← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinci zaka fara ci ko sallah zaka fara yi ne?dan kar tayi sallah tace cin abinci ne gaba da sallah, Na'im ya ganeta tsab sai ya hada mata Tea me kauri da Farfesun naman rago sai Friedrice a gefe,da yaya zanci? bayan ka karya min hannun damana,Harara ya balla mata yana tsaki ya matsa da kujerarsa gefe yace ha bakin,ta bude Hakoranta ne suka tafi da imaninsa,sharewa yayi ya shiga bata tana kallonsa tana ta faman murmushi,shi kuwa ya hade rai sai harara da take Sha,har ya gama bata,tace Amai take ji taje toilet ta Kwara Amai sosai ta dawo ta fada saman bed,yace tashi kana yin Sallah mana(tashi kiyi Sallah mana)
Sai da taja tsaki ta Mike ya sa mata hijab maimakon tayi sallah sai ta wani kwanta a jikinsa suna a tsaye kamar zatayi kuka idonta jajir, saman Sallaya ya hankadata rai a bace yana mata warning ta daina taba masa jiki,
Tayar da sallah tayi harda fashewa da kukan bakin ciki ance sai tayi sallah kuma tsoron Na'im takeyi baza ta iya cewa a'a ba.

Barin Room din Na'im yayi kamar gaske Ashe kuwa kamar ya sani ya labe a jikin kofar room din sai yaga Salma ta waiga tana ganin baya nan ta fasa sallar tayi zamanta a sallaya kawai,baram taji an bude kofa,ta tashi zumbur ta kara tayar da Iqama,ya sake fita ya labe,tana ganin haka ta koma tayi zamanta,ya kara fadowa dakin sai kawai tayi masa kamar tana zaman Tahiya,fita ya kara yi again sai ma ya ganta ta koma saman Bed tayi kwanciyarta,ya bude kofa ya shugo cike bacin rai yace sakko to kiyi sallar a gabana ina gani,shi yasa Aljanu suke shiga naku suji dadin Zama bakwa sallah bare ayi sauran Azkhar dole su samu wajen Zama,ba wani Aljanu dama can bakwa son yin addini,gaskiyar Na'im domin zamanin nan zaka ga yan mata labta labta basa son yin sallah da sauran addini,sallah bata damesu ba,da Aljanu sun shiga sai su kara abin yafi Nada dama can halin mutum ne ya kara karuwa,yan mata da matan aure basa sallah da yawa,ko baza ayi kan lokaci ba sai an gama duk wani girki da ayyuka anyi wanka sai azo ayi ta jero salloli,ba dole ayi ta aikata muna nan sabo ba,ba sallah bare karatun Qurani da su azkhar etc,damuwa tayiwa mutum yawa baiyi ibada na farilla ba ina ga nafeela har ya roki Allah bukata,
Dole masu bin maza suyi yawa ba a sallah da addua bare Allah ya kareka,lesbian,Romancing da maza barkatai,shaye shaye gasu nan dai da yawa,A koma abi Allah ayi addua da tsayar da Sallah,azkhar etc zaku ga yanda Allah zai na kare mutum amma kullum sai Jin kida da kallon films,chating,karatun Novels etc duniya kawai aka sa a gaba dole mu aikata laifuka ba adadi.

A gabansa Salma tayi Sallah ta idar,tana idarwa Aljanunta na tashi ta fara yage yage da bige bige,tana Farawa Na'im ma nashi suka tashi ya fara kalar nasa wanda ba a San yana da su ba,Na'im ya damki Salma itama haka suka dinga cin uban juna suna ta kokawa ba wanda yafi karfin wani,karayar Salma ta kara karyewa baras sai an gyara amma bata sani ba,
Na'im yaji ciwo a kafarsa fata duk ta yayyage,malaman Hospital suka taho da gudu akayi musu Allurai bacci amma suka ki yin bacci duk karfinta bata sasu bacci ba, kamar wasa suna ta aljanun
Suna ciwa junansu mutunci,Salma tace Kai kamar na kunkuru,Na'im yake baki kamar na tsuntsu, Idonka kamar na kunama,Naim yace kanki kamar takalmi,saina yankaki,saina fede ma ciki, mutanen asibiti dake dakin dariya ma abin ya basu dama idan mutum na Aljanu sai aga kamar yana sani yakeyi karyace kawai kuma da gaske ne.

Wani malamin Doctor ne a Hospital din yazo da Qur'ani ya musu ruqiyya duk da cewa Aljanun basuyi magana ba guduwa kawai sukayi amma sunji sauki nan suka kwanta ko wanne a bed dinsa suna ta bacci basu farka ba sai da gari yayi haske tangararan.tun jiya da dare an kara dora Salma Living things tana bacci,haka shima Doctor me Imani anyi masa Treatment na rauninsa.washe gari da suka farka babu wanda yasan yayi komai sai Raunin da suka gani,Na'im yana yin Sallah ya bar asibitin ya tafi gida,ita kuma brush kawai tayi ta hau gado ba sallah ba komai tayi kwanciyarta tana tunanin Ina Raheel ya tafi karfa ya gudu ya barta da ciki,

