← Book details Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 62

Sashe 54

Naga Ta Kaina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar iskar da take San Zahira ta zama sai gashi Safiyya ce ta Zama a gaban idonta zaa Zo a d'auketa a dawo da ita washegari ko sisinta ba Kuma zata bata ba daga ita har Bashir Basu d'auketa a matsayin uwa ba ubanta kawai suke ci.

Abu goma da ashirin haka suka hade mata duk lokacin data duba yaranta ta ga halin da suke ciki zuciyarta kamar ta buga sabida bakin ciki ga mugu mugun tsanar da ta yiwa Naeema da iyalanta gabadaya rashin nutsuwa yasa ta kasa komawa wajen Oban da ayi Mata mugun aikin da zai Saka Naeema ta mutu Tama bar Mata duniyar duk da tana ganin ko Naeema ta mutun hakan bazai sa taji sanyi a zuciyarta ba sabida tsabar tsanar da ta mata.

Tana sane da Hajara bata taba tunanin waiwaiyar ta ba Dan gani take itama tana cikin wayanda Suka jawo mata Kara lalacewar Bashir.

Haka Safiyya ta kasance cikin tashin Haukacewar Asmau da ta lura har ciki ne da ita.

Wajen Oban ta koma ta cigaba da rokonsa ya Mata aiki Asmau ta dawo daidai shi kuwa Oban ya ringa kwasar rabonsa a jikinta Yana saka ta Nemo kudi ta kawo masa akan Kar ta damu Yana aiki akan Asmau zata samu lafiya.

Haka tayi ta saka Rai da samun lafiya Asmau da ke haukanta tuburan da ciki har ta haifi yarta mace a cikin halin hauka.

Safiyya tana ji tana gani tayi jika shegiya da Bata San ubanta ba haka ta hau rainon jaririyar cikin bakin cikin duk halin da ta tsinci Kan ta a ciki da take ganin duk Naeema ce ta jaza Mata.

Wanan kenan

Hajara

Rayuwa ba karamin wahala ya Mata ba dan ciwon kafar da take yasa dan kosai da take soyawa ta daina iya fita soyawa dan canji Kan da take dashi haka duk ya kare a hannunta haka ma kudin hayan gidan da ta Kama

Tana ji tana gani aka koreta daga gidan.

A ranar da aka koreta da Jan kafa ta nufi gidan Safiyya dan bata da Inda zata je daya wuce wajen

Sai dai da isarta Safiyya ta rufe idonta ta koreta akan bazata zauna Mata a gida ba itama ta kanta take abinci itama sai tayi da gaske take sa mu taci taje wajen Naseeru da ta zabeshi da sabida Kar ta Masa komai ta gwammace ta fasa mudubi danta Bashir ya Kara zama katon barawo.

Hajara kuwa bakin cikin abinda Safiyya ta Mata yasa ta ringa tsinewa Safiyya tana jawo Mata iftilai rayuwa

Zagi in zaga Haka sukayi kamar ba uwa da 'ya ba

Hajara na kuka ta baro gidan Safiyya ta hau laluman Inda zata zauna dan Bata Isa ta soma tafiya Kano wajen Naseer ko Tijjani ba Safiyya ta Riga da ta cutar da ita intaje Kano ma kila Yan sanda su Kamata

Yau da ba dan Naeema ba da rayuwata duk bata juya haka har wajen Zama ya gagareta ba.

Haka ta ga ma kewaye unguwar Bata samu waje ba kamar tsinuwa duk Inda taje sai an koreta

Sai a wani rumfa da Rabinsu mahaukata ne anan ta samu wajen kwana

Anan Kuma ta mayar dashi gidanta

K'arfin hali irin nata yasa ta hau bara tana neman kudin da zata ga bayan Safiyya da Naeema.

Dan tsana take Mata da take Jin wani Abu ya tokare Mata kirji har sai ta samu cikar burinta zata samu sausauci a zuciyarta

Wanan kenan.

