Sashe 22
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Naseer da yazo har wuya a tsawace yace "Umma ki kasheni Dan Allah Dan annabi ki Huta Umma bayan abinda kikamin har Zaki iya cewa na nema Mana wajen da zamu zauna umma Nagaji Nima.yanzu ta kaina zanyi tunda kinyi nassarar rabani da komai Abu daya Zan Miki shine na baki kudin mota kije calaba wajen Safiyyan data Baki shawarar ki siyar da gidana ta San yanda zatayi dake bani kadai ne danki ba Umma idan bakya San zuwa calaba kije gidan Tijjani yanda Kika haifeshi Haka Kika haifeni Umma bazan kashe kaina akanki ba Umma na rasa Mai na Miki a rayuwata Umma kin kassaramin rayuwa yanzu banida komai a rayuwata sai wanan Kayan sawan nawa Umma Dan Haka nima Zan Shiga duniya naje na nemi kudi tunda yarana ma da matata duk kin rabani dasu"
Kuka Hajara ta fashe dashi ta zub'e a kasa tana ta Shiga uku taya zataje gidan Tijjani da matarsa ke dukanta take Mata horar yunwa Taya zataje gidan Safiyya da ko sati biyu batayi da aure ba"
Naseer kuwa kudin hannunsa ya raba gida biyu ya Ajiye Mata agabanta ya kinkimi bakonsa ya tafi ya barta tana ihun Kiran ya dawo Kar ya tona Mata asiri.
Yana kuwa fita yasamu taxi daya zo ya sauke Kaya a wani shagon provision
Ya tsayar dashi ya saka bakkonsa biyu a ciki ya Gaya masa Inda zai kaishi.
Yana kallon Hajara ta fito daga gidan hankalinta a tashe har Dan biyo taxin tayi shi kuwa ya d'auke kansa Dan ya gaji da halin mahaifiyarsa zata Dade Bata Kara ganinsa ba
Baa sauke shi a koina ba sai a gidan Naeema.
Ina zaune da Yara na a tsakar gida suna home work dinsu Ni kuma gabadaya hankalina na wajen tunanin Inda Naseer yayi daya kwana biyu Bai zo ba sosai na damu da rashin zuwansa Dan tunda yasan Inda nake Bai taba fashin zuwa ba hakane yasa na damu da Jinsa shiru Dan Ni nasan da lafiya yake ba yanda zaayi ya k'i lek'omu yanzu Haka ina tunanin idan gobe Bai zo ba Zan tura Isihu unguwar ya gano min ko zai ganshi Naga ya shigo gidan da bakko manya guda biyu a hannunsa ya ajiye.
Daga yanda Naganshi sai da gabana ya tsinke sabida yanda ya rame ya fice daga hayyacinsa kamar bashi ba.
Hankalina a tashe na mik'e Ina kallonsa ko kallon su Zahira dake Masa sannu da zuwa baiyi ba ya cire Raheema data je Masa oyoyo daga jikinsa ya shige dakina.
Ni kuwa na bishi da Sauri Dan ban taba ganinsa ahaka ba.
A Gefen gado na sameshi ya zauna ya sunkuyar da kansa
Ni kuwa na zauna a gefensa tare da ruk'o hannayensa Ina tambayarsa lafiya Mai ke damunsa.
Bai d'ago ba sai sheshek'an kukansa naji daya tayarmun da hankali yasani jawo shi jikina
Shi kuwa ya Dora kansa akan kafadata ya cigaba da kuka kasa kasa.
Ba karamin Abu ke saka Naseer kuka ba hakane yasa hankalina a tashe nima na hau kukan Ina tambayarsa abinda ya saka shi kukan.
Sai daya yi kukan Mai isarsa da har sai dayaji nauyin da kirjinsa ya Masa dake barazanar dauke Masa numfashi ya ragu kafin ya hau bani labarin duk abinda ya Faru.
