← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 80

Sashe 4

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faduwa kasa tayi hannayenta da kafafunta suka shanye tana ta faman kakari da gurnani,
Affa da gudu yayi kanta yana karanta mata ayatul kursiyyu,shima jifa dashi akayi gefe ya Sume,Ummitu ta fice da gudu tana kiran jama'a a taimaka mata,sun taho tare da maza da yawa Affa suka gani har ya farfado ya Dafe kansa yana Nishi,Salma kuwa ba ita ba labarinta,

Tuni Raheel ya Lula da ita kasar Paris,cikin wani katafaren gida ya ajiyeta yana gefenta abin mamaki Salma tana farkawa sai gata garau kamar bata yi komai dazu ba,gashinta Bai ragu ba duk kuwa da yanda ta tsigeshi,Bata san ma tayi komai ba bata iya tunawa,Tana kusa da Raheel cikin hadaddun kujerun wanda babu kamar su a duniyarmu,
Ta saba da gidan yana kaita duk wani abu ta iya amfani dasu sabo da komai na manyan masu kudi Raheel ya gama koya mata ta waye,

Amfani da waya da kuma computer Salma ta gama kwarewa sabo da yanda yake bata nasa yana koya mata,
Cikin yan uwansa duk ya kaita amma a suffer biladama take ganinsu,sunsha yawo kasashe daban daban,ta kara wayewa,kimanin 3wks aka kwashe ba Salma ba labarinta,yau katsam Ummitu da Affa suna tsakar gida sai ga Salma ta fito rike da buta daga cikin bayi,ga jakarta a rataye na kayayyakin da ta siyo a paris.

Ummitu sun rigada sun gano Aljanu ne masu karfi suka kama Salma,basu ce mata komai ba haka suka ci gaba da muamularsu

Cikin kauye kuwa magana ta watsu cewar Salma Karuwanci ta fara yi,ta koma sa kaya na masu kudi ta koma kamar yar shugaban kasa,komai nata me tsada,musamman irin wayar dake hannunta da computer ko a city babu me irinta a tsada da kyau,
Kuma sai aga tana ta fito da kudi sababbi tana kyauta dasu sai abinda take so takeyi,watarana kuma a nemeta a rasa har tsawon kwanaki,basu San Salma har daji Raheel kaita yakeyi waje waje yake kaita,
States na Nigeria kuwa ba inda bata sani ba,karatu ma tunda suka shiga ss2 sai taga dama take zuwa,kullum Raheel na tare da ita ya hanata addini,tana so tayi amma a ranta baza ta iya ba.

Tun ranar da ta karanta Qurani sau daya sai da tayi sati guda tana kulle a daki Raheel yana gana mata azaba iri iri dole ta daina karantawa da kanta.
Soyayya kuwa Shanta suke basu fasa ba,yanzu anga kawai Salma ta iya tuka mota abinta,kuna tsaye za kaji tace Raheel I need money ko adadi nawa ta fada sai kaga ta zaro daga aljihu ko bag dinta,abin haushi kudin basa mafanar kowa ayi abu me muhimanci sai na shiririta,Affa garin gigin nemowa Salma magani gaba daya ya rasa shanunsa kaf da suke samun na abinci dasu,talauci yayi musu katutu da kyar suke iya daura tukunya watarana,abun yaci tura addua sukewa Salma ba dare ba rana amma kullum abin gaba yakeyi,domin yanzu sai ayi wata guda ba a ga Salma ba,ga gorin mutan kauyen cewar sun kasa bawa yarinya tarbiyya suna fakewa da Aljanu bayan Karuwanci takeyi,me Aljanu za a gani harda mota tana ja ta alfarma,kaya kamar yar Gomna,wa zai ce Salma a kauye suke har ta fi yan Birni komai da komai,kudi wasa takeyi dasu,marikanta suna cikin talauci sai taga dama zata basu yar Dari biyar ko Dubu daya,basu San Aljani Raheel shine Bai son yaga su Affa sunyi kudi ba,sabo da kar su samu kudin yiwa Salma magani,shi yasa ya jefa musu talauci,suna ta cikinsu ina neman wani magani.

