← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 62

Sashe 24

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga calaba nake na Kuma dawo Nan da Zama Dan Safiyya ta siyar da gidan Naseer tayiwa kanta kayan daki banida wajen Zama shiyasa nayo Nan Dan Ni na Haifeka Ina Kuma da iko dakai matarka Bata Isa ta hanani na zauna a gidanan horar yunwar datamin a baya wlh bazan dauka ba indai ta gwadamin kuwa wlh sai ka saketa"

"Mamakine ya rufe Tijjani a lokacin da Hajara tace Safiyya ta siyar da gidan Naseer anyiwa Safiyya kayan d'aki cikin mamaki yace "Umma Safiyya ta siyar da gidan Naseer fa kikace bangane ta siyar da gidan Naseer ba Umma yanzu gidan Naseer kuka siyar Dan ayiwa Safiyya kayan daki innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Hajara Tsaki tayi ta mik'e tana "Duk ba laifin Kai da naseerun bane kuyiwa Safiyya kayan daki kunce bakuda kudi karka sake ka dameni da tambayoyi kaji ko"

"Umma kinsan Allah bazan d'auki abinda kuke yiwa yaya Naseer ba bazan hanaki Zama a gidana ba Amma wlh bana San hayaniya da takura Dan gaskiya bazan dauka ba.

Daga Haka ya fice waje.yana Jin bakinciki siyar da gidan Naseer din datace sunyi har mamaki Naseer ke bashi daya bar Hajara take garashi yanda ranta keso.

Hajara kuwa Inda suka zauna da Safiyya Nan d'akin ta shige abinta da kayanta.
Ta fito daga d'akin ta shiga kitchen Kai tsaye ta zubo abincin da ta gani ta dawo palo ta zauna tana hararar Murjan dake Mata wani irin shu'umin murmushi tana girgiza kai Dan ta daga Mata kafa ne kawai Dan Tijjanin na Nan.

A takaice duk inda Hajara taso itama ta nuna iko da isarta kasawa tayi Dan Murja shu'uma ce ta gaske Dan haihuwa da tayi yasa danginta suka cika gidan Tijjani Kuma ba wani Zama yake ba yana fita zasuyi tayiwa Hajara rashin mutunci Bata Isa ta tanka musu ba idan kuwa ta saka Abu a bakinta sai dai idan Tijjani ne ya dawo ta rokeshi ya Bata makirci kuwa sai abinda ya dadu da Murja ta Karo Dan kawai ta bar gidan

Hajara kuwa duk yanda taso yiwa Tijjani bayani sai yace Mata shi Baya San tashin hankali Shifa ba naseeru bane.

Idan ta masa hargagin ita fa uwarsa ce Bai Kamata ya Fifita Murja akanta ba sai yace wane shi ya Fifita Murja akanta ahaka zai maidata mahaukaciya Yana Mata dariya.

Sosai ta gwammaci zama a koina da zaman gidan Tijjanin Dan sau uku kenan Murja na Mata duka.

Ba yanda batayi da Tijjani ya saketa ko ta tsine masa ba yak'i sakinta yace Mata Yana San matarsa.

Ahaka zata rufe ido. Ta Masa mugayen kalamai idan Murja ta Mata wani Abun shi kuwa Tijjani sai ya fice ya bar gidan

A ranar data cika wata uku a gidan Tijjani
A ranar Safiyya itama ta duro gidan da cikinta da takardar sakin da Umar ya Mata wiwi tana kuka da lodin Kayanta.

Tijjani kuwa rantsuwa yayi bazata zauna Masa a gida ba sai dai ta nemi wajen Zama sai da.hajara ta hau Masa kuka ya bar Murjan ta zauna Dan ko ba komai taji dadin ganin Safiyya da sakin da aka Mata Dan zuwanta zai saka ta Dan samu saukin wani abun daga wajen Murja su Kuma nemi hanyar da zasu ci uban Murjan su dau fansar duk abinda ta musu.

