← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 62

Sashe 15

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuwa na fara k'ok'arin bin bayanta aguje naji Naseer ya ruk'o hannuna ya Kuma jawoni jikinsa ya kamkameni ta baya tare da Dora kansa a kafadata naji dumin hawayensa a kafadar tawa daya haddasa min wani irin raunin zuciya da San na juya na rungumeshi na rarrashe shi

Cikin rawar murya ya fara magana Yana "kiyi hakuri Naeema nsan kinyi hakuri Zama da Mahaifiyata tsawon shekaru Wanda sai da Kika tafi nagane irin hakurin da kikayi da ita Naeema na kasa sauke nauyin da Allah ya doramin na gaza ciyar dasu na gaza tufatar dasu ba irin kudin da ban nema ba ban samu ba Naeema Dan Allah idan Kika tafi da yaran Nan ki Kular min dasu Allah ya Baki Lada ita kuma Nadeeya tunda ta dage bazata biki ba ki barmin ita Zan kula da ita insha Allahu na Kai su gidan Tijjani ne sabida Ina tunanin acan babu Mai musguna musu bansan matarsa itama ba matuniyar arziki bace na Miki alkwari bazan Bari Umma ta Taba Nadeeya ba indai ta Taba ta insha Allahu da kaina Zan kawo Miki ita"

Duk maganar Nan da Naseer kemin Yana kamkame Dani kansa Akan kafadata Yana zubar da hawaye nima hawayen nake sosai Dan. Har ga Allah a yanzu ne Naseer ke bukata ta a kusa dashi yau da Umma Bata sako mu agaba ba Dan abinda nake samu iya zaman duniya dai zai ishemu dagani har yarana da Naseer Amma Umma ta dage sai mun rabu.

"Daga Bauchin Kika zo"?
Naseer yace
Girgiza Masa Kai nayi Ina k'ok'arin Magana naji muryar Umma cikin ihu tana "Yau Naga karuwa har cikin gida yau Naga ikon Allah yanzu har daki Kika shigo Dan ki yaudari Naseer ya Kara miki wani cikin kenan kamar yanda Kika Saba Kai jamaa wannan yarinya anyi jarababbiya kwartuwa"

Fusge jikina nayi daga na Naseer da har lokacin yake rik'e Dani tsayuwar Umma a bakin kofar d'akin Bai saka ya cikani ba Ni kuwa na ja Tsaki na bangaje Umma dake bakin kofa ta kawo hannu zata kawomin duka Dan sai data Kusa fad'uwa dana bangajeta na kauce "Shegiya karuwa Dole ki hankadani tunda na kamaki kina k'ok'arin yiwa Dana fyad'e"

Bance Mata komai ba na fice waje ta biyoni har waje tana min ihun kwartuwa

Naseer kuwa magana yake Mata Yana k'ok'arin hanata Amma sai ihu take cigaba da yi.

Hannun Raheema kawai na rik'e Dan Waleed na hannun Aunty su Zahira Kuma suna can gaba dasu Minal.

Muka hau tafiya Ina danne kukan dake neman fitomin ta karfi Dan har waje Umma ta fito tana min ihun kwartuwa karuwa.

Wai nice karuwa ban waiga ba duk da naji Naseer ya daka Mata wani uban tsawa akan tayi shiru Amma a madadin tayi shirun sai cewa tayi "Saukar Mari nake jira naji Dan ka Riga da ka Saba marina Maza Mareni sabida wancan karuwar data biyoka har gida zata maka fyad'e.

Naseer bakin ciki ne yasa ya koma ciki ya lek'a dakin Umma ya ruk'o hannun Nadeeya suka fice daga gidan.

