Sashe 14
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikinta ne ya dau rawa cikin tsoro ta zub'e a kasa tare da fashewa da kuka
Ni kuwa nace "Ke jahilar inace da Zaki biyo yara har gidan ubansu a gaban iyayensu Kuma ki nemi dukansu Mai suka Miki"?
Nace wa wacce ta biyo su zahiran da bansan dalilin dayasa ta biyosu ba banma San daga Ina suke ba
"Murja lafiya kuwa"?
Shine abinda naji Naseer yace Mata ita kuwa sai rizgar kuka take"
Tana k'ok'arin magana naji muryar Nadeeya data rungume kafafun Naseer ta Baya ta lek'o da fuskata tana "Allah ya isa tsakaninmu dake muguwa Azzalluma sai Allah ya saka Mana bazamu tab'a yafe Miki ba
Abba muguwa ce kullum sai ta dake mu ta d'auko wuka Wai sai ta kashemu Bata bamu abinci sai dai Wake da sabulu"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Nadeeya Mai na Miki da zakimin wanan Sharrin Yaya Naseer wlh karya take min tunda ka Kai su kullum sai sunyi kuka Akan suna San su dawo kullum sai na rarrashe su shine yau daga Shiga wanka na fito mak'ota sukace min gasu can sun gudu shine fa na biyosu har Nan Dan bana San wani Abu ya samesu Amma wlh ban musu komai ba"
"Wlh Abba karya take yi kaga shattin tsintsiyar kwakwan data dakemu dashi kaga Gefen fuskar aunty Zahira wlh muguwa ce yanzu ma sai data dakemu Wani Mai shago ya bamu kudi Akan mu gudu kafin ta kashemu"
Murja na k'ok'arin Magana
Hajara da tunda ta ga Murja ta daskare a tsaye
Ganin irin sharrin data kula musu Kafin su har gidan Tijjani irinsa take kulawan yanzu yasa ta daka wani uban tsalle ta tsaya Agaban Murja tana "Karya kike wlh shegiya munafika kafira makira Yar wuta duk abinda yarinya Nan tace wlh Zaki aikata tsaf Yau kinzo har inda nake kin sameni kin rabani da Dana kin sa ya koreni hakan Bai isheki ba sai kin taba jikokina toh wlh yau sai na Rama abinda kikamin"
Hajara tace tana cakumo rigar Murjan tare da ware murya ta hau kwallawa Safiyya dake daki tana bacci batare da tasan duk abinda ke faruwa ba yanda ta ware murya ne yasa Safiyya ta jiyota ta kuwa fito a guje.
Murja kuwa irin cakume mata Riga da tayi yasa ta mik'e tana "Umma Mai na Miki Dan Allah Mai na Miki kika tsaneni"
"Allah ya tsinewa bakinki albarka da kike KIRANA Umma dashi Ni da kika zaneni wanan Bai isheki ba Kika hada da makirci sai da muka bar gidan nida gidan Dana k'arfi da yaji Kika hanani abinci dayake bakida ta Ido ni Zaki kalla kicewa Umma Allah ya tsine Miki Murja Nan ma makircin zakimin kenan duk da babu idon Tijjani?
"Murja sosai.ta ringa Kai zuciyarta nesa Dan ji take kamar ta daga Hajaran ta maka da kasa Amma Bata San ta kwafsa sabida Naseer da ya saki baki Yana kallonsu
Hawaye ta hau yi cikin shesheka tana "Haba Umma kiyayar da kikemin har ya Kai Haka da Zaki min sharri"
Ke Amma bakida kunya Yanzu anan ma makircin Zaki mana"
Safiyya tace tana nada hannun rigarta
"Haba Umma"
Wani irin Mari Hajara ta d'auke Murja dashi sabida bakin cikin yanda Murja ke neman nunawa ita ta Allah ce
Murja kuwa ta dafe kumatunta tana Jin zuciyarta na zuwa wuya tana k'ok'arin Kara magana ta Kara kwashe Murja da.mari
Murja kuwa zafin Marin Yasa ta manta da wani Naseer da ke tsaye ta daga Hajara sama duk da uban cikin jikinta ta makata da kasa
Safiyya tayi Kan Murja ta hau Kai Mata duka
Naseer kuwa dake sallati
Ya nufi.kansu aguje Yana ihun Kar a tab'a Murja ciki ne da ita adaidai lokacin da Hajara ta samu ta mayar da.murja kasa ta d'ebo kasa.ta cusa a bakin Murja
Naseer kuwa ya wancakalar da safeeya ya ruk'o Hajara da k'arfi da itama kamar karfin aka Kara Mata sai ma k'ok'arin tak'e cikin Murja dake kawo Mata duka itama take.