Sai dai zuwan Murja gidan yasa.tijjani ya bud'e kwandunan. Rashin mutunci Baya dagawa Safiyya kafa ko kad'an duk da kanwarsa ce ya balain tsanarta

Ga Murja itama a gefe tana Gana musu azaba Dan kudin da Safiyya tazo dashi na kayan d'akinta data siyar a can calaba da baiyi albarka ba dashi Suke siyan abinci idan Murja ta hanasu

Sosai suke rufe Ido suna neman bokon da zai.musu aiki akan.murja,Hafsa da Umar da suke ganin sune makiyansu a Duniya Bayan Naeema.

Ganin kudin su ya tasama karewa yasa Suka yanke shawarar fara siyar da kosai a waje.

Safiyya ce ta tafi siyan kayan da zasu bukata na kosai

A wani shago dake can kasa dasu

Kamar ance ta waiga ta hango Naseer da Tijjani a tsaye nesa dasu suna magana hakane yasa ta gwallo Ido tana kallonsu

Ganin Tijjanin ya hau vespensa ya tafi shi Kuma Naseer ya fara k'ok'arin tarar taxi yasa tayi saurin fitowa daga shagon itama ta nufi titin da Sauri tana rufe fuskarta.

Tana Isa titin Naseer.ya samu taxi ya shige

Itama.ta tari wani da Sauri ta shige ta ringa bin bayan Naseer.

A takaice ahaka ta rufe fuskarta tabi Bayan Naseer har k'ofar gidan Naeema

Ta gwallo Ido a lokacin da ga su Minal sun fito suna Masa oyoyo.

Ya rik'e hannunsu Suka Shiga gidan

Sai da Safiyya ta Fadi ya Kai sau uku sabida azabar saurin ta koma gida ta Sanar da hajara Kamar ta tashi sama.

Ido rufe ta Kara Hawa taxi ya maidata unguwar su Tijjani tace ya jirata gata Nan fitowa.

Hajara kuwa Safiyya na Bata labari ta hau had'a Kayanta tana Godewa Allah.

Cikin kankanin lokaci suka jiddi kayansu suka zuba a taxi Suka dau hanyar dorayi Kamar su karbi tukun Dan gani suke Kamar ba tafiya taxin keyi ba.....

*Inaso na Dan Yi shi a gurguje mu shiga ainihin chapter 3 na labarin Naeema Dan na Gaya muku Yana da tsayi ahaka ma masu Dan mahimmancin nake rubutawa*
[7/16, 8:31 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 46*

Suna isowa k'ofar Gidan jiki na rawa suka mik'awa Mai taxin duk kudin hannunsu kowacce ta fito da kayanta da kanta bakinsu a washe Kamar gonar auduga sosai sukeji Kamar sun samu yancin kansu.

A k'ofar shagon da Isihu ke sallamar mutane suka tsaya suna karewa gidan kallo.

Hajara ta Shiga shagon ta daga Kai sama tana kallon yanda shagon yake cike da Kaya har da buhunan danyen abinci ake siyarwa a shagon

Da farko Bata Gane Isihu ba sai daga baya tace"Shege Ashe kaima Nan din ka gudo shiyasa baa ganinka Kai Kai kai Safiyya Kinga katon shagon da Naseer ya bud'e amma muke zauna a gidan Tijjani muna Shan bak'ar wahala kawai sabida an siyar Mai da gida sai yamin karyar zai Shiga duniya Ashe Yana. Nan Yana Jin dadin rayuwarsa da Naeema da yayansa.

"Wanan ba shagon Yaya Naseer bane shagon aunty Naeema ne"

Isihu yace Yana had'e Rai tare da fusge bredin da Safiyya ta d'auka Dan bak'ar yunwa takeji cikin jikinta balain sakata cin abinci yake.

