← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 62

Sashe 55

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin siga na hau shigar Masa da maganar Waleed da naga rabi yafi damuwa da halin da Zahira ke ciki har Yana cemin yanzu so yake idan mun koma gidansa ya dukufa da Addu'a Zahira ta samu Lafiya idan na Shigar Masa maganar Waleed sai ya Sako min wani zancen.

Washegari da sassafe aka hau jiddar kayanmu Ana kaiwa sabon gida

Ina ganin ya fita naje na samu Inna Amina cikin damuwa na hau gaya mata karantar da nayiwa Naseer akan Waleed.
Hakuri ta bani tace na bi komai a hankali Kar na damu kila Abunda akayi a tsakaninsu bai gama warware bane mu cigaba da Addu'a.

Yarana murna kawai suke zasu koma sabon gida Nima a kasan Raina na ji dadi sosai da Naseer ya samu ya Gina gidan kansa tamkar ni nayi gidan haka na ringa ji shima fuskarsa kawai zaka kalla kasan Yana dokin sabon gidan da yayi kamar bai tab'a gidan kansa ba.

Ranar tashin namu daga Zahira har Waleed ba Inda suka je a ranar duk da Ina lura da Waleed da Naseer suna Yar kallon kallo Wanda hakan ya dameni sosai.

Da yamma na shishiga mak'ota muka musu Sallama

Inna Amina ita ta ringa lallaba Waleed dan kar ya botsare Mana yace bazai bi mu ba.

Su Nadeeya dama sun dade a can dan tun safe Naseer ya Kai su dan su shirya Mana kayayyakin mu.

Iya ni da Inna Amina sai Waleed da Zahira ne bamu tafi ba sai daddare Naseer ya kawo taxi muka hau Muka tafi gabadaya.

Gidan yayi kyau ba laifi duk da gidan bai Kai girman gidajensa na baya ba dakuna hudu ne a gidan da falo kitchen da band'aki a kowane daki.

Dan karfin hali har da dan kujeru sababi masu saukin kudi.

Daga ni har yarana Sai murna muke Dakunan duk a cikin falo suke d'akin da bai Kai sauran girma ba aka sawa Inna Amina karamin katifarta da kayanta.

Su Nadeeya Kuma suka dau d'akin tsakiya suka saka katifarsu guda biyu.

Daya d'akin Kuma shine nawa dayan na Naseer.

A Raina naso Waleed nada d'akinsa ba d'akin daya dace ya d'auka Sama da Wanda Inna Amina ke ciki Amma insha Allahu zanyi k'ok'arin sama Masa d'akin.

Ban dawo daga tunanin dana tafi ba naji Waleed cikin dan daga murya Yana "Ni a wane daki Zan ringa kwana"?

Naseer d'auke kansa yayi ya shige dakinsa

Tuni naga Waleed na k'ok'arin Hawa wanan dokin zuciyar tasa dake sa yayi zuciya ya bar gidan

Allah cikin ikonsa Inna Amina tayi saurin cewa a d'akinta zai ringa kwana ita a dakinsu Zahira zata ringa kwana dan Sam Bata San kwana ita kadai

Inna Amina ce ta taimaka min aranar waleed bai zuciya ya bar gidan ba.

Tunda Muka dawo gidan na lura Naseer bai fiye baccin dare ba yakan raba daren wajen sallah da Addu'oi tamkar dai yanda ya ke yi ada.

Hakane yasa nima na Kara akan Wanda nakeyi da.

Dawowar mu sabon gida tamkar k'ofar samun warakar yarana ne dan a hankali naga Zahira da Waleed sun fara nutsuwa suna Jin maganata har sallah da suke Wasa dashi yanzu suna maida hankali suyi duk yawace yawacen nan da sukeyi yanzu basa yi duk da Basu dawomin dai yanda Suke gabadaya ba Amma ko hakan suka zauna alhamdulillah.

Allah kawai nake Godewa daya amsa Mana adduar mu akan yaranmu.

Abu daya ke damuna Naseer da Waleed Dana ga Kamar basa ga miciji dan yanzu Waleed na gaishe shi wani zubin ya amsa wani zubin yyi kamar bai ji ba

Inna Amina ke ta kwantar min da hankali tana hanani yiwa Naseer magana akan Kar na damu komai zai warware tunda har Allah yasa sun fara dawowa hayyacinsu ko Kuma muce sun ma dawo tunda yanzu duk sun daina Abunda sukeyi Waleed abinda kawai bai bari ba shine saurin zuciya da fushi.

Itama Zahira hakane Amma ta dawomin zahirata yanda take a da.

Burina Zahira da waleed su koma makaranta Dan an barsu a baya sosai hakane yasa nayiwa Naseer magana take ya Nemo makaranta ya biyawa Zahira waec shi Kuma Waleed da k'arfi nasa ya nema Masa makaranta ya fara daga jjs 2 duk da ya girma da jss 2 din Amma haka ya fara zuwa dan a haka ma mun masa tsallake.

Sai a yanzu na samu kwanciyar hankali nake Kuma Godewa Allah da Kara neman kariyarsa a garemu gabaki daya

Naseer yanzu kanannan sana'oin daya koya dashi yake rik'e damu duk da Nima Ina taimaka masa sosai dan ban saki sanaar da nake ba na siyar da kananan Abubuwa a gida.