"Cikani munafiki Ashe Dama gidan Tijjani ka Kai yaran Nan shine kacemin sun b'ata ka dagamin hankali Naseer Ni zaka yaudara Naseer Akan na Mori yaranka mu samu na rufin asiri gabadaya ka gwammace ka Kai su gidan azzalluma Nan makira har kazo kamin karyar sun B'ata Naseer Dan kawai Kar na Dora musu talla?
Tallan Dana Dora musu Dan wa na Dora musu Naseer ba Dan mu samu abinda yaran naka Zasu ringa ci bane tunda ka kasa Nemo Mana kudin kirki tunda shegiya matar Nan taka itama.ta bar gidanan ta asirceka komai naka ya tsaya cak daga Kai har Tijjani kun auro shegu tsinannu"
"Wlh Ni ba shegiya bace Umma kuma danki da kike magana ai na bar.miki shi tunda bana gidansa yanzu Yara Kuma da kike magana wlh a yau Zan kwashe su na tafi dasu Dan bazan Kara barinsu a gidanan ba Ni Zan iya kula dasu ke D'an naki ya kula dake kedai Umma ki nemo masa wacce ta kwanta Miki ki aura Masa"
Nace Ina rik'e da hannun Zahira Dana Nadeeya daga abinda ya faru.nagane Murja ce matar Tijjani tunda Naseer ya rik'e Umma.ta kwashi takalmanta tare da furzar da kasar da Umma ta cika Mata bakinta dashi.
Da sauri.ta hau tafiya tana rufe fuskarta da mayafi Safiyya kuwa har da diban dutse ta jefa Mata
"Karki sake Kimin rashin kunya in Banda kaddara Mai Naseer zaiyi dake Yara Kuma da kike magana ba Inda Zaki tafi dasu ko kwaki ya samo ya Basu suci so kike ki tafi da yaran sabida ya biyoki ko toh na Gane wayonki ba Inda zakije da yaran"?
"Wlh sai na tafi dasu Umma Banga uban da zai Hana ni tafiya dasu ba"
Nace Rai a bace tare da rike hannayen yarana nayi gefe dasu Nadeeya kuwa Naga ta Dan tirje
Naseer da idonsa ya kad'a yayi wani irin ja dak'yar ya bud'e bakinsa yana "ki tafi dasu Naeema Allah ya musu albarka"
Ameen nayi saurin cewa na fara k'ok'arin juyawa hannuna rik'e Dana yarana Zahira kuwa har tayi gaba.
Aunty ita Kuma tana rik'e da hannunsu Raheema.
Umma kuwa tace "Kace ta tafi dasu kana da hankali kuwa"?
Naseer Bai ce Mata komai ba
Illa ma hannunsa da ya mikomin Yana "Dan Allah Dan bani Waleed Naganshi Naeema"
Ban ma saurareshi ba duk da tausayinsa na nukurkusar zuciya ta
Aunty kuwa ganin na ma share shi na dau hanya zan tafi yasa ta saki hannunsu Raheema ta karaso wajena ta kunto Waleed Ni kuwa nace Mata "Kar fa ya hanani Dana"
Bata saurareni ba ta mik'awa Naseer Waleed
Waleed kuwa ya karbe shi da hannu biyu ya rungumeshi a kirjinsa adaidai lokacin da hawaye suka zubo Masa yayi saurin d'auke hawayen ya sumbaci Waleed a goshi Yana "Allah ya maka albarka Naseer"
Daga Haka ya mik'awa Aunty shi
Ya kalli Zahira da har sunyi gaba Yana "Ba Sallama Zahira Raheema.humaira bazaku zo kumin Sallama ba"
Da Sauri duk.suka nufi wajensa ya sunkuya ya rungumesu ya shafa kansu gabadaya har da Nadeeya dake gefensa yace "Maza kubi ummanku ku tafi kunji Allah ya muku albarka kuringa yiwa Abbanku addua Allah ya bashi kudi kunji"?