"Gaskiya ban taba ganin uwar miji irin Taki ba Naeema duk yanda Zaki bawa mutum labari bazai Gane ba sai ya ganta da idonsa wlh rabuwarki Da Naseer yafi alheri Kai wanan Mata anyi tsinaniya yanzu Nadeeya dagewa tayi bazata bikin ba"? Mai yasa Baki tilasta Mata ba Naeema kinsan yarinta ke damunta ita gani take ba Wanda zai zauna da abbanta shiyasa ta dage bazata biki ba"

"Hmmm"

Kawai na iya cewa Aunty Dan Sam bana Jin yin magana sabida abinda ya tsayamin a mak'oshi yak'i tsirgamin

Muna fita titi na tare Mana taxi su Zahira suka Shiga na karbi Waleed daga hannun Aunty
A k'ok'arina na inyi magana na fashe da kukan dake cina tundazu

"Sai hakuri Naeema Allah dai ya shiryi matar Nan idan tana da rabon Shiriya

Ban ce Mata komai ba na Shiga taxi Ina cigaba da kukana.

Sunkuyowa Aunty tayi daidai window motar tana "zanzo jibi kafin na Zo dai Zan lek'a gidan Naga ko Zan iya shawo Kan Nadeeya dan inaga sai kinfi samun kwanciyar hankali idan Kika gansu a gunki gabadaya.

Kai na gyad'a Mata muka wuce.

Muna Isa Muka sauka gabadaya na karbi kudi a wajen Hassana dake ta markade na bawa Mai taxi.

Na dawo muka zauna a palo gabadayan mu.

Yarana sai kalle kalle suke.

Sosai nake Jin ba dadi da Nadeeya Bata biyoni ba da nasani na Mata tsinannen duka na taho da ita Dan ai ba fin karfina tayi ba Naseer ne ma yake wani lallaba ta.

Kitchen na fita na Dora Mana ruwan tea Dan Nima ban karya ba na fita shagon k'ofar gida da Isihu shima tafiya da nayi karbowa Waleed magani Nazo na same shi ya dawo daga garinsu rashin nutsuwa yasa ban ma bi ta kansa ba

Hassana dai tacemin shi yake jire min shagon

Kayan shayi na d'aukar Mana da manyan bredi har da kwai wajen goma

Na koma ciki na soya Mana na fito da kofuna na kwallawa Zahira Kira tazo ta d'aukar Mana flask din shayin.

Sosai jikin yarana ya ringa rawa farinciki shimfide a fuskarsu ahaka na zubawa kowace Madara da bournvita Dan gwangwanin su na dauko.

Kwan Kuma na ajiye a tsakiyarsu.

Sosai jikinsu ya ringa rawa wajen Shan shayi Kamar basu tab'a cin abinci ba.

Bare Zahira da duk zafin shayin Haka take kurba sosai tausayinta yasa kwalla zubomin Dan ga shattin tsintsiyar Nan a kwance a wajen idanta ga jikinta Nan ma yayi rudu rudu sabida duka.

Hannunta kuwa ya Kara sirrancewa kasancewarta Mara jiki.

Ganin ta a irin halin Nan yasa nama.kasa cin abincin nace "Zahira Mai ya samu jikinki haka"?

Hadiye kwan data saka a baki tayi tana "Aunty ce take zanemu kullum"

"Da kuka Mata me take zaneku kullum"?

Shanye shayin daya Mata saura tayi ta hau bani labari irin rayuwar da sukayi a gidan Tijjani da yanda Take dafa wake Mai uban attaruhu da sabulu Tana bani labarin tana kuka Dan Abu kad'an ke saka Zahira kuka ko tsawa ka daka wa Zahira yanzu Nan zaka ga idonta ya ciko da hawaye

Sosai na ringa kuka Ina duba jikin Zahira daya Sha tabon bulala da dorina "Allah ya Isa tsakani na da ita bazan tab'a yafe Mata cutarmin daku da tayi ba Mai kuka Mata da zata azabtar daku Haka har ta muku horon yunwa ta ringa bawa Nadeeya Sabulu da wake sabida mugunta Allah ya Isa bazan yafe Mata ba Allah sai ya muku sakayya tun a gidan Duniya idan Allah ya yarda Allah sarki Nadeeya yanzu Haka ta ringa cin wake da sabulun babu abinda ya sameta"?

