← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 62

Sashe 23

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen karfe shidda na asuba baccin wahala yaso ya d'auketa.

Har ta fara baccin sama sama taji an banko k'ofar dakinta da balain k'arfi.

Mik'ewa tayi a firgice Dan ta balain tsorata.

Hafsa ce ta shigo cikin kayan bacci har kasa kanta a bud'e Yana ta digar ruwa.

Cikin wani irin murmushi hafsa tace "Amarya dafatan kin tashi lafiya baccin ya Isa Haka a fito a Dora Mana abincin karyawa Dan Yara zasu tafi makaranta Dan nasan kinsan Yana da Yara masu zuwa makaranta dole zasuci abinci kafin su tafi makaranta".

Wani irin Mugun kallon tsana Safiiya ta kwashe Hafsa da shi tana "Juya ki barmin daki kafin na tureki da kaina uwar abincin Zan dafawa Yara ba abinci ba ke da kwana da miji Ni da dafawa Yara abinci kin dauka Yar aiki aka kawo Miki wlh bashi kikaci duk abinda Kika min sai na Rama bakisan waccece ni bane kina Wasa da wuta Bari na kamaki"

Wani irin Dariya Hafsa ta kwashe dashi tana "Zaki sha wahala idan kikace zaki ja Dani a yau Zan tabbatar.miki da ke Yar aikin ce tunda har.kika auri mijina idan Kika min gardama Kuma wlh na Miki shegen duka da kafarki Zaki bar gidanan"

Ta juya ta fita daga d'akin Safiyya kuwa ta buga uban Tsaki Tana Shan alwashin gari na wayewa zata tafi wajen shugubarsu Kuma indai taje sai ta saka an kashe Mata hafsa.

Fitar Hafsa da Yan mintina sai Gata ta dawo da Umar daya balain had'e Rai ya saka doguwar rigar maza

Safiyya kuwa Ido ta zuba Masa tana mamakin yanda yake mata wulakanci Agaban kishiyar ta duk da tasan idan ta saka kwalli Yana rikicewa akanta Amma wani zubin Bata saka kwalin idan yazo Kuma Baya canja Mata haka.

Fuska a had'e yace "Ki tashi ki Dora wa Yara abin karyawa Dan zasu tafi makaranta sai kinyi kwana bakwai Zaki ajiye girki kafin hafsa ta karba"

"Idan ni kuke jira na Dora muku muku abinda zakuci wlh sai dai ku mutu da yunwa yaushe kuka tab'a Jin daga auro amarya ta fita ta Dora girki.naga ma ba a d'akina ka kwana ba akan me.zan Dora girki wlh Umar ka bani mamaki ban taba sanin Haka. Kake ba wlh Allah ban taba sanin wulakanta ni kakeso kayi ba shiyasa ka auroni agabanka wanan shegiyar matar taka Mai zubin maza ta Dokeni"

Jinta ne ya d'auke na wucin gadi Sakamakon Marin da Umar din ya d'auke ta dashi Yana "daga yau karki sake ki Kara zagarmin Mata idan kina San zaman lafiya a gidanan ki tashi ki dorawa yarana abinci karyawa karsu makara zuwa makaranta"

Umar yace a fusace Yana barin d'akin Hafsa kuwa cikin wani irin murmushi ta karasa gaban Safiyya dake dafe da kumatunta har lokacin sabida tsananin mamaki Marin da Umar ya Mata tace "Baki ga komai ba wlh da kafarki Zaki bar gidanan Dan mijina yafi karfinki na Gaya miki ba yanda zaayi sama ta kizo ki aure min miji alhalin bakisan wuyan Dana Sha dashi ba"

Daga haka ta fice daga d'akin

Safiyya ta zub'e kasa ta fashe da kukan bakinciki.

