← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 80

Sashe 62

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha da Doctor Aliyu bata wani sonsa amma ba yanda zatayi haka ta hakura tayi biyayya ga yayyenta,abinda suka yanke dole zata bi sabo da sune kamar Abbansu tunda bashi da rai,a yanzu zamanin nan waye yaya ko wasu yan Uwa kowa abinda yaga dama yakeyi,ba biyayya iyayen ma bare yan Uwa yayye,wasu kannenma za kaji suna zagin yayyensu face to face ba tarbiya.
Na'im ya kai Malam bangaren Business dinsa na noma yana aiki a nan tunda dama shi bashi da karatun boko sai Arabic sai noma,shi yasa ya dorashi akan abinda Malam ya sani kuma yana aiki yanda ya kamata,
Rahina da mijinta ma Abubakar suna Abuja duniya sabuwa Na'im ya gama musu komai,sai waya da sukeyi suna jira bikin Irfan yazo suzo ayi dasu,haka ma Su Barira kawayen su Zainura jira suke biki ya matso su taho bikin kawarsu,
Aikin da Na'im ya bada Kwangila ayi a kauyen an gama komai da komai,da kansa yake shi kadai Da chairman na Lg din suka bude wuraren akayi addua sannan aka yiwa mutane bayani aiki zai fara ranar Monday.

Zainura Amarya ko Zance bata damu su zauna suyi da Irfan ba daga makaranta sai gyaran jiki,sai dai dole idan watarana yaje dauko ta tofa shine za ayi hira,gaba daya ta gama sanarwa yan schl za ayi bikinta har yanga take zata yi aure,Irfan ya kirata tazo garden sai da ta dauki dogon lokaci tana tsantsara wanka ta cakare kamar zataje Dinner sannan ta tafi wajensa,tana yanga ta karasa gabansa tare da Sallama ta zauna saman kujera kusa dashi,Irfan sai kallonta yake kamar maye,Zainura taji kunya har wasa take da yatsunta,kin San me?taji muryarsa me dadin saurare da sanyi sai ka fada,ki daina min shuru shuru nan Bana so yanda na ganki naji ina Sonki to hakan nake Sonki shi yasa har zan aureki,Yanda kike Zainuranki ta asali me surutu da abin dariya haka nake Sonki ni duk wannan yanga,jan aji,basa birgeni ga mace,indai zaki min abinda nake so ki min biyayya,da tsafta iya kwalliya,shike nan wannan shuru shuru din naki ki dauki abinki kiyi shi a waje ni kuma tsakaninmu ya Zama normal yanda kike da,
Da yawa maza wasu ba son yangar nan ta mata tayi yawa ko mace tayi ta faman masa iyayi wasu ma mazan haushi suke ji wlh ba birgesu take ba kuma basa Jin dadin Zama dasu,komai baza a fada ba,ba wasa ba dariya sai kayan iyayi wai Jan aji ne to dai maza da yawa ba a birgesu ta nan,amma ace kuna tare tsakaninka da miji kullum cikin nishadi ana Jin dadi,amma wasu sai suyi duf suna cika suna batsewa ana magana da kyar wai shine Jan aji ta ya zaiji dadin Zama dake,ke kullum sai serious abu ba wasa ba dariya,yana da kyau ki dinga sashi nishadi ba lallai ace sai ta hanyar kwanciya ba,ko a gida kullum gidansa a nishadi ake ko da za ayi yangar ai ba kullum ba,amma su wasu Sam mutanenmu basu gane yanga,iyayi,da jan aji ba,kuma wai abin haushi kullum a haka suke a gidan ba canji,wasu ma gani za kayi sun dauki waya suna chat mijin shima ya juya baya can yana danne danne ba wanda ke magana,kowa Danna waya yake abinsa,itama tana can tana chat ta hade rai,tana ta faman yanga da kyar take masa magana kamar yar sarki,ga karyar iyaye,wai matanmu yanzu karya har miji ake yiwa,ta siyi kaya da kanta tace iyayenta suka kawo,ta siyi abu tace yar uwarta ko Kanwarta ta kawo mata,a gidansu basa cin kaza kaza suke ci,babansu kaza yake dinka musu,basa sa atamfa yar kaza karya iri iri,kuma wlh mazan suna ganewa kawai sharewa sukeyi,to ci gaba kikayi ko baya me karyar zata miki?miji yasan ke makaryaciya ce ai ba sauran daraja.
Ya kamata mata mu hausawa mu gyara zamantakewa wlh ba a iya komai ba,kowa abinda yaga dama yake har mazan,ba a tunanin wasu ka'idoji da dokoki da Allah ya daurawa masu zaman aure a'a kawai abinda naga dama ko taga dama ko yaga dama shi zaiyi .

