← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 80

Sashe 72

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fitowa yana murmushi Salma da wuri ta karasa tare da goge masa jikinsa ta shafa masa mai tana masa hira me dadi cike da kalaman so,fes ta shiryashi cikin kana nan kaya yaci Uban kyau na ban mamaki,tana yi tana duba time ta daukar masa komai da zaije dasu Hospital tare da Jan hannunsa zuwa dining ta bude abinci iri iri sai kamshi suke,Na'im ya kalleta tare da daga mata babban yatsa kin hadu Sweetheart ta ko ina thts y I always love u,kin San me ya kamata,Salma tana murmushin jin dadi ana yabonta ta kara kasa da murya tana zuba masa Abinci tace honey Bana so ka makara fa kalli time kace 10am kake so kaga patients duba 10am ta kusa,Kallonta yake ta faman yi yanda ta birgeshi tayi kyau komai nata me kyau ne,ga iya wanka,ido suka hada da sauri ta dauke nata idon,sabo da wasu taurari da take gani a cikin idonsa suna kashe mata jiki tana susucewa ta kasa control na kanta, yace ko dai kin gaji dani ne Sweetheart? Naga sai sauri kike kina murna na bar gidan,murmushi Salma tayi ta dan kalleshi tace taya zanyi murna Honey ban son kayi wasa da aikinka ne amma ai buri na bai wuce mu kasance tare ba,babu yanda zanyi ne shi yasa,hanyar da kake nemo mana ai dole na goya ma baya amma ni in zakaje dani ma zan bika pls.
Murmushi ya saki na birgewa tare da kashe mata Ido daya yace got u Dear.abincin ta shiga bashi itama tana ci har suka gama sannan ta daukar masa wayoyinsa suka fita har inda motocinsa suke kala kala ya zabi wacce zai hau,Salma tace Honey da kanka zakayi Driving? Driver yana waje nace ya tsaya taya zan barshi kin zo rakani ya kalle min ke shi yasa nace ya jirani a waje sai na fitar da motar da kaina mu wuce,alright cewarta, a jikin motar ya rungumeta ya dinga kissing dinta ba adadi da kyar ta kwace sukayi Salma sosai sannan ta koma ciki shi kuma Ya fitar da motar Driver ya karba suka tafi.

Tun a motar basuyi nisa ba ya kira Salma ya kusa karasawa,da yaje ma ya fada mata ta masa addua,ya fara duba patients wani lokacin sai ya kasa sabo da tunanin Salma sai ya kirata a waya yaji Muryarta sannan yaci gaba,haka Salma ma da taji shuru zata nemeshi taji lfy.
2pm Salma ta kira Hello Honey am just missing u kaki dawowa na gaji da jira ni kadai gidan so bored ba dadi,pls ka dawo zanyi kuka,No..no..karki yi kuka kinji zan dawo aiki ne ya rikeni sai wurin 5pm ba yanda zanyi Operation zanyi kin San aikin Babyna ceton rai kiyi hakuri,ok ba matsala to naje gidan Zainura? a'a ba yau ba sai weekend zamu je tare,kukan shagwaba ta fara masa da kyar ya lallasheta ta hakura,sai jiran Na'im akeyi yazo a shiga Operation yana ta faman lallashin matarsa,har mamaki ya bawa Doctors,Doctor Aliyu kuwa dama ya dauki Hutu bazai je aiki ba sai yayi 3wks.

Irfan ma yau 6days da aurensu da Zeena,Zainura dama ita ba Ganda ga saurin aiki,nan taje ta shiryashi tayi komai ya fita Office,abin haushin Irfan baya hasala komai sai chat da Zainuransa yana ta dariya shi kadai,daya gaji ma fitowa yayi tare da barin building din ya shiga mota ya koma gida,1:30pm ya tsaya a masallaci tare da Gabatar da Sallah ya shiga gida,tana jin karar danna password dama tasan da zuwansa cikin wata gown take iya rabin cinya tayi mugun kyau kamar a saceta,da murna ta rungume abinta lips dinsa ta kalla wanda suke zautar da ita ta shagala tana kallonsu,a hankali ya matso da fuskarsa hancinsu na Gogan na juna sabo da Zainura ma akwai hanci me tsini da kyau,kamar zai cinye mata lips haka ya shiga tsotsarsu,Zeena yanzu expert ce a nan bangaren hannayenta biyu tasa tare da sakalo wuyansa tana nutsa yatsunta cikin sumarsa,sun dauki lokaci me tsawo a haka sannan ya zare bakinsa a nata suna maida numfashi kamar wanda sukayi dambe,Zainura bata koshi ba tasa hannu wai dan Iskancin Zainura ma kunnensa biyu ta ruko tana da matso da fuskarsa saitin tasa yana dariya wannan wani new style kika samo ban san dashi ba?Itama dariya tayi sannan tace kunnenka nake tsoro kar ya tsinke sabo da dadi shi yasa na rikesu sai lokacin ta saki kunnuwan ta tallafi kumatunsa da hannun biyu ta kara hade bakinsu wannan lokacin ita take masa salonta iri iri,a hankali tayi masa magana a kunne tare da zura harshenta ciki nan take Irfan ya zauce ya dauketa sai bedroom tun kafin su karasa bedroom din sukayi watsi da kayan jikinsu,da Zafi zafi cikin Zumudin juna suka fara kashe Kansu da kauna tare da shauki.
Hunaif kuwa suna shopping tare da Afrah dinsa,Afrah bata saba da wahala ba komai sai dai ayi mata,girkin ma kadan takeyi sai taga dama,sam Hunaif kuma shi ba haka yake so ba yafi so ace matarsa bata da kyuya,ta dinga dafa masa Abinci,Afrah bata da wata matsala in banda ta kyuya komai sai dai dan aiki yayi sabo da haka ta taso,Hunaif kam yace dole ta Mike shi bai son haka,har fada sukeyi watarana kan hakan,tunani yake wa zai iya gyara masa Afrah,Salma bata cika shiga sabgar wani ba,Zainura itace zata iya,nan Hunaif yace dole zai sa Zainura kullum ta dinga zuwa gidansa idan Irfan baya nan ta gyarawa Afrah Zama,yasan ba sai ya fadawa Zainura matsalar ba tana gani Afrah ta shiga uku da ita.