Salma yanzu Aljanu take tayarwa sosai watarana sai tayi 3days tana daki tana ta bige bige,addua akeyi amma ba kanta,duk akan tace tana so ta taimakawa Affa da kudi Raheel yake jefa ta cikin wani hali,duk da haka ba karamin so takewa Raheel ba tana Jin idan ba shi mutuwa zatayi, kullum cikin tunani da shaukinsa take ta kasa ganewa ba mutum bane ya hanata ganewa.

Kamar cirar kaya yau wata Uku kenan Salma ta koma normal bata wani Aljanu,kuma bata kara ganin Raheel dinta ba,abinda ke daga mata hankali kenan,kullum a tunaninsa take sai kukan rashinsa,Ummitu tun tana lallashinta har ta gaji,Salma ta rame ta karmashe sabo da son Raheel da takeyi abin ya wuce hankali,da gaske sonsa takeyi tsakaninta da Allah,ko baya jikinta yayi tafiya tofa sonsa yana jininta sun riga da sun shaku da juna,dashi ta saba tun tana karama,baza ta iya auren wani ba sai shi.

Kamar kullum suna zaune Ummitu ta tura mata abinci tace dole sai taci,loma daya takai bakinta ta barke da kukan tuno da Raheel dinta,kullum abincin yan gayu yake bata tana ci na alfarma,
Bata cin garau garau,da karfi tace Raheel sabo da me zaka gujeni dan Allah ka dawo ka taimaka min,
Tausayinta Ummi taji tasan Aljani ya riga da ya auri Salmanta kamar yanda Malam ya gaya musu.

Lallashinta Ummitu ta fara tace kiyi shuru Salma zai dawo ne ai kinji, dan ci abincin kin rame sosai ko so kike idan yazo ya ganki kin lalace ya daina Sonki?cike da farinciki Salma ta karbe abinci taci ta koshi kar Raheel ya ganta ta lalace tun basuyi aure ba.

Ranar kuwa da dare Raheel yazo zance sunsha love kamar zasu cinye junansu sabo da murnar ganin juna,ya bata hakuri tafiya yayi me tsawo,kuma komawa zaiyi karta damu nan da 6mnths zai sake dawowa.
Ranar kamar kar su rabu ta rungumeshi tana shakar kamshinsa me sanyi haka ya bata kudi zasu kai Dubu dari,da kayan sawa taji dadi ta boye abinta ko Ummitu bata San dasu ba in da sabo sun Saba da ganin Salma da kayayyaki da kudi sun San aljaninta suke bata,
Addua ce kawai tasu.

Bayan wata daya da sake tafiyar Raheel Salma ta fara laulayin ciki sosai,Ummitu kuka takeyi da Affa duk tunaninsu da gaske ne Salma karuwancin takeyi ba Aljanu bane,Affa yana kuka a gefe Salma na sheka Amai dawowarsu daga asibiti kenan,Affa yace Salma kin cucemu ki fada min dan ubanki wa yayi miki ciki Ashe abinda ake fada a gari gaskiya ne?

Salma ta fashe da kuka tana rantsuwa wlh ita bata taba kwanciya da namiji ba,Ummitu tace sake magana Salma a ruwa zaki sha gashi dai har a asibiti an tabbatar mana ciki kikayi,Wlh Ummi ban san wani namiji ba,muje a dubani Ku gani am virgin ba wanda ya taba sanina,yo ke ai Allah daya zakice na yarda abinda ko sallah bayi kike ba sai ansha fama,
Amma Allah ya kaimu gobe zamu koma a duba.