Bansan lokacin Dana Zamo daga Kan gadon na zauna a kasa na hau sallati ba Dan ban tab'a tunanin Rashin Imanin su Umma har ya Kai Haka ba tayaya zasu siyar da gidan Naseer Dan kawai ayiwa Safiyya kayan daki Ni kaina na kashe kudi a gidanan sosai kafin yayi kyau
Tambayarsa nayi nawa Suka siyar da gidan yacemin shi Bai tsaya tambaya bama Dan da alama safiyya kadai ce taci kudin
Bansan lokacin Dana hau musu Allah ya Isa ba Dan ba iya Naseer Suka cuta ba har nida yarana sun cucemu.
Daga Ni har Naseer bamu iya wani bacci ba Dan sosai siyar da gidan ya min ciwo har hango gidan nake a idona.
Ganin damuwar da nayi na Kara saka Naseer cikin wani damuwar Dan ko abincin Dana zuba Masa Bai iya ci ba yasa na daure na hau bashi baki dak'yar ya ci abinci ya Sha magani bacci yayi awon gaba dashi.
Ni kuwa sanin bacci bazai d'aukeni ba yasa na rayya Daren Ina rokon Allah ya kawowa Naseer mafita ya musanya Masa da abinda yafi alheri.
Hajara kuwa ita kadai ta kwana ko bacci Bai ga idonta ba sosai hankalinta ya rabu gida biyu tana tunanin Inda ya Kamata ta dosa.
Sosai Naseer ya Bata mamaki da har ya iya tafiya ya barta Amma duk abinan Safiyya ce ta jaza Mata
Bata Isa ta soma dosan gidan Tijjani ba Dan Murja Yar iska ce shi kansa Tijjani bashida mutunci da Yana Mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata biyayya da zata samu saukin wani abun babu ma yanda zatayi ta soma dosan gidan Murja da take ganin tafi kowa mugunta ga makirci ga horo da yunwa idan ta gayawa Tijjani ma ba yace ta dameshi.
Tsinaniyar Safiyya data saka ta siyar da Naseer gidan Safiyya zata je a goben tasan yanda zatayi da ita.
Washegari kuwa da sassafe Mai gidan ya duro ko kallon hajara dake kwance a kasa ta shimfida zaninta baiyi ba aka hau buge buge a d'akin
Tana ji tana gani Yan aikin Suka Mata watsi da.kayanta waje ita kuwa ta fita waje tana matsa kwalla ta had'a Kayanta ta nufi Tasha Bata Sha wahalar samun motar calaba ba suka dau hanya tana cin alwashin irin bugun da zatayiwa Safiyya idan ta Isa gidanta.
Safiyya
Sosai taji dadin ganin bangarenta fes da kayan data siya da suka kasance tsadaddu.
Agajiye suka Isa calaba da Kuma bak'ar yunwa hakane yasa wayanda Suka rakata da suka kasance Yan calaba suna kaita Suka tafi.
Sai data Gama Shiga koina a gidan sanan ta fito palo ta zauna tana Allah Allah Umar ya shigo tace Masa tana Jin yunwa sai dai har akayi sallah Isha Bata ga keyarsa ba.
Sai muryar Yara ke tashi a tsakar gidan tana ta daga wuya taga ko zata ga uwargidanta data matsu taganta itama sai dai Bata ga alamarta ba.
Ahaka yunwa keta nukurkusarta
Ta rik'e cikinta wajen karfe Tara taji muryar Umar take Taji wani irin Sanyi a zuciyarta ta mik'e da sauri tayi waje.
Sai dai me tana fita taga Umar din a tsaye da manyan ledoji ya mik'awa wata datake kyautata zaton itace kishiyarta taci kwalliya cikin doguwar riga.