A takaice a cikin kwana bakwai da Kai Safiyya tayi wani irin Rama tayi wurjan wurjan Dan duk Inda take tunanin Hafsa ta wuce Nan Dan muguwa ce ta karshe horar yunwa da take Mata yasa ta yarda ta fara girkin duk Yan gidan Sabida ta samu na abinci

Nan ma idan ta girka Hafsa ke zuwa ta juye a babban kula ta bar Mata kanzo ta kankara Dan kudin Hajara data kwaso ma yaranta sun bita har d'akinta sun kwashe ballantana ta siyawa kanta abinci

Duk yanda taso fita Umar ya hanata Dan mugunta ma Safiyya kulle gidan take idan ta saka ta aiki tak'i sai ta jibgeta.

Yaranta ma a palonta sukacin abinci su Mata kaca kaca da Palo da daki Bata Isa tayi Magana ba da mugunta ma yaran Suka fafarka kujerunta da Reza da Zuciya ya d'ebbeta hade Yaran tayi ta zanesu dayake sabida bakin cikin ganin tsadaddun kujerunta da suka yaga

Sai dai yaran na fita sai ga Hafsa Nan daga k'ok'awa ta Mata shegen duka ta kumbura Mata fuska tundaga ranar Bata Kara gigin tab'a yaran ba
Tana ji tana gani yaran Hafsa ke wulakanta Mata Kaya
Bata isa tayi magana ba kuka take ci sosai tana nadamar ma auren Umar din dan gwara Zamanta ba auren da irin wanan kuntacecen rayuwar da take sati daya da kwanakin da ta tafi ji take kamar tayi shekaru a kurkuku ta Sha yunk'urin guduwa daddare Hafsa datake cewa Mayya na dawo da ita Dan Hafsa so take sai ta azababtar da ita kafin tasa Umar ya saketa.

Dan ba karamin kamu tayiwa Umar ba,Bai Isa ya ketare umarninta ba

A yau ma Kamar yanda Hafsa take tilasta Mata aikin gidan.

Ta fito Ana iddar da sallah asuba ta fara aikin gidan.

Da gayya ma yaran da suka jiku da makirci ke B'ata katon gidan ta share ta goge ta zo ta Dora babban tukunya ta Dora musu abinci

Ita kuwa hafsa Haka zata fito da jikakken Kai tana Mata murmushin mugunta Dan Umar sau uku kenan Yana kwasheta da Mari idan ta Bijirewa umarnin Hafsa zuwa yanzu ba abinda ta tsana sama da zaman gidan auren dan tayi auren ne Dan taji dadi sai gashi tana Shan wuyan da ko a mafarki Bata tab'a hasasowa.kanta ba muryar Hafsa kawai fadar.mata da gaba yake

Ahaka ta Gama abincin Hafsa ta juye ta bar Mata kanzo ta kankara taci ta Kara wanke wanken
Yaran Suka
fita gabadaya har da Hafsa.

Sosai Safiyya taji dadin fitarta ta Shiga d'aki da Sauri ta d'auko mayafinta ta fita itama.

Duk da nisan dajin da suke zuwa wajen shugabarsu ahaka ta Nadi tafiya Mai nisa tana Isa bukkar ta hau yaren tsafin su sai dai har ta Gama babu shugubarsu babu dalilinta.

Kamar tayi kuka ahaka ta fito daga dajin ta koma gida tana Shan alwashin kwashe Kayanta ta tafi Dan bazata iya cigaba da zaman bauta ba.

Sai dai tana dawowa ta tarar Da Umar a d'akinta.

Ya wani marairace ya hau Bata hakurin Bai San Mai ya hau kansa ba a takaice a ranar ya kwanta da Safiyya Yana samun nutsuwa ya sauka daga kanta ya rufeta da dukan ita ba budurwa bace Yar iska ce ita a ranar Umar ne ya karbi ragamar mugunta yayi ta azabtar da ita da aiki.yana zaginta akan ita Yar iska ce .

A irin wanna yanayin da Safiyya ke fuskantar.azabar wahala daga wajen Umar da Hafsa da yamma Safiyya na jidar wankin da Hafsa ta loda Mata bayan ta gama wawanka Mata Mari Hajara kuwa suna isa Calaba ta d'au hanyar gidan Umar da yake sananne da lodin Kayanta data Dora aka.