"Iyye a gidan uwarka ya Zama shagon Naeema wato abinda aka kitsa maka kenan ka.ringa fada zaka ci ubanka Bari nashiga gidan wlh sai na saka Naseer ya koreka daga shagon Nan"

Daga haka ta fito daga shagon Safiyya na dannawa Isihu zagi tare da dumbuzar garin kwakin dake cikin buhu ta tura a bakinta Dan kamar taci babu Haka takeji.

Ba Wanda yayi Sallama a cikinsu suka Shiga gidan.

Ina zaune a tsakar gidan Ina yiwa Zahira kitso su Nadeeya su Kuma suna cin shinkafa da miya da kifi Naseer kuma ya Shiga d'akina yayi wanka Dan ya canja Kaya ya Kara fita Dan Tijjani ya Nemo Masa irin aikin da yakeyi a wani company duk da albashinsu ba yawa Haka Naseer ke fita da sassafe idan sun samu break sai ya dawo gida yaci abinci ya Kara watsa ruwa ya fita bazai dawo gidan ba sai wajen Goman Dare.

Dawowar Naseer da siyar Masa da gidan da su Umma sukayi sai Dana Yi dgsk Naseer ya iya fawwalawa Allah komai Dan sosai yayi rashin lafiya gidansa.

A ranar da Umma taje gidan Tijjani take Sanar.masa da sun siyar da gidan

A ranar Tijjani ya nemi gidanmu yazo ya kuwa tarar da Naseer a gida.

Sosai ya nuna Jin haushinsa da Naseer ya Bari Suka cutar dashi Bai dau mataki ba har korar Hajara yayi niyyar yi ya Bata kudin mota ta koma calaba wajen Lami ko Safiiyya Naseer yayi ta rokonsa akan yayi hakuri Kar ya koreta tausayin Naseer yasa ya Nemo Masa aikin dak'yar da albashin ba wani taka Kara yayi ba Amma ya gwammace ya ringa fita din daya zauna Haka Naeema na d'aukar Nauyin shi da yaransa.

Naeema kuwa budi take samu ko ta ina Dan har katon fili ta siya da Sunan Waleed.

Tunda Naseer yayi ramar siyar da gidansa da su Umma sukayi Bai Kara maida jikinsa ba.

Ni kuwa daga Ni har yarana munyi sharr damu ban taba tunanin Zan danyi kib'a a rayuwata ba sai yanzu Zan iya rantsewa ban taba jina a cikin kwanciyar hankali batare da fargabar komai ba sai a yanzu da babu umma da Safiyya dake dagamin hankali Ashe Zan tab'a tsintar kaina a cikin kwanciyar hankali Haka kudin da nake samu Bai taba sawa na Raina Naseer ko na nuna Masa iko da dukiyata ba duk da Naga alamar Yana da gudun zuciya Dan karfin Hali irin nasa yasan muna da komai Amma idan aka bashi allowance din sati ko albashi sai ya Dan tsinto Mana wani Abu ya kawo na amfanin gidan.

Sai danayi dagske ya daina siyowa nace ya ringa Tara kudin ya samu na siyan fili Dan Naga rashin gidansa har yau yasa bashida walwala Kuma Yana fama da ciwon kirji har yanzu.

Yarana kuwa duk suna ingantaciyar makaranta Dan Zahira yanzu tana jss 2 San Sai da aka Mata tsallaken jss1 sabida tsayinta.

Sosai nake mamakin girman Zahira da kyaun da Allah ya Bata da ko Ni Dana haifeta wani zubin bana iya d'auke idona akanta.

Ga balain farin jini da Allah ya Mata na kawaye tun ma ba'aje koina ba Wai wasu ke zuwa Sallama da Zahira.

Nadeeya ce take primary 5 yanzu Minal a primary 4 Humaira 3 Raheema a primary 2 Waleed Kuma na nursery Dan makaranta ma Dana saka shi na daban ne.

Shigowar Umma da Safiyya yasa na saki baki Ina kallon ikon Allah.

Yarana dake cin abinci kuwa duk suka Mik'e tsaye Suma Kamar sun ga dodon Ni
Chapter 24 · 0% Book details