe Inna Amina yarika sai datayi yafi kala ashirin yanda take k'ok'awa da Inna Amina sabida tana watsa Mata ruwan zam zam data kwana tana addua akai yasa.na baxama na Nemo maza

Suka ririketa Amma a banza Haka ta watsar dasu

Sosai muryarta ya dawo na maza na tsorota danaga yanda Inna Amina ta bada himma wajen turaren.

A takaice sai gashi Aljannun da aka turawa Zahira suna magana wajen su bakwai a jikinta maza da mace daya Kuma arnaye yanda Inna Amina ke konasu da ayoyin Allah ta daure manyan yatsunta guda biyu yasa Suka hau cewa zasu fita Kar ta konasu aikosu akayi

Take Inna Amina tace waye ya aikosu sukace Shugabansu ne ya aikosu tace waye suka Kira sunansa

Inna Amina kuwa ta cigaba da gana musu azaba suna zuba yarika

Haka muka kwashi kwana bakwai Inna Amina na fama da Zahira ko bacci bama Yi Dan gidanta muka koma gabadaya tunda muke zuwa wajen masu rukkiya ban taba ganin wanda ya haukata Zahira Haka ba sai Inna Amina

A kwana na takwas zahira ta hau amaye amaye har da gashi Haka ta ringa amayo shi

Inna Amina kuwa ta cigaba da zabga turare data hada sai gashi zahira na muryoyi kala kala Akan zata fita a yau su koma wajen wayanda Suka turo su

Inna Amina dak'yar ta tsagaita tace sunyi alkawarin fita suka ce ee tace ta Ina zasu fita suka ce ta Baki a take kuwa Naga Zahira ta hau atishawa ba kakautawa.

Can ta saki Kara Naga idonta nata fitowa waje daya saka hankalinmu tashi gabadaya Inna Amina kuwa tayi saurin cewa karka fita ta idonta Zan Kona ka sai dai ina aikin Gama ya Gama sai da daya ya fita ta idon Zahiran da har yau idan ka Kura Mata Ido zaka ga idonta daya ya Dan fi daya girma

Kamar a mafarki Zahira ta zube a kasa.

Hallitar jikinta ya hau canjawa idonta na komawa ciki Jikinta na cikowa

*Alhamdulillah sadaka maganin Masifa wlh Tallahi akwai sirri a sadaka da ba kowa ne zai Gane ba ba sai kin Zama Mai kudi zaki iya sadaka ba akwai mabukata kana cikin matsala tsanananta da Addu'a da sadaka duk biye biyen da sukayi a sanadin farantawa baiwar Allah Nan Rai sun samu maganin matsalarmu Allah yasa mudace*

*Comment*

Wlh exactly irin abinda ya faru dani nikuma kishiyar mamanah ce tafara ne akan mamanah Allah bai bata sa,a ba sai tadawo kaina saboda mamanah tafiji dani duk cikin diyanta shine tayi amfani dani don ta kuntatawa mamanah wlh yadda idon zahira suke da bantsoro haka nau suke inka kalleni so daya baka marmarin kasake kallona wlh har kuka akeyimin ina sati kwance babu babusha kuma da anje dani asibi duk bincikenda za,ayi sai ace lpy ta lau banida matsalar komai duk inda mukaje bidar magani aikin banza munyi na asibiti ba,a gane komai ba aka komo na hausa shima shiru haka za,a kiro malamai suyita yimin rukiya amma basu magana wlh wani wuri da aka kaini hadda turaren barkono akayimin amma suka ki magana na wahala na wahala nasha azaba sosai wlh haka mamana zata sakani gaba tayita yimin kuka wlh gurin da muka fara zuwa da aka gayamana kishiyar mamanah ce bamu yarda ba sai da mukaje wuri yafi uku anagayama itace kafin muyarda itace tayimin ije da bakin aljanu guda uku wai su haukatani kuma su hanani aure da kyet da taimakon Allah akasamu naji dama nadaina rashin lpy amma duk da haka wlh basu rabu dani gaba dayaba don sunki barina inyi aure inaji Ina gani aure ya gagareni munyi magani munkashi kudi har karfinmu yakare amma wlh haryanxu shiru yanxu shekarata goma kenan cikin wannan matsala wlh matsalar sihiri babbar matsala ce.
Chapter 40 · 0% Book details