"Eee umma sai dai tayi ta kashi Mai kumfa tacemin duwawunta na yaji idan na hanata cin wake sai tacemin yunwa takeji sai taci"

Kaina har ciwo yamin sabida kukan zalincin da matar Tijjani tamin

Sai da Hassana ta Gama markaden tazo ta zauna na Dan Bata labarin duk wuyan dayarana suka Sha taci kuka itama tana Dama Nadeeya ta biyoni .

Nima iirn wuyan da Zahira ta bani Akan nadeeya ta Sha naji inasan na dawo da Nadeeya gabana na kula da ita

Ita da Minal suna da balain ci

Anan Zan Basu duk abinda suke so ta dawo Nan tabar Naseer Yaji da kansa

Hassana ce ta Tayani tsefewa su Raheema Kai har Minal ta musu wanka ta wanke musu Kai.

Zannuwana na raba musu Suka daura na janyo gwangwanin na danake Tara kudi .
Na duba Naga kudin ciki da Dan yawa na dibi yanda zai isheni karfe uku na nufi Sabon gari Dan acan na Dan Tsintowa Waleed Kaya masu kyau kamar sababi Kuma a kudi kalilan.

Sosai na jiddo wa yarana Kaya har da panties Zahira danaga ta fara kirgen dangi har ves ves na siya Mata dasu under wear duk abinda na daukarwa Zahira sai Dana d'aukar wa Nadeeya

Dan nasu zahiran yadan fi yawa.

Kala.uku na daukarwa Isihu shima Dan ya zama tamkar Dana Tinda barina gadon Kaya yasa shima ya hakura da makaranta ya dawo wajena duk da ba a gidana yake kwana ba a wani makaranta Allo dake unguwar yake kwana a Kuma Nan yake karatu.

Sai wajen Magriba na isa gida.

Yarana sai tsalle tsalle suke suna Wasa Zahira itama sai washe baki take abinda ya ragemin Jin dadin kasancewata dasu shine Nadeeya da Bata Nan Dan da tana Nan da kila hankalina Bai rabu gida biyu ba.

A Daren nida hassana har da zahiran muka wanke kayan gabadaya.

Suka saka vest din Dana sisiyo.musu.

Zahira akwai San.kallo Dan tv black and white Dana siya karami da lokacin tashar Nta ne kawai da ctv suke Dan drama Dan sai kana da video kake iya siyan cassette kayi kallo.

A gaban tv tayi zaman dirshan tana ta kallo har kannenta sukayi bacci suka barta.

Sai da zamu kwanta na umarceta data kashe.

A daki daya muka kwana gabadaya Banda hassana.

Ni kuwa Sam baccin ma Bai min wani dadi ba sabida zuciyata dake wajen Nadeeya.

Naseer kuwa Yana barin gidan Bai zame ko Ina ba sai wajen da aka basu kwangilar gini.

Ya samo benci ya zaunar da Nadeeya ya siyo Mata shayi da bredi har da kwai ita kuwa ta hau ci tana Masa hiran sabulu da waken da Murja ke basu sunaci.

Ta dage rigar jkinta tana nuna Masa shattin bulala dake kwance a jikinta tana "Abba kaga yanda ta zanemu kullum sai ta dakemu ta zageka ta zagi Umma Wai an kawo Mata jarraba"

Naseer kasa magana yayi Sabida tsananin b'acin Rai dayake Nadeeya tana da surutu a take ta bashi labarin duk rayuwar da sukayi a gidan.

Naseer sosai ya daure baiyi kuka Agaban Nadeeya ba sabida yanda yake ji a Ransa wai da Ransa aka zalunci yaransa Haka Bai taba tunanin Murja Haka take ba Taya yaransa zasu Sha wanan bak'ar wahalar Tijjani yace ko sau daya Bai taba Sani ba baya ganin jikin yaran nasa ne Zahira dake ruwa ruwa wajen kuka ai ko kallon minti uku ya Mata yaci ya Gane Ana gana musu azaba.

Sosai ya rik'e tijjjani a Ransa.

Dan Bai ga wani laifin Murja ba Tijjanin da Bai saka Ido a gidansa ba yaga laifinsa.
Chapter 15 · 0% Book details