Sashe 61
Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba Wanda ya amfaneta da wani Abu.
Sai Rabia da take wahalar da ita da bata da bambanci da wata dabbar tana girma tana Kara zama abin tsoro
Tunani da abubuwa dake rayya Mata munanan abubuwa yasa ta d'auko wuka
Ta nufi d'akin da Rabia ke kwance tana Isa wajenta ta daga wuk'ar da zumar soka mata dan ji tayi gwara.kawai.ta kashe Rabia ta huta
Tana daga wuk'ar taji kamar anyi cilli da ita.
Wani iirn gugguwa Mai k'arfi ya zagayeta
Ta hau wani irin jijjiga tana Kara duk Aljannu dake azabtar da Rabia Suka bar jikin Rabia suka Shiga jikin Safiyya
Wani irin canza Mata hallitar fuskata sukayi fuskarta ta dawo bakikirrin wuyanta yayi wani irin kumburewa idonta yayo waje gabad'aya
Ihu kawai take Tana birgima.
Har gobe haka Safiyya take fama da kumburarren wuya da Ido a warwaje takan dan tab'a hauka wani zubin.
Daga ita har Hajara Basu nemi yafiyar.naeema ba suna Nan Kuma da tsanar Naeema dama ne kawai Basu samu ba
Safiyya k'arfi da yaji ta koma yin Abun mahaukatan aka koreta daga gidan hayan
Hajiyayye budurwar Bashir kuwa Yana rasuwa ta kama gabanta
Asmau kuwa tana nan a haukacenta
Safiyya data haihu guduwa tayi.ta bar gidan
Rabia kuwa aljnnun suna barin jikinta ta dawo daidai.
Ita kadai ce a yaran Safiyya bayan Aljannun sun bar jikinta wani Abu Bai sameta ba sai ita ke kula da yaran Safiyya da Asmau.
Naeema
Godiya kawai nake yiwa Allah daya bamu ikon ganin auren Zahira da Nadeeya da nake Jin tunda na auri Naseer ba Abunda ya tab'a faranta min rai sama da Aurensu.
Yarana suna cikin rufin asiri a gidajen mazajensu.
Yara na Kuma dake gabana suna cigaba da zuwa makaranta ina kula da tarbiyyarsu Naseer na cigaba da sana'oin hannunsa Wanda dashi asirinmu ke rufe.
Ranar da bazan taba mantawa ba watansu Zahira hudu da aure daga amai da gudawa na kwana uku Inna Amina ta amsa Kiran Mahallici Ko lokacin Dana rasa iyayena banyi kukan da nayi da rasuwa Inna Amina ba
Ba iya ni ba har Naseer da sauran yarana Allah ya jikanta ya Kai haske kabarinta sosai na ringa ji Kamar wani barin jikina ce ta tafi ta barni.
Sanin watarana dole ko muna so ko ba ma so mu ma zamu amsa Kiran Mahallici dan mutuwa ta zama Dole akan kowa
Haka muka bi Inna Amina da Addu'a dacewa da rahamar Allah
Mu ka cigaba da fuskantar rayuwa yau da Dadi gobe akasin haka har Allah ya sauki Zahira lafiya ta haifi yarta mace Mai Kama da ita Inda Abubakar yamin Kara ya saka Mata sunana ake kiranta da iman
Iman nada wata uku a duniya Abubakar da mahaifinsa da su kaje gaisuwa garinsu rano sukayi mummunan hatsari suka mutu
A shekara 2012/10/10 wanan Rana Yana cikin ranakun da bazamu taba mantawa ba anyi Mana rasuwar da ya dakemu da har yata Zahira sai da muka dage Mata da Addu'a kafin ta iya dawowa daidai
Bazan manta Abubakar da mahaifinsa ba har gobe Muna adduar Allah ya sadasu da rahamar Allah yasa Aljanna ce makomarsu
Zahira na fita daga takaba naso ta cigaba da zuwa makaranta ta nuna min bata son komawa makaranta tafi so ta cigaba da sanaarta ta dinki har yanzu Zahira tana nan tana dinkinta
Yarana dukansu rayuwar da Allah ya tsara musu shi suke dan Nadeeya yanzu haka yaranta uku Minal itama tayi Aurenta da yaranta biyu.
Sai Humaira yanzu da aka sawa Rana
Waleed toh sai dai nace Alhamdulillah Yana Nan da taurin Kai Bai koma min kamar Waleed din Dana sani ba abinda aka masa Kan motsa Masa wani zubin ba Kuma sa shiri sosai da mahaifinsa.
Naseer ko tuna Umma da Safiyya baya so yayi.
Shekara 2016 wani makocinmu Sagiru da muka zauna a garin calabar yazo garin Kano neman Naseer da kyar da.kwatance ya gane gidanmu.