Aisha ta Kamu Da son Doctor Aliyu gaba daya,dama Na'im ya fada masa kar ya sake ya bar Afrah da frnds,kar ya bari suzo masa gida kuma kar ya barta taje,Aliyu haka ya saka mata mugun tsaro,sai yanzu take ganin Ashe da hauka takeyi tana Kula mata suna lez Ashe duk bata lokacine da dabbanci takeyi,yanzu Istigifari take sosai tana farantawa mijinta bata fita ko ina,ko gidan su Zainura da wajen Mummy da tace zata je,Aliyu ya Sanarwa Na'im,Na'im yace kar ya barta ta fita ko ina yanzu sai nan da watanni shidda,shi dai Aliyu bai San me Aisha ta aikata ba,yasan dai tana kule kulen kawaye da yawo amma su Na'im sun rufawa yar uwarsu asiri basu bari kowa yaji sirrinsu ba balle ace watarana miji a samu matsala ya mata gori ko wani abu,shi dai Aliyu tunaninsa duk sabo da Aisha macece shi yasa suke bata kulawa,yanda Aliyu yake kaunar Aisha ko a gidan karuwai ya ganta ya rantse shi sai ya aureta ba ruwansa da wani Aisha sai ta Zama Virgin ko tayi kaza haka Allah yasa masa Sonta badan wani abu ba.

Ummitu ana karbar wahala sai abinda yaci gaba,A wannan lokaci Affa idan ka ganshi baza ka ganeshi ba,ya fita daga hayyacinsa,wannan ciwon har karamar hauka ya sashi,domin surutai yake barkatai marasa kan gado,Masa'udu dan Uwansa yace ya gaji su tafi gidansu su zauna zasu dinga aiko musu da abinci,Ummitu tasan korarsu kawai yayi amma ba yanda suka iya haka suka tattara suka koma gidansu,Ummitu ita ke zuwa gona ta samo itacen da zasu danyi girki,yanzu sana'ar sirfe da daka takeyi a kauyen suna samun na Koko da kosai,Affa ana daki ba fita ba shiga komai sai dai ayi masa,Ummitu tana cin bakar wahala tayi kuka har ta gode Allah,kullum idonta jangame da hawaye basa tsayawa,sai suyi sati basu daura tukunya ba,sai dai gidan me gari ko yayarta su aiko musu da abinci sabo da tausayi,Masa'udu kuwa yana fadawa Harira ta kai musu abinci amma sai tace ta kai kuma karya take,Ummitu da Affa suna ganin rayuwa sai yanzu suka San cewar Lokacin da Salma take gidan suna ganin suna talauci basa godewa Allah Ashe cikin wadata suke basu sani ba,sai yanzu suka San Talauci,da ace ma Affa da lfy da sauki,ina ma Affa zai samu Lfy ko da talaucin su Zauna sun godewa Allah.
Affa yana daga daki haukar tasa ta motsa magana yakewa Ummitu Yaushe Alhaji Zakari ya mutu? Ummitu tace tun yaushe Zakari ya rasu ai yafi shekara ashirin da mutuwa,da kai fa akayi komai na zaman makoki amma yanzu ka tambaya?Affa yace yanzu Zakari ya mutu ba a gaya min ba sai ya fara kuka sosai,wata tazo ta kawo dakan gero ta tafi,Affa yace wacce doguwar matace ta wuce min daki? Ummitu da mamaki ta kalleshi tace Hajiyayye ce fa makwaftanmu,kuma ba daki ta shiga ba fita waje tayi gidansu, wace Hajiyayye ban Santa ba? Affa ya tambaya.
Yace Ummitu ta fito dashi waje zai sha Iska ta fito dashi kuwa yana kwance,yake nuna ledoji yace sai an dauko masa suna bin iska,idan ta dakko yace a wankesu a ajiye idan na mutu sai ku zuba Wainar Sadaka a ciki,Ummitu ya bata tausayi ta fara kuka,ya dawo yace sai ta nemo masa me daukan photo dake kauyen,takanas taje har shagon Buba me hoto ta kirashi da camera,Affa yace ya daukeshi masu kyau sai da aka dauki kala biyu Buba ya tafi,Affa ya kalli Ummitu da kyar ciwo yana cinsa yace wannan Hoton ke na daukarwa shi idan na mutu sai ki kalla,wannan gidan nawa tunda Allah bai bamu haihuwa ba na bar miki shi halak malak,ragowar gonata guda daya duk nakine Ummitu na gode Allah ya miki Albarka kinyi kokari kina ta dawainiya dani,Ummitu kuka take kamar ranta zai fita gani take da gaske ne Affa rasuwa zaiyi sabo da ciwon an kwashi wurin 6mnths har yau yaki warkewa,ba kudin asibiti,shi kanshi Affa wannan lokacin sai da yayi kuka sosai na tausayin Kansu.
Chapter 72 · 0% Book details