Naeema

Tunda Inna Amina ta min fada na watsar da komai na maida lamurana wajen Allah nayi k'ok'arin rungumar duk jarrabtar da Allah ya min da hannu biyu addua Shiriya kawai nake yiwa Waleed da Zahira.

Inna Amina na Tayani

Dauriya kawai nake da muka tafi shekara biyu Naseer bai neme mu ba Ina tsoron ko wani abune ya same shi sai dana dawo hankalina na fara tunanin duk halayyen da ya ringa nuna min ba halinsa bane kila shima tab'a shin akayi.

Addu'a nake akan Allah ya kareshi ya sa ya dawo hankalinsa ya dawo ko dan Nadeeya da yanzu ta fara jamia maneman Aurenta na ta zuwa ko ta Ina neman aurenta.

Burina yanzu ko Humaira ce ta samu miji aurar da ita zanyi.

Zahira da waleed Kam addua kawai Zan cigaba da tayasu dashi akan Allah ya shirya min su duk da bana San yaudarar kaina sai nake ganin kamar sun fara dan canjawa tunda Waleed na dan zama a gida yanzu inya ga dama har ya kwana.

Zahira ma ta fi bani mamaki dan tana zama yanzu a gida sai idan an b'ata Mata Rai take fita.

A yau da yamma muna zaune gabad'ayan mu atsakar gida har da Inna Amina dasu Nadeeya suka tilasta mata fitowa tsakar gida.

Suna ta tsokanar ta itama tana tsokanarsu.

A rayuwata ba abinda ke Sakani farinciki sama Dana ga yarana gabadaya a waje daya suna hira ko ban sa musu baki ba Ina Jin dadi a Raina.

A hankali na ringa binsu da kallo dukaninsu sun girma sun Zama Yan Mata Masha Allah har Raheema dake da shekara goma Sha shidda.

Abinda ya ragemin Jin dadi Bai wuce halin da yarana biyu suka tsinci kansu a ciki ba.

Ko yanzu ma Zahira bata nan haka ma Waleed

Ina zaune ne kawai amma zuciyata na wajensu.

Shigowar Waleed da Sallama kasa kasa yasa na amsa da Sauri Ina lalubar kwayar idonsa

Ina ganin canji sosai a tare dashi tunda aka juya Masa Kai bai tab'a shigowa gidan da sallama ba sai gashi kwana biyu na lura Yana shigowa da sallamar duk da kasa kasa yake sallamar.

Girman jikin da yake dashi da kwarjini yasa k'arfi da yaji yayayensa suka koma shakkarsa idan ka ganshi zaka iya tunanin ya girmesu

Sabida naseeha Dana wa yayyensa yasa suke hakuri da duk wani rashin kunyar da yake musu.

Kitchen ya Shiga ya d'auko abincinsa har zai Shiga d'aki Inna Amina ta Kira shi akan yazo gefenta ya zauna.

Gefenta ya zauna ya fara cin abincin kallona da Inna Amina tayi yasa na mik'e na Shiga d'akinta na dauko ruwan Addu'ar Waleed da Zahira na tsiyaya a Kofi na Kai Mata ta mik'awa Waleed ya karba.

Jansa Inna Amina ta fara yi da hira

Sai gashi Waleed ya saki jiki Yana hirar shima alhamdulillah Ina ganin canji sosai a wajen yarana.

Kamar Dani yake hiran haka na zuba Masa Ido Inna Amina na Masa naseeha cikin siga har tana idan ya gama cin abinci yaje yayi sallah

Yana kuwa gama ci yaje yayi alwala.

Ya Shiga d'aki da zumar yin sallah Dan tsakar gidan namu karami ne sosai.

Sallamar da akayi tare da shigowa yasa dukan mu muka kalli bakin kofa.

Yarana Suka saki ihun murna sukayi wajen Naseer dana kasa d'auke idona akansa.