Sai da ya huta yake fadawa Naseer dalilin zuwansa akan Umma yazo shima bai fiye zama ba sabida tafiye tafiyen da yake Yi
Sai kwanaki ya dawo ya Shiga kasuwa yaji an rik'e Masa Riga da kyar dak'yar ya Gane Umma Inda Umma ta fashe Masa da kuka dan ta Gane shi tace ya taimaka Mata ta Kira mishi Naseer yunwa zai kasheta mutane gudunta suke dak'yar take samun na abinci
A labarin yake fadawa Naseer kila umma hatsari tayi sabida yanda kamaninta Suka canja dayake a can kowa yasan waccece Umma daidaiku ne basu san halinta ba naseeha sagiru ya hau yiwa Naseer Akan Bai Dace ya wulakanta Umma ba ko Mai tayi Masa kuwa yayi hakuri yanzu tana bukatar taimakonsa
Naseer amsa shi kawai yayi akan zaije kwanan sa biyu ya koma
A zuciya irin tawa da tausayi halin dana ji Umma na ciki ya sanyaya min jiki ya Kuma Sakani Jin tausayinta hakane yasa na hau yiwa Naseer maganar yaje ya ganta dan uwa tabbas ba Wasa bace
Sai dai ga mamakina Naseer b'acin Ransa ya nuna min yamin gargadi Akan Kar na Kara Masa maganarta duk halin ma da take ciki ita ta jawowa kanta.
Naso na share kamar yanda ya share din sai naji zuciyata ta ki nutsuwa yanda sagiru ya bada labarin wuyan da Umma ke Sha ya tsayamin a wuya Ni nasan hakkinmu kawai bazai bar Umma da Safiyya su zauna lafiya ba sai dai idan har mun yafe musu.
Damuwarta Dana saka a Raina yasa har mukayi zancen da Zahira Zahira ta shawarci naje idan har abbansu bazai je ba mu Rama sharrin da suka Mana da alkhairi yanzu tunda tana samun kudi nayi amfani da kudinta na yiwa Umma siyayya nace Mata tana rayye tayi aure Allah kuma ya azurta ta da iman
Ni nasan da biyu Zahira take san naje Ni nasan so take ta nuna musu ranta baa hannunsu yake ba yanda suka so kasheta Allah baiyi ba gata Nan a rayye
Nima sai naji inasan na gansu Naga ya suka dawo din
Dana tari Naseer da zancen zuwa calaba nida Zahira bai Hana mu ba
Ya Mana fatan dawowa lafiya ya Kara da duk abinda ya biyo baya Kar muyi kuka dashi.
Insha Allahu ba Abunda zai biyo baya Nima inaso suci arzkin yarana da suka so watsa rayuwarsu
Zahira cemin tayi zata bini muje can calabar da biyu Kuma naji inasan zuwa sabida na cigita Mallam Musbahu dan har na mutu bazan manta alherinsa a gareni ba.
Nadeeya har da turmin zaninta da kudi Wai mu bawa Umma muce Mata itama tana cikin rufin asiri a gidan mijinta.
Dak'yar na gane unguwar da.muka zauna dan garin ya sauya sosai anyi gine.gine unguwar ta Kara cika ba kamar da ba
Da taimakon Sagiru Muka gano Inda Umma ke zaune a rumfar mahaukata.
Ganin Umma kawai da nayi yasa na fara yiwa annabi sallati mun kad'u mun razana da yanda ta dawo dan Zahira har buya tayi abayana sabida tsoratan da tayi
Mun dauka ganinmu zai saka ta hau hawaye tana neman yafiyarmu.
Sai dai fuskar ta a karkace.
Take jifanmu da mugun kallo
Da da yanzu ba daya bane
Ina daga tsayen na gaisheta Ina karewa wajen da take kwana kallo.
Akan tsomokara take zaune rumfar sai doyi yake.
Bata ce Mana komai ba ta cigaba da shafa wani Abu a kumburarren kafarta.
Ni kuwa ledojin da muka ciko Mata da kayan abinci na ajiye mata ina gashi inji zahira akwai sakon Nadeeya a ciki da kudi.
Yarana dukansu sun hada kudi Akan mu bata.
Na dauka zata watsar da ledar ga mamakina da hannu biyu ta fusge Leda fuska a karkace take hararana Tana
"Wlh ko duk duniya Zaki bani Naeema bazan tab'a sanki ba har gobe Ina Kan bakata bana sanki bana kaunarki Dana Kuma da Kika rabani dashi Allah ya Isa tsakanina dake Kaya Kuma na karba Dan nasan bada kudinki Kika siya ba"
Mai Umma zatayi da zai bani mamaki ban ganshi ba hakane yasa kalamnta ma Basu bani mamaki ba illa tausayi ma da tabani dan nasan Umma har yanzu Bata da rabo kila shiyasa ta kasa Gane gaskiya da tana da rabo iya karkacewar Nan da tayi ya isa.yasa taji tsoron Allah"
Amma gashi a wulakance da take tana Nan da kiyayya ta a ranta
Koda Muka bar wajenta
Sai Dana siyi katifa na aika Mata dashi.
Yanda akayi nasan halin da suke ciki kenan Safiyya ban samu na sakata a idona ba Amma naji labarin irin wuyan da take Sha da haukar da take dan tab'a wa Allah ya tsare Mana imaninmu
Bazan iya cewa matsalarmu ya kau gabadaya ba ba a rasa dan jarrabta na rayuwa da bawa ke fuskanta yau fari gobe baki sai dai muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawarmu wanan shine labarina nakan ji labarin wahalar rayuwa da Umma da Safiyya suke sha ta wajen iyalan Sagiru duk wanan bai.isa su gane gaskiya su nemi yafiyar wayanda suka zalunta ba rayuwa tun a gidan Duniya Allah yake yin hisabi Allah yasa mu cika da kyau da Imani ameen
Naeema.