Zahira na dab da gama zana waec dinta tamkar yanda take da farin jinin samari awancan lokacin haka samari Suka hau layi a k'ofar gidanmu Wanda hakan ya sakani farinciki sosai dan inata addua Allah yasa Kar Nadeeya ta rigata aure tunda itace babba data samu Mai kaunarta Zan cewa Naseer mu aurar da ita.

A Rana sama da mutane biyar na sallama suna neman Zahira

Hakane yasa na zaunar da ita na gaya Mata a cikin masu kaunarta ta zabi wanda hankalinta ya kwanta dashi dan muna so tana gama jarrabawa idan Allah ya nufa tayi auren

Ta cigaba da karatu a gidan mijinta sai dai budar bakinta sai cemin take ita so take ta cigaba da karatu tamkar yanda Nadeeya ta cigaba da karatun dan ita burinta tayi karatu Mai zurfi ta Zama lawyer dak'yar na shawo kanta ta amince zata tsayar da mutum daya

Take kuwa ta tsayar da wani kabiru da Saurayine Mai Kuma kudi dan wlh duk Samarin Zahira ba karamin mutum.

Tana gama jarrabawa ya turo magabatansa da kudin neman aurenta.

Manyansa suka Kara da basa San a saka dogon lokaci kabiru yace zai dau nauyin komai ba sai mun wahalar da kanmu ba.

Naseer kafewa yayi akan su bashi Nan da wata shidda zai Mata komai shi Baya so ayiwa Zahira gori.

Sai dai dangin kabirun da roko da magiya da kyar suka shawo kansa ya amince aka saka wata daya da sati daya.

Fadar halin farinciki Dana tsinci kaina a ciki bata Baki ne kudi na hau tarawa Inna Amina Tama fi kowa farinciki na kasa yarda zahirata da aka so watsawa rayuwa ce ta samu nagartacen miji har baifi sauran sati uku Aurenta ba.

Dukanmu shiri muke har Naseer saura sati daya auren Zahira da kabiru aka kawo lefenta akwati shidda cike da kaya masu tsada a wancan lokacin.

Nadeeya da Minal iyayen doki ba Wanda Basu Kira ganin lefen Zahira ba.

Gefe daya Kuma dagani har Naseer da Inna Amina addua muka dukufa dashi ba dare ba Rana.

Ana saura kwana uku daurin Auren Zahira kabiru ya aiko yan uwansa akan a bamu hakuri ya fasa auren Zahira hmmmmmm....

Advertisement

Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples,
Black spot
cream reaction
eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰
Soap price:3k
Chat 08062991549 to plc ur orders
Call:08064532391
We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏
we can't wait to be a part of your beauty story🤭[8/23, 2:44 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

Page 62

Suman zaune nayi bakina yamin nauyi ballantana na tambayesu dalilin daya sa kabiru yace ya fasa auren tunda Suka Fadi abinda ya kawosu naji kamar an sokeni da kibiya a kirji har yau da nake labarin nan Ina fama da Wanan ciwon kirjin idan abu ya girgiza ni.

Muryar Zahira naji da bansan lokacin da ta fito da ga daki ba sai ganinta nayi a tsakiyarmu

Kwalla cike da idonta ta zub'e a gaban wacce take yayar kabirun da itace Kan gaba wajen Shirin bikin kanin nata ba ma a garin Kano take aure ba daga Abuja tazo.

"Aunty Mai nayi Masa yace ya fasa aurena"?

Aunty yau saura kwana uku aurenmu ba Wanda Bai San zamuyi aure ba Mai nayi Masa da sai a yanzu zai janye"?

"Wlh bansani ba Zahira jiya ya sako mu a gaba akan muzo mu baki hakuri akan ya fasa auren ba yanda ba muyi dashi ba ya gaya Mana dalili yak'i da yaga mun dage Masa ma sai ce Mana yayi idan muka matsa Masa Zai kashe kansa Akan Dole yasa muma muka zo yanda Kika ga Kuna ta Shiri wlh muma haka muke shiri ba Wanda bai zo ba duk gidan mu baki ga yanda muke kaunarki ba amma kabiru lokaci daya yace mu zo mu baki hakuri ga wasika nan ya bani na Baki"

Yayar kabirun ta karashe kamar zatayi kuka tare da mik'awa Zahira da hawaye ya jika gaban bak'ar doguwar rigar da ke jikinta hannunta ya Sha Jan kunshi da baki gashinta har baya ya sauko dan Kamar yanda naji su Nadeeya na shiri a yau zasu yi kamu a gidan wani Alhaji dake kallon gidanmu yanzu haka ma su Nadeeya na can suna ta shirya wajen.

Zahira ba ta iya karbar wasikar ba illa mik'ewa da tayi ko taku biyu ba tayi ba ta zub'e a kasa.

Nayi kanta aguje a daidai lokacin da Waleed ya shigo hannunsa d'auke da kayan rabon da zasuyi a kamu.
Zubar da kayan hannunsa yayi yayo wajenmu agujen ya Tayani tallafar zahira dan Nima jikina rawa yake d'aukar ta yayi cak yayi daki da ita.
Ni Kuma na cewa yayar kabiru "Ba komai Allah yasa Hakan shiya fi alheri kila da ma Zahira ba matarsa bace shiyasa ya janye"
Chapter 55 · 0% Book details