Washe gari sunje asibiti again an tabbatar musu Salma virgin ce bata taba muamula da maza ba,
Ummitu tace to Salma ko dai Aljanin naki ne?me yake miki?Salma tace wlh ba ruwansa kuma ba Aljani bane ba,salihine gaskiya karku daura masa hakki abinda ko hannu baya rikemin sai ta kama,ni dai wlh kuna zaginsa sai na bar gidan nan,ku dinga daukan hakkin bawan Allah haka kawai,kuma ina son cikin nan dole ni zan raineshi,
Affa bakin ciki ya rufe shi ga talauci ya ishesu ga masifar mutan gari,ya zasuyi idan aka gane Salma Nada ciki.

Wajen Malaminsa yaje Malam yayi istihara yace Aljanun da suke tare da itane suka sa mata cikin kuma zasu dauke abinsu nan gaba dama suna yin haka amma zamu taimaka da addua,ga rubutu lallai a bata ta Sha ko ta yaya ne,Koda Affa ya bawa Salma rubutu tasha kamar gaske tana karba sai ta watsar dashi ta jefar da kwanon.

Affa da Ummitu shawara sukayi su kai Salma wajen danginta ace tayi aure nan gaba idan ba cikin sai ta dawo wajensu sabo da gulmar mutan kauye tabbas idan aka gano sai an koresu daga kauyen koma a jefesu gaba daya.

Haka suka tattara Salma da kayanta suka tafi Borno suka zankada karya cewar auren Salma akayi mijin ya saketa tana da ciki taki sakin ranta shine suka kawota nan gaba idan ta huta ta dawo wajensu.
Dangin uwar Salma da ubanta sukayi tsalle suka dire sukace sai dai in cikin shege tayi za a raina musu hankali abinda Salma na zuwa musu akai akai tayi kwana daya biyu da za ayi bikinta ai da sun sani,bayan last 3wks ma tazo musu,basu San Raheel ke kawo musu Salma ba ita bata San ma tazo musu ba Sam.

3wks ta cika yaune kuma Mummy ta Raheel da Irfan zasu sauka a kasa Nigeria sai murna Na'im yakeyi,wajen kakarsu zasu sauka Dada kenan,Na'im da kansa tare da securities suka tafi har airport dauko Mummy da Irfan,
Dattijuwa kyakyawa fara da Irfan kyakyawan gaske shima suna sakkowa daga steps din jirgi,da sauri Na'im ya fada jikin Mummy ya dade yana mata shagwaba wanda ya jawo hankalin mutane Kansu yanda yake abin ya zarta tunani kamar yaron goye,
Irfan ne ya gasa masa hararar wasa Allah bro baka da kunya jibi yanda kakeyi kato da kai,Naushin wasa Na'im ya kai masa yana dariya yace ya ankayi ni kun fini shiyya hausa?( Ya akayi kuka fini iya hausa)
U r nt serious bro pls let's go mana cewar Irfan. Suna mota yace Na'im akwai hadaddun mata kuwa a kasar nan?
Mummy ce ta make masa kai Shut up baka da hankali Irfan kai komai mata kuyi aure kunki kuyi,Na'im yace da hausarsa marar kyau Shi wannan yana so Iskanci ne Mummy,kyaleshi sweet son baya ganewa,Irfan yace Oh!Mummy nifa ba Sweet son bane? Yeah of course.kwanciya yayi ajikinta yace Mummy kici gaba da mana addua zamu daina wannan yaron naki bakya ganin shi Beer yake Sha ma.
Duk kun San ba kyau dai ko wlh Ku kiyayeni kafin raina ya baci nayi maganinku ai nasan me kuke aikatawa,sabo da kun maidani mace ban isa daku ba da ubanku yana raye zakuyi haka?ko Danni mace ce ba kunya ba komai a gaba kuke fadan ma laifin da kukeyi ko?baki suka hada a tare suka ce we r sorry Mummy, sorry for ur self cewar Mummy.

Gidan Dada suka sauka Dada sai murna tsohuwar takeyi tana jin dadi yarta ta dawo cikin danginta,Na'im yana zuwa Direct ya kwanta a cinyar Dada yana sauke gajiya.
Chapter 4 · 0% Book details