"Abba bada Kai zamu tafi ba"?
Nadeeya tace hawaye na cika Mata Ido adaidai lokacin da su Zahira suka.dan Kara yin gaba Dan suna tsoron Naeema ta tafi ta barsu
Murmushin karfin hali Naseer yayi Yana "badani zaku Tafi ba Nadeeya Amma zanzo kinji maza Kibi Yan uwanki ki tafi"
Hawaye ta hau Yi Tak'i motsawa
Ni kuwa na daka Mata tsawa Ina "Dan ubanki kizo ki wuce mu tafi"
Umma kuwa sai zagin Naseer take tana zagina Akan na asirice Naseer yace na tafi da yaran
Ga mamakina Nadeeya girgiza min Kai tayi tana "Umma idan bazamu tafi da Abba ba a wajen Abba Zan zauna bazan biku ba"
Ta karashe cikin kuka.tana kankame Naseer
Ni kuwa na Kara daka Mata tsawa Ina "kizo ki wuce mu tafi Nadeeya wlh Zan zaneki Dan idan Kika zauna a Nan duka Zaki ringa sha a Dora Miki talla ko makaranta ma bazaki je ba"
"Nidai ba Inda zani wajen Abba Zan zauna umma"
Naseer kuwa banbare ta yayi daga jikinsa cikin murmushi da kana gani kasan na yak'e ne ya sunkuya ya rik'e hannun Nadeeya Yana "Karki damu Nadeeya ta zanzo na sameku Kibi ummanki ki tafi kinji idan Kika zauna anan ba Wanda zakiyi Wasa dashi"
"Nidai ba Inda zani Abba indai bazaka bimu ba a wajenka Zan zauna"
A zuciye na nufi wajen Naseer da niyyar na fincikota ita kuwa ta dib'a aguje ta Shiga gidan tana hankada Umma dake bakin kofa........
Toh ga readmore biyu Nan tunda kun matsamin😝😝😝😝😝😝😝😝
[7/5, 10:40 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 41*
Har ciki na bita Nima Ina dan bangaje Umma datayi bake bake a bakin kofa ita kuwa tayi ta auna min zagi Wai na fito Mata daga gidan d'a Kar na Musu Sata.
Ban saurareta ba na bi Nadeeya har d'akina na da Dan Nan ta shige
Tana ganina ta kankame jikinta tana ihun kukan "Ba Inda zani Umma bazan biki ba a wajen Abba Zan zauna Umma idan Kika tafi damu waye zai zauna da Abba ba Inda zanje Umma"
Haushin taurin Kan Nadeeya yasa na Kai Mata duka na rik'e hannunta da Karfi da nufin janta a kasa sosai Kuma nake mamakin Inda Nadeeya ta samo taurin Kai
bazata Gane Gata nake Mata da rabata da gidanan ba daga Ni har sauran yaran nawa ai ba a San ranmu muka bar Abban nata ba Dan muma ba finmu San shi tayi ba
Kara fincike hannunta tayi da k'arfi ta hau burgiman ba Inda zataje Ni kuwa na cire takalmina da niyyar zaneta.
Naseer ya shigo da Sauri ya rik'e hannuna Yana "kiyi hakuri karki bugeta Bari na rarrasheta"
Ya saki hannuna ya durk'usa gaban Nadeeya tare da dagota ya hau rarrashinta Akan ta bini ita kuwa sai tirjewa take Akan bazata bini ba ita a wajensa zata zauna a karshe ma sai ta fita aguje