Zainura tace ni fa ba yanga nake ba kawai kwana biyu ne Bana Jin magana amma ai kasan dai inayi jiya ma ai ka dakko ni a schl kuma ai munyi hirarmu ko,ae na sani nafi so kullum na dinga ganinki haka,Zainura tayi dariya tace to insha'allah zanyi,yanzu me kike so za kiyi?na baki kudi? Zainura tace ni bana son kudi fa ka daina yi min zancen kudi idan ina so zan fada ma,lefen kin gani sunyi?ko akwai abinda za a canja? Kayan sunyi yawa ma fa akwati set sunfi 12 har yanzu ban gama kallonsu ba,da baka da kudi sai nace ka rage ka siya mana kayan abinci amma tunda me kudi ne ba ruwana.
Mata da yawa suna shawarar kayan lefe da saurayi amma basa shawara ta kayan abinci,sai kaga mace tasan mijin da zata aura bashi da wani karfi wai sai ta bashi common body cream din da zai zuba a lefen sai ta bada me tsadar wasu Dubu Hamsim guda daya,wani ashirin,sha biyar,wanda za ace ma sanata ko dan majalisa ne zai iya yi miki wannan,ba ruwanta da me zasu ci nan gaba,maimakon suyi shawara ayi komai na hankali sai kawai ta barshi a gama biki ba abincin shekara daya ko biyu,sai ya dogara da gara da iyayenta suka kawo,gara tana karewa zuciyarsa ta mutu an kashe masa zuciya sai ki ga ko yana da halin yana kasa siyen abinda take son taci,ko kuma iyayen nata basuyi mata gara me yawa ba,ko ma basuyi fa wuri ba,shi kuma kudinsa ya kare kat,sai kika sai katon gida da sutura store ba komai a ciki sai dan mitsitsin buhun shinkafa irin dan karami,sai dan gishiri komai sai dai a dinga dan cefano kadan,Yar taliya guda uku a gefe,doya uku a jingine,sai ta fito tana taku dai dai cikin sutura gidan ba abinci,me kenan to ya kamata a dinga Zama ana fahimtar juna,wasu kuma mazan idan ba a lefen ba ba ta inda za a moresu,sai a fahimci halin mutum ayi shawara mai bullewa sai a zauna lfy ba tare da an takura mutum ba an shiga hakkinsa ba.

Bayan Sati biyu biki ya rage Saura sati daya kenan,mummy tace baza ayi party ba,Daurin aure kawai za ayi da Walima,da yamma suyi Dj a gida shike nan da dare a kai Amare ba wani party da za ayi ta faman yi.
Su dai Angwaye sunfi so ayi party amma Mummy tace a'a baza a wahalar da kowa ba.saura kwana Uku biki su Barira frnds din Zainura na kauye kaf Malam yasa aka kwasosu za a Sha biki dasu a birni,ko wacce da hakorin makkanta da taje aikin Hajji ta gallako guda,Zainab harda saka guda biyu irin shegiyar nan daya sama daya kasa kuma sun mata kyau abunta ta Zama Hajiya wai,baki yan biki duk Wanda ya gansu sai yayi dariya gaba daya ko wacce da hakorin Makkah kamar masu anko.
Mamakin kyan gidan su Irfan suke kamar ba a duniya ba,Zaunura ta karbesu hannu biyu ita da Salma,dakin Zainura suka sauka wai su nan zasu zauna har a gama biki,Hunaif da Irfan tare da Salma yanzu dakin Zainura ya Zama majalisa nan suke haduwa dasu Jamila aci dariya har a gaji suna nishadi,su Hunaif susha labarin dariya kamar me,idan kaga Na'im a ciki to Salma yazo nema kawai baya bata lokacinsa.

Sunyi Sallar Isha sunci abinci Saura kwana biyu biki,Zainura duk ta karbo musu dinkinsu ko wacce kala Uku masu kyau,Atamfa,lace da shadda,sai murna suke zasu sa kaya me kyau dinkin yan Birni.
Yan Uwan su Hunaif ma da Amaryarsa Afrah duk sunzo Larabawa part dinsu daban suma gida ya cika da yan biki kowa da bangarensu,Zainab da su Barira duk suna kwance saman bed suna ta zuba surutu,Zainura ta shigo taci uban takalmi me tsini wai zasu fita da Irfan,Barira tace ke Zainura Wallahi kema kin Zama yar gayu har kinfi ma yan birni,Zainab tace ai wanka sai Salma mayyar kamar a jikinta aka kirkireshi,Jamila tayi shewa heeeee Zainura dadi miji tun ba a daura ba ya fara daukanki yawo ai dole ya dan eh...hhhh suka sheke da Dariya,Jamila tace to nima Alhmdllh sanda muka je kano Gidan Rahina nayi Saurayi dan Birni sunansa Mahmud kuma yace da gaske yake zai aureni,Zainura tace Na miko murna bari naje Baby yana jirana,Zainab ta bude baki tare da cewa kamar wani jariri dama ana fadawa babban mutum Baby haka sangangan dashi kice wani Baby gaskiya ki canja masa Suna ina laifin ma kice Me gidana ko Yaya,Zainura ta rike baki see ur face Me gida or what so ever u called it an daina yayin wannan sai kauye,ku bari na dawo na baje muku labari,to muna jira,suna haka sai ga Irfan yana Precious let's go kin shanyani,Barira tace wannan Kalmar sai dai mu shiga dictionary Zahra'u kin iya duba kalma ki duba mana ma'anarta,Bari Salma tazo iyayen turanci ta fassara mana,Rahmatu tace nima ina yin Aure zan dinga cewa mijina Babyna yasin sai dai a yankani amma billahillazi sai na fadi hakan,Z Zainab tace yo tun yaushe ma Wanda yayi magana ya raina uwatas ni Darling ma zance masa naga shegen da zai yi magana,ai ina cewa Darling akace nayi Iskanci to Alqur'an ta Salma zanyi Na koma ce masa Honey yasin.
Chapter 62 · 0% Book details