Ta yiwa umar din magana taga Umar din ya shige b'angaren ta batare da ya ma kalli bangarenta ba
Mamakine ya kasheta data ga uwargidanta ta nufo b'angarenta da ledojin a hannunta
Ita kuwa Safiyya ta gyara tsayuwarta tana jiran isowarta Dan daidai take da ita
Tana kuwa zuwa ta hau bin Safiyya da wani irin Mugun kallo tana "Ke a lailai Baki yarda ke amaryar bace koh duk mazan duniya Nan ki rasa wa Zaki aura sai mijina ko hmmm lailai yaro bai San wuta ba sai ya taka wlh Tallahi da kafafunki Zaki bar gidanan Dan Miji a tafin hannuna yake tsakaninki dashi sai gani sai hange.
Na Bari ya auroki ne Dan na samu Yar tayin aiki Dan Haka a goben Nan ba sai na Gaya miki ba karfe shidda kifito ki Dora Mana abincin karyawa kaza Kuma nida mijina da yarana ne zasuci Zaki ci ubanki ba dai mijina Kika Aura ba hmmm"
Tace tana k'ok'arin juyawa ta tafi
Safiyya kuwa ta damko kafadarta da zumar dawo da ita.
Ita kuwa tana juyowa ta kwashe Safiyya fa lafiyayyun Mari biyu ta hankadata har sai data Bugu da kujera dake palon
Ta Kara Mata wani mugun kallon ta tafi.
Safiyya kuwa kamar mahaukaciya ta bita aguje ta cakumeta ita kuwa ta daga Safiyya sama ta hau ruwan cikinta ta hau dukanta kamar yar cikinta.
Ihun Safiyya ne yasa Umar fitowa daga b'angaren kishiyar Safiyya ya nufi wajensu........
[7/12, 10:21 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 45*
Da saurinsa ya Isa wajensu ya rik'e hannayen hafsa dake ta buga Kan Safiyya da kasa Dan karfafa ce ita Bata Wasa ba
wani zubin shi kansa Umar din idan Abu ya hadosu tana Masa mugun duka idan fada ya kaure musu.
Safiyya dafe keyarta da takejin lema tayi da alamar.jinine ta mik'e da kyar tana jiran Umar ya d'auke Hafsa da Mari sai dai a madadin Marin sai ya hau Bata hakuri Yana rarrashinta.
A wahalce Safiyya tace "Umar kanka daya kuwa Taya zaayi matarka daga kawoni yau ta hau dukana amadadin ka tsawatar Mata sai ka hau Bata hakuri"?
Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da bawa hafsa hakuri dake cika tana batsewa.
Mamaki yasa Safiyya wartsakewa daga azabar da takeji a keyarta
Dan Umar din ma hannun Hafsa yaja suka Shiga bangarenta suka rufo k'ofar batare da ma ya Mata ko kallo daya ba
Safiyya kasa ma motsi tayi sabida tsananin mamakin abinda Umar din ya Mata gani take Kamar ba Umar din data aura bane.
Sai da Sauro Suka fara kaiwa fatarta cizo ta koma bangarenta da mugun ciwon Kai ga mugun yunwa da takeji ga ba abinda zata saka a bakinta a tsakiyar palon ta zub'e tana tunanin abinda zai saka Umar ya Mata Haka a Daren ranar da ta tare a gidansa da yake ta dokinta kamar ya cinyeta.
Gwallo Ido tayi data tuna kwallinta data manta dazaa daukota hannu ta Dora aka Dan kwallin Nan shine yake balain tasiri a wajen Umar yau kuwa ko kwallin Bata saka ba.
Ya Zama Dole ta nemi shugabarsu tunda tana garin calabar zata nausa daji nemanta ta Kara Bata kwalli tare da damke Mata Umar ta kuma cin uban kishiyar Nan tata Mai Kama da maza sosai ta zargi kila sabida bata saka kwali ba shiyasa Umar ya wulakanta ta batasan shi kansa Umar din sai yanda uwar gidan sa tayi dashi ba.
A ranar Bata iya bacci ba sabida mugun yunwar da takeji ga azabar ciwon Kai Dan keyarta ya kumbura yayi suntum.
ruwa kawai ta ringa dirkaka wa kanta cikinta na Kara kullewa.