Yunwa ce ta addabeta tana ta faman tunani to wai wannan idan ba Raheel bane waye?kamshinsu da kayan da yake sawa duk iri daya dana Raheel,kamarsu daya da Raheel komai nasu ba banbancin
, ta dauki lokaci me tsawo har Mummy,Dada,Aisha,Hunaif,da Irfan suka shugo suka taddata ras da ita,Mummy da murmushi tace sannu ya jiki,ita dai Salma kuka takeyi Raheel ya tafi ya barta nufinta Na'im ne Raheel ya tafi kuma,
Irfan duk sun mata sannu sun dauka zafin ciwo ne yasa take hawaye,Irfan yace wa ya miki wanka?tana shesheka tace Ni...ni...ce nayiwa ...kaina da hannu daya,Kaya wa yasa miki?tace Raheel mugu ne ya sa min,Kallon kallo sukayi Mummy tace dan Ubansa ga nurses ba zai kira su sa miki ba sai shi Allah ya shirya,

Ita dai Kukanta takeyi ta kalli Dada tace dan Allah Iyya ba Raheel bane wannan din nan? Dada tayi murmushi tace ba shi bane wannan Na'im ne jikata,ba wani ke dai kice kin kare Jikanki cewar Salma.

Abinci Aisha ta mika mata,Salma ta kalleta kurrrr tace ni bana cin abincin yar shaye shaye,wlh Mummy ki mata fada kwayoyi da syrup take Sha,dazu ma da sassafe da Codein ta karya ko ba haka akayi ba?kuma kina neman mata yan uwanki jiya ma kunyiwa juna kiss da wata.
Aisha kunya ta kamata tayi miki miki tabbas gaskiya Salma ke fadi ko Aljana ce ne?

Mummy ta Kalli Aisha tace kinji kunya dama baki daina halinki ba?Dada ta fashe da kuka Wlh baza su koma turai ba zuri'ata da shaye shaye wannan mutanen boye ne da ita gaskiya ta fada.

Irfan a dole na kirki ya fara cin uban Aisha, Salma ta kalleshi tana Kukanta tace hmmm kai har kana da bakin magana?abinda jiya jiya a Sheraton Hotel ka kwana da wata,Mummy ko ya kwana a gida jiya?
Mummy karya ya miki yace yana da meeting a Kaduna a hotel ya kwana da Arniya Amy wogu sunanta, Irfan yayi mukus ya tabbatar Salma Aljana ce tasan komai,nan Mummy taci Ubansa son ranta,Hunaif ya sheke da dariya,Salma ta Galla masa Harara tace kai fa jiya har wiwi kasha kaje club kaida frnds naka kuka dinga Romancing yaran mutane.

Na'im a kunnensa komai ya faru yazo shigowa Room din kenan yaji Tonon sililin da Salma keyi,haka ya daure ya shigo ta daga kai ta kalleshi Salma ta saki murmushi dimple dinta ya loba me kyau tace wannan Mummy da kike ganinsa duk kalar giya ba wacce baya Sha,yanzu ma ya jefar da kwalabar da ya shanye wata yana Dustbin na jikin dakin nan,aje a duba idan karya nake Allah ya tsine min na zama Barewa a daji.
Mummy ta fashe da kuka yanzu duk yaranta ba wani na gari ciki,da kyar Dada ta lallasheta,Na'im yaji haushin Salma yace ke kuma wanne laifi kike aikatawa? Tace yo ni me nake yi ai ni ta gari ce, in banda Sallah dana ke dan kin yi amma ai gwara ni Sallah ce kawai Ku fa?giya fa giya fa,neman mata ga shaye shaye da chasu tirrr daku.
Ai ke kinfi kowa ma lalacewa tunda Sallah ce guda bakyayi duk wanda baya sallah baya musulunci,duk aikinki a banza ba a karba tunda bakya sallah wawiya, baki ta murgudawa Na'im tace kaine kake ba da Ladan? Kuma na fika dai wooooo tayi masa gwalo.

Mummy tayi ta salati tace yo ke yar nan ai kece me babban laifi ma ai kuwa kiyi gaggawar tsaida Sallah,
Abinci Mummy ta mika mata amma taki ci akayi akayi taci taki kuma Allura ake so ayi mata,Na'im kayi shuru kasa baki taci mana mu Kebbi zamu wuce Allah kara lfy sai jibi zamu dawo ka kula da ita dan Allah kaji abinda nace ko Na'im karka yarda ka saba min a bayan Idona kan wannan yarinya na fada ma,to Mummy Allah kaiku lfy,suka fita Driver ya jasu sai Airport.

Tsawa Na'im ya bugawa Salma ci mana ban son Hauka,ba shiri ta fara ci,da sauri zakici da yawa kuma haka yanda yace takeyi,Rankwashi ya zuba mata a kai kin jawo min masifa,mayya wlh na kara ji kina cewa Mummy munyi Bad something sai na karyaki again,Dariya Salma tayi tace Fada kyau yake ma Raheel mugu kalli dan lips dinka ta kai yatsa zata shafo da yatsanta ya make hannu,zafi ya ratsata sosai sai da tayi hawaye tace haba Raheel Haba Raheel dan kaga ina sonka? Kaine fa ka samin sonka ka dinga zuwa zance wajena,cikinka ne a jikina,kaine fa ka bani ajiyar cikin nan dana ke Shan wahala dashi,kasan me nake ji a jikina?kasan irin ciwon da nake yi?kasan irin yanda na rabu da masu riko na?dangina basa Sona basu da zumunci iyayena kafi kowa Sanin sun rasu ban san kalar Uwata ba ban san Ubana ba,haka sabo da kai ka rabani da masu rikona na gaskiya Affa da Ummitu na,Yan gari da yan Uwa duka zagina sukeyi suna ce min karuwa,bani da sauran mutunci.
Chapter 8 · 0% Book details