Sashe 75
Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wata daya tsakani suka bar kasar zuwa Saudiya,Na'im da Salma,Irfan,Zainura,Hunaif,Afrah,Aisha tare da mijinta Doctor Aliyu,suna gama aikin Hajji suka suka tafi Lebanon ansha riti,sai USA,daga nan suka dawo Nigeria,Zainura da Irfan sunje kauyen iyayenta kwanansu uku sunsha hira dasu Jamila suka dawo gida,Jamila ta samu miji a birni itama,Haka Zainab cikin Katsina,sai Zahrau Kd,Barira kano kusa da Rahina a nan ta samu miji,duk an sa ranar bikinsu,Rahmatu ma wani dan Uwansu aka bata dake Zaune a cikin dutse Jigawa state counselor ne a can dutse alhmdllh sun samu nutsatsu samari duk da cewa Zahrau ce kawai zata auri wani me mata me kudi dan 40yrs duk sauran masu rufin asiri ne amma samari kuma wayayyu yan Birni.
Bayan wata biyu da dawowar su Salma daga Saudiyya Afrah ma ta samu ciki wata daya,lokacin na Zainura har ya girma ana ganinsa,Itama sai murna kowa ta fara iya hausa yanzu,Salma har tausayin kanta taji,sai tunani take ko bata haihuwa ita Na'im zai iya karo aure wata ta haihu,hankalinta ne ya tashi duk da tana kokarin dannewa tana addua tare da turawa Allah Lamarinta,bata gama tsurewa ba sai da taji cewar Aisha ma ciki ne da ita na wata biyu,Allah sarki Salma ranar sai da tayi kuka a boye na tausayawa kanta.
Gashi sai taga Na'im normal harkar gabansa yake ko a jikinsa,tana so ta masa zancen ko zasu je asibiti amma tana tsoro.
Tana zaune a Palo ita kadai tana tunanin halin da take ciki ita har yau ko bari bata yi ba,katsam sai ga Na'im ya shugo bayansa Ummitu da Malam ne Shar dasu gaba daya babu alamar cewar Affa yayi wata cuta,haka Ummitu babu maganar wahala a jikinsu kamar ma sun Zama yan Birni haka suke,a rude Salma ta Mike harda kukan Dadi,Affa da Ummitu suka zube a kasa tare da fara bada hakuri,Salma da sauri ta katsesu haba Ummitu ashe ma zan bar iyayena na jini su bani hakuri,ai ni ya kamata na baku hakuri,ku zauna dan Allah Affa in ma nice na yafe muku kuma ku yafe min,Ummitu tana kuka tace baki mana komai ba yar nan mu ne da laifi sabo da son zuciya,yanzu mun gane gaskiya,Allah yayiwa mijinki Albarka,kinyi dace Salma,Salma tayi murmushi sannan Ummitu ta bata labarin halin da suka shiga da cutar Affa,Salma harda kukan tausayi,sannan Affa yace mijinki shine silar warkewa ta,muna zaune cikin kunci katsam sai gashi yazo da motoci,yana ganin halin da ya samemu yasa aka kwashe mu har birnin Abuja cikin asibinta sa shine yayi min magani ya kashe makudan kudi na warke,haka bayan na warke ya mai damu gidan kakarsu Dada a nan aka bamu bangare guda,da masu aiki bama komai sutura da komai sai dai mugani ya kawo ko ya aiko dasu,yanzu in kinga jin dadin da muke,kuma Mummy mahaifiyarsu da kowa nasa ya sanni ke kadai ce baki sani ba,har su Zainura da Afrah sun San damu,yace kar a fada miki sai mun murmure munyi kyan gani sabo da idan kin ganmu cikin wahala hankalinki zai tashi.
Ummitu ta kara da ki godewa Allah Salma kinyi miji managarci,ki dage kiyi masa biyayya haka suka dinga Kwara addua suna yiwa Salma nasiha,Salma kam ita bata San ma wacce godiya zata yiwa Na'im ba abin yafi karfinta,suna ta hira dasu Ummitu har dare sannan Driver ya maidasu gidan Dada,Salma tace itama gobe Zara zo musu yini,a bedroom ta iske Na'im yana aiki a system jikinsa ta fada tana ta murna da jin dadi tana masa addua da godiya har sai da yace ta daina ya isa haka,tace ni ban san me ma zan maka dan na faranta maka ba ka gama min komai a duniya,Na'im yace akwai mana kema kin San me nafi so sai ki min,Salma ta rufe ido a kunyace tace Allah yasa kayi min ciki,Na'im ya kalleta tare da cewa yanzu kuma matsalarki kenan?wannan bani nake badawa ba sai ki roka wajen me azurtawa,Salma tace uhm Insha'allah ai amma ka dage,Dariya yake yace taya zan dage?duk wannan abun Baby bai isa ba?Allah ne bai kawo ba zai baki kema naki Bana son kina damun kanki,Salma tayi shuru da ita yanzu kuma ta gama matsalar su Affa ma kawai Haihuwa ce take damunta,Maganar Na'im taji yana mata nasiha da karbar kaddara me kyau ko marar kyau.
