← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 80

Sashe 76

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin Zainura ya cika wata tara cif Haihuwa kawai ake jira,Irfan baya fita aiki sabo da Zainura,yau Monday yace bari ya leka Office ya dawo da wuri zai ga wasu mutane,Zainura tace Habibty kullum baka fita sabo da jiran haihuwa gashi har yau Bana jin wata Haihuwa,yaune ma kawai nake jin ciwon Mara kadan,Irfan yace ai yanzu zan dawo ciwon Mara ma ai kwana nan kullum dai kin ce kina yin kadan,Salma sukayi ya fita da niyyar ya dawo da wuri,Bayan ya fita da 1hr Ciwon Zainura yayi karfi sosai da sosai,tun tana iya daurewa ta kasa,Waya ta dauka ta kira Irfan bata shiga ba,Sai ta Kira Hunaif bugu daya ya daga,tace Kanina kayi sauri kazo dan Allah ka kaini asibiti maybe Haihuwa zanyi,Habibty ya fita wayarsa bata shiga,kafin ta karasa magana tuni Hunaif ya kashe wayar yasa Afrah ta shirya su tafi dama shi yanzu baya fita,da sauri yazo da mota suka dauki komai na haihuwa suka tafi asibiti,Zainura tana bayan Mota tana daurewa bata cewa komai,Har sukaje Hospital din Na'im,Allah ya taimakesu ana bawa Zeena Room ta Haihu,kamar dama jira ake,Ta haifi danta Namiji kato kyakyawa na gasken gaske.bayan an gama komai sannan Aka sanarwa su Hunaif,Afrah dama tana ciki wajen Zeena,Zainura ta hana su fadawa kowa tace dan Allah karsu fada,Wanka tayi ta shirya tsab kamar ba ita ta haihu ba,Afrah ta dauki dan cikin kaya masu kyau farare,suka shiga mota sai gida.
Lokacin Irfan ya dawo yana tunanin Zainura ta shiga wajen Afrah ko Salma yana jira ta dawo sai tsaki yake ja,Doorbell ce tayi kara ya bude kofar Hunaif ya fara gani,Sai Afrah dauke da Jariri,Zainura ta fito itama charas da ita kamar ba ita ce me jegon ba,binsu yayi da kallo yana mamaki ganin Zainura ba cikin kenan haihuwa tayi,Hunaif yayi dariya sannan ya sanar masa da komai,Naushin Wasa ya kaiwa Hunaif wai basu fada masa ba,nan ya dinga murna tare da karbe dansa yasha addua,sannan yace su Afrah suje gida su huta zai fadawa Mummy yanzu sai a turo dattijuwa me aiki ta zauna tare da Zainura,Haka kuwa akayi,yan Uwa da abin arziki kauye da birni kowa da suka San Irfan da Zainura sunzo,amma baza ayi suna ba,kawai a masallaci za a rada suna ayi yanka shike nan ba wani taro,shi yasa ko dangi da frnds na Zainura daga na birni har na kauye barka suka zo suka koma,jariri yaci suna Arif.
Bayan suna da kwana hudu Zainura tana kashe wanka na tashin hankali,Irfan kuma yace Bai San zance ba,sai dai su rabu da kyar ko ta gudu,h aka sukeyi har Allah yasa tayi arba'in,tasha gyara wanda yaci Uban na Amarya,Zainura Abar kallo ta koma sabo da kyau da tayi,Irfan ya kara rudewa kamar wanda za a kawo masa sabuwar Amarya haka yake zumudi, yafi me Sabuwar Amaryarma murna.
Jariri Arif kuwa yana can shi da dattijuwa me rainonsa tare da taimakawa Zainura da wasu ayyukan,Zainura yau Angon nata ko kuda baya so ya giftasu,sun gurji Amarci son Ransu,sun nunawa juna so,sunyi missing juna,wannan rana ta shiga cikin ranaku mafi girma a zuciyarsu,Zainura wannan game din ita ce jagoran bugata,har kyautar mota Irfan ya bata sabo da dadin da yaji tare da farin ciki,Allah sarki Salma sai yanzu ta samu Hutu,tunda Zainura ta haihu take sintiri a gidan Zainura tana taimaka mata,hakan har fushi Na'im keyi da ita,Na'im yana matukar son Arif ji yake kamar ya daukeshi.

Bayan wata Uku da Haihuwar Zainura Afrah ma ta haifi danta Namiji kato balarabe sak,Itama ba shagalin suna a mosque aka rada tare da yanka mata raguna guda hudu manya kamar na Zainura,Yaro yaci sunan Babansu Alawwal suna ce masa King,wata daya tsakani Aisha ta Haifi yan biyu mace da Namiji,ansha murna da tsalle sabo da Doctor Aliyu danginsa suna da gadon haifar yan biyu,ga Aisha ma ta haifa amma Aisha ita sai da akayi shagalin suna a wani hadadden waje cikin Abuja suka kama anci an Sha an cashe,yara sun samu suna Suhail da Suhailat abinsu Shar Shar dasu.