Ko Sallama batayi ba ta Shiga katon gidan da tun a waje ta fara dan Jin sanyi samun wajen da zata zauna Mai kyau Dan ko Mai zaayi sai dai a ayi wlh Zamanta zatayi a gidan tunda Safiyya ce silar siyar da gidan da take zaune cikin rufin asiri.

Kamar a mafarki Safiyya taji muryar Hajara tana dagowa kuwa taga itace

Aguje tayi wurgi da bokitin hannunta taje da zumar kankame hajara Dan gani take kamar zuwanta ne zai saka ta bar gidan

Hajara.kuwa sakin kayanta tayi a kasa ta matsa tana isowa wajenta ta kwashe Safiyya da wani mahaukacin Mari tana "har ni Zaki yaudara Ina uwarki Safiyya har Ni Dana Haifeki Zaki cuta ki hainceni kisa na siyar da gidan Naseer Dan na Miki kayan daki iya nan Bai isheki ba sai da Kika kwashe kudin da Kika bani dan na siyi karamin gida

Toh wlh Tallahi sai kin fito mun da kudin gidan ko Kuma na zauna a gidanan tunda banida gidan da Zan zauna"

"Safiyya hannunta ta fara k'ok'arin ja Dan ta kaita daki sabida Hafsa dake zaune a Kan tabarma data zubo musu Ido sam.bata san tasan abinda ke faruwa.

Hajara cigaba da bambamin masifa tayi tana kwashewa Saffiya albarka dake ta Jan hannunta

Hafsa kuwa ta mik'e tana dakawa Hafsa tsawa tana "Wacce wanan Zaki shigo.mana da.ita gida"?

Hajara wani mugun kallo ta Mata ta kalli Safiyya tana "Halan wanan Mai zubin mazan ce kishiyarki"?

"Nice Mai zubin mazan?

Hafsa tace cikin mamakin Hajara .

Hajara kuwa ta ja Tsaki ta fara k'ok'arin Shiga b'angaren Safiyya.

Hafsa kuwa ta jawota ta kifa mata Marin da sai da Hajara taga walkiya a takaice har waje Hafsa ta fitar da Hajaran ta Kuma rantse bazata kwana a gidan ba.

Hajara haka ta kwashi Kayanta ta nufi gidan Lami tana Shan mugayen alwashi akan kishiyar Safiyya Dan ta Gane Safiyya Bora ce a gidan.

Sai dai shima gidan lamin data Isa kwana uku ta iya yi Sabida abinci sau daya ake dorawa a gidan Sabida talaucin da suke fama dashi.

Gashi shi kansa mijin Lami wani gani gani yake wa Hajaran hakane yasa ta Kara tattara Kayanta da kudin mota ta nufi Tasha ta hau motar Kano Inda ta yanke Zama a gidan Tijjani tunda Bata da Inda zata zauna har.daji ta nausa Dan shugabarsu ta gano Mata Inda Naseer. Yake ta kuma.kara rokarta mudubin tsafi Dana karfinsu har ta karaci yaren tsafin dake sa ta bayyana a gabansu Bata bayyana ba.

A mugun gajiye ta isa gidan Tijjanin Inda taci Karo dashi a bakin kofa zai fita massallaci turus yayi daya ganta da Niki Nikin Kaya Hajara kuwa ta sauke kayan daga Kanta tana "Bani hanya na wuce ka tsaya kana kallona kamar baka sani ba ka shigo min da kayan Nan maza"

Tace tana matsar da Tijjanin tare da shigewa cikin gidan tana Kara hade Rai Dan so take ta gwada karfin uwa akan Tijjani ya mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata duk da kasan zuciyata tana Dan Jin shakkar Murjan

A.palo ta tarar da Murja da jaririyar ta a hannu da Bata fi kwana biyu da haifarta ba.

Kallon kallo suka yiwa Juna a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da bacconta Yana "Umma Wai daga ina kike naganki da Niki Nikin kaya"?
Chapter 23 · 0% Book details