Shima hadesu yayi ya rungumesu.

Kwalla ya cikamin Ido Dana ga yanda ya rame har furfura ne suka firfito Masa

Inna Amina kuwa tsabar murna tafi ta ringayi daga zaune tana Masa oyoyo.

Dak'yar ya bambare su Nadeeya daga jikinsa

Ya nufo wajen da muke Zaune yana zuwa ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau gaisheta.

Cikin murna ta ruko hannunsa ta hau amsawa tana had'awa da Masa tambayar Mai yasa ya Dade haka Bai waiwayo mu ba a matsayinsa na da namiji ai hakuri ya Kamata yayi bai Kamata yayi fushi ba.

Fada da naseeha Inna Amina ta Masa ta had'a da bashi hakurin Abunda na Masa akan yamin uzuri idona ne ya rufe akan su Zahira shiyasa na Masa haka

Murmushi yayi yana "Ba komai Mama wlh ban riketa a raina ba korar da tamin daga gidanta yasa Nima na samu Allah ya dafamin na nemi kudin da Nima na siyi filin nayi gini naje wancan tsohon gidan nata anan nake Jin labarin Kun tashi dak'yar na gane Kuna nan nima nasan Ina da laifi da Abubuwan da na ringayi a baya da Nima sai daga baya nagane ban kyauta ba sai dai na baku hakuri Allah ya kiyaye gaba"

Sai a lokacin muka hada Ido dashi ya dan sakarmin murmushi Nima na sakar masa.

Nadeeya ya kala Yana "Inna Zahira"?

Nadeeya na k'ok'arin Magana Waleed ya fito daga d'akin.

Na zubawa Naseer Ido naga ya zaiyi idan ya ga Waleed zai Masa wanan kallon tsanar daya Saba Masa

Kallon kallo sukewa juna da yasa na kasa karantar kallon da Naseer ke yiwa Waleed har Waleed ya d'auke kansa yayi waje ba tare da ya gaishe shi ba

Inna Amina da Sauri ta hau Masa bayanin halin da Waleed da Zahira ke ciki har yanzu da muke ta addua Allah ya shirya su.

Girgiza Kai yayi Yana insha Allahu shima Yana addua Akan Allah ya warware abinda aka musu

Daga haka ya cewa Nadeeya ta fita ta nemo masa Zahira

A Dan karantar da na Masa sai Naga kamar har lokacin ba soyayar Waleed a Ransa

(Duk da asirin da aka musu na karyewa har gobe Da nake rubuta wanan labarin wani zubin idan abin ya motsa Naseer da Waleed basa Zama inuwa daya bi maana Babu wanan soyayya d'a da uba Mai k'arfi a tsakaninsu)

Nadeeya ya tasa a gaba suka je neman Zahira gidan kawayenta da wasu mun San gidansu wasu bamu sani ba da suka Taki saa gidan kawarta da muka sani anan suka same ta.

Naseer ya taso ta gaba suka dawo gida.

A Palo ya zaunar da ita ya hau Mata naseeha

Inda ni Kuma jikina yayi balain sanyi da na ga kamar da Zahira kawai ya damu Banda Waleed.

A ranar nayi kukan da na dade ban yi ba dan duk da a gidan ya kwana ya Kuma bani labarin Dana koresa daga gidan bai koma Abuja ba motarsa ya siyar ya hada da kudaden daya samo ya siyi fili Rabin filoti a gyadi gyadi ya hau gini ta hanyar neman kudi Yana buga buga har Sana'ar hannu sai daya koya dan kawai ya samu kudin da zai gina gidansa.

Ko abinci baya iya sawa cikinsa sosai sabida kawai ya samu kudin gini Addu'ar da ya dage dashi yasa ya dawo hayyacinsa.

Yana Kuma Kai karar mahaifiyarsa wajen Allah Dan ta cutar dashi.
Chapter 54 · 0% Book details