Ranar da dare da suka dawo daga shagalin sunan da dare wurin 2am Salma Kuka ta fara wiwi na tausayin kanta,Na'im ya rasa yanda zaiyi da ita tayi shuru,ba irin lallashin da bai mata amma taki ji,har haushi ta bashi ya shareta haka sukayi shirin bacci,shi ya shiryata ta fes tana ta hawaye yace ta kwanta taki kwanciya ta zauna a kasa tare da jingina da jikin Bed taci gaba da Kukanta ba Sauti,Na'im ya kwanta ya kyaleta idan ya fara bacci sai ta fara me Sauti yanda bazaiyi baccinba,idan ya tashi yace tayi shuru baza tayi ba,Fushi yayi ya tashi tare da komawa Palo baya son jin kukan Salmansa,gashi bazai iya bata abinda take so ba Allah kadai ke bayarwa,
Yana PA saman Sofa ya kasa bacci,kawai ya hakura ya dawo cikin bedroom tare da daukan Salma kamar tsinke,yayi jifa da kayan jikinsu gaba daya,saman bed ya daura ta yana a samanta sannan yace yi min shuru malama kin San ni bazan iya baki da ba,amma kin San ba abinda Bana miki Allah bai kawo ba,dan me zaki sani gaba kina kuka,bafa ni na hanaki ba,Salma tana shesheka tace ai kaine kaki dagewa gashi nan su sai haihuwa sukeyi,karfa kiyi sabo Salma,ya kike so nayi miki,mene ne zaki hana kanki zaman lfy?why all ths? Salma cike da Shagwaba ta furta ni...ni...to...kawai kaje kayi min kishiya,dariya ma ta bashi dama duk akan kishi take wannan abun,to wa yace miki zanyi aure?ba wata wacce zan aura ko na hadaku bazan iya adalci ba,ke zan fifita Salmana yana maganar yana kissing din lips nata tare da cewa Yau till down zamu yi Allah yasa ki samu cikin to tunda kin fi damuwa da Baby a kaina.

Baki ta turo gaba tana kunkuni ae naji ni dai ayi min,me kike cewa,shuru tayi tare da cewa cewa nayi to Ameen fa,murmushi ya saki domin yaji me tace,fuskarsa take kallo kamar zata hadiyeshi a hankali ta rada masa kana da kyau Honey ban san ya akayi kafi mace kyau ba,dariya yayi ta jin dadi yana me kara kankameta tare da shakar kamshinta me matukar dadi da sanyi,kansa ya tura tsakanin boobs dinta yana wasa dasu,Salma ta kara matseshi a jikinta tana lashe masa wuya kamar wata Akuya ta haihu tana lashe danta😍😅,Ranar Sun kwashi shagali Salma taji maza ranar amma buri take Allah yasa ita ma ta samu cikin Na'im dinta.

Zainura an girma fa danta Arif har ya fara rarrafa da zama,wani zukeken gaske dashi,amma Zainura abin dariyarta baya karewa kuma Arif bai isa yayi mata ta'adi ba sai ta kaiwa Irfan kararsa wai yayi masa fada,yau Sunday Irfan yana gida yana aiki a laptop nasa,Zainura tana kitchen ta fito zata shirya dining,sai ta hango Arif Ashe ya tashi daga bacci ya fito ya bar dattijuwa me Kula dashi bata sani ba,ya dauka remote na TV ya farfasashi,Zainura ta kalleshi ta rasa ma me zata ce masa, shi kuwa wasan sa yake yana mata dariya,da sauri ta wuce palon Irfan,yana ganinta haka yasan Arif ne yayi mata ta'adi,kallonta yayi yana murmushi tare da cewa Babyna ya akayi?Zainura tana shagwaba tare da direren kafafu Allah...ka masa fada yanzu sabo da Allah kalli yanda ya lalata remote ni banji haushin lalata remote din bama tunda kai zaka siyo wani amma yanda ya bata min Palo da tarkace For God sake,to yanzu ya zan masa Babyna dukansa kike so nayi ko me? Ke da danki sai ki gyara wajen,Zainura tace ni Allah sai ka bimin hakki na haka kawai,Dauko min shi to na masa fada,da sauri ta fita ta daukoshi,yace yawwa kawo min shi na zageshi yau zaneshi zanyi yana sa min Matata aiki,Zainura tace a'a Dan Allah karka zaneshi,ni baza ka dukar min yaro ba fada zaka masa,oh to kin San hakane zaki ce ya miki laifi,dariya tayi tana shafa kan Arif tace bari na masa wanka na shiryashi sai na kawo ma shi.

Afrah ma Alawwal dinta ya girma haka ma Aisha duk sunyi dagwai dagwai dasu abin sha'awa,suna zamansu lfy da kowa ana zumunci.
Chapter 76 · 0% Book details