Salma dan Adam dole baya Zama babu wata jarabta,wani damuwar mutum ko kashe kansa zaiyi sai sanda Allah ya yaye masa ita,addua kadai ke sawa ana iya canjawa mutum ko rage wahalar ta,ki barwa Allah komai,mutane nawa basa haihuwa da wuri amma mu har yau bamuyi 2yrs bama kin damu kanki,ki godewa Allah da muke da lafiya,Nasiha ya dinga yiwa Salma sannan ta dawo normal ta daina damuwa,amma duk da haka idan ta tuna takan shiga damuwa.
Zainura kwance take a jikin Irfan yana mata tausa tare da lallashinta,Zainura tana shagwaba cike da salo tace Habibty Allah ka bani wahala,cikin nan ya girma amma baza ka dan hakura ba sai na haihu,Irfan yana murmushi me dauke da nishadi ya furta taya ina da kamar ki zan iya hakura Mine?ina ganinki kema kin san bazan iya ba,yanzu idan ma kin haihu tausayin kaina nakeji wanne Hali zan shiga,Zainura tayi wani fari da Ido tare da lumshesu ta kara wani kyau,Irfan ya shagala da kallonta iska ta hura masa a Ido kadan,ya dawo daga tunanin shaukin Zeena dinsa daya fada,gira daya ya dage mata tare da kashe mata Ido daya kyawunsa ya kara bayyana,Zainura taja ajiyar zuciya,Habibty kai me kyau ne,kin fini kyau Zeena,yawwa Habibty na tuna kaga fa ka hanani komawa schl,ina ss2 kace sai dai na zana Waec da Neco bayan na haihu amma zaka nemo min University ko? Irfan nan take ya bata rai tare da cewa a'a me kike nema My love?nifa ko kinyi karatu bazan barki kiyi aiki ba,yanzu so kike ma ki koma schl yanda kike din nan maza suna kalle min ke,nasan lokacin kin kara girma kin kara Zama yan mata kinga maza zasuyi ta damun matata,Zainura tayi dariya tare da cewa Habibty ka fiye kishi ni dai dan Allah ka barni nayi ba sai nayi aikin ba to,zan barki amma Bana so sai dai na hakura haka.
Afrah cikin nan nata wahala yake bata,tana laulayi sosai,Hunaif wani kara sangarta ta yakeyi sai abinda tace kamar a jikinsa cikin yake,ko Office bai fiye fita ba kullum yana wajenta,Haka Aisha matar Doctor ana zuba Love da dan cikinta a gaba, yana kula da abarsa kamar me.Na'im ya biyawa Affa da Ummitu Saudiyya suma zasu tafi tare da Mummy,Harira Da Masa'udu sunga yanda dare daya Allah ya Azurta Affa ta dalilin Salma,haka mutan kauyen sunsha mamaki domin Affa har jama'a ya tara a kauyen ya sanar musu irin abinda suka yiwa Salma,da kansa ya wanke Salma tas a kauyen a daina zarginta,Gashi kuma Salma ta daukesu ma gaba daya sun koma Abuja makeken gida sai abinda suke so,har kauyen suke zuwa a dalleliyar mota driver ke kawo su suyi musu kyauta tare da dangi albarkacin Salma yar riko,Harira sai wani noke noke takeyi anji kunya,sai dana sani take marar amfani,Masa'udu ma da sauran dangi sai kunyar abinda sukayi sukeji suna dana sani,dama duk abinda akayi hakuri zai wuce komai dadewarsa.
Salma yanzu tafi kowa gata iyaye hudu gare ta,ga danginta su Shehu yanda suke ji da ita kamar kwai,Malam da Umma,Affa da Ummitu,ga kuma Mummy uwar mijinta,tun kafin Na'im yace yana son Salma Mummy ta dauki Salma a matsayin yarta.