← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai sai Nadiyya ta shige jikin Na'im tare da rungumeshi jikinta na rawa har tafi Na'im jaraba,Salma bakin ciki ya kamata kishi ya taso mata bata san sanda taje ta fincike Nadiyya daga jikin Na'im ba tare da jefar da ita kasa ta fadi tim gefe,wuyansa ta Shaka nan take Ashe aljanunta tuni sun tashi ta koma ta cafki Nadiyya ta fara dukanta,Na'im yayi Korari ya raba fadan Amma karfin Aljanu ne da Salma ya kasa haka tayiwa Nadiyya lilis,Su Mummy suka shigo,Mummy tace yau naga yar iskar yarinya jimin yarinya kamar gidan ubanta,daga cin arziki,mutum bakuwa ma Baza ki bari suyi harkar aikinsu ba,N Nadiyya da kyar ta lallaba ta fece daga gidan tana tsinewa Salma tace kuma daga yau ba ita ba Na'im ya jawota gidansu anyi mata duka.
Salma na aljanunta Mummy na masifa,sai da Na'im yace why Momma? Kina kallo nata yana abu ba lafiya kina fada fada aka? Why ku daina bana so ba kyau,sai lokacin Mommy tayi shuru tabbas bata kyauta ba, dan Adam ajizine , addua tayiwa Salma da kanta har taji sauki ta fara bacci,Na'im ya daura ta saman Bed nasa da Katon cikinta da kullum girma yake yi.

Salma sai bacci take Sha abinta Na'im ya sata gaba sai kallonta yakeyi sai da ya gaji ya watsa ruwa ya fito ba ruwansa ya haura saman Bed dinsa bacci ya kwashe shi shima.
Salma tana farkawa ta hangoshi kusa da ita gefe daya,murmushi tayi yau kuma ta tashi fes cikin nishadi sakamakon cikin da ta duba taga babu shi a jikinta ko daya ya bace,sabo da murna ta fara tashin Na'im tare da daddagewa ta dana masa duka a gadon Bayansa,firgit ya bude Ido cike da bacci,tace ana ga yaki kana ga Kura duba cikina,kalli ya bace babu Raheel ya dauki abinsa.

Godiya Dubu masu Sharhi kuna birgeni,kuna kara min karfin gwiwa
Sosai.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

51-55

Official

By
AsmaBaffa

AsmaBaffa fans club
Hause of Hausa Novels
Taskar Fiddausi sodangi.
Yan wannan Gps ina matukar jinjina muku da Sharhi ba yankewa kuna kara min karfin gwiwa godiya nake.

Surayyahrms gp kuma ina godiya kuna gyara halayenku😅

Sauran gps ma ina ganin masu Sharhi da tnx na gode sosai,sai gps wanda Bana cikinsa kuma suna Sharhi na gode sosai fans a ko ina kuke ina miko gaisuwa.

Mamaki ya kama Na'im wannan wanne ciki ne gaba daya basu 1mnth da haduwa da Salma ba amma har ya girma ya bace abinsa babu alamarsa,yana tunani can tasa hannu biyu ta girgiza fuskarsa tare da jawo masa kumatu wai kayi magana mana ka tsaya kallona,hannunta ya cire a hankali,yaja tsaki cikin hausarsa yace sai ana bacci ne kuma sai kina duka na mutum,ciki is ur own Business zai kara baka wani wani soon.
Da murna Salma ta Mike tsaye a saman Bed din,harara ya zuba mata,sauko mini from my Bed zakina zowa a taka min Bedsheet with ur dirty legs.
Salma dadi yasa ko sauraren Na'im bata yi sai tsalle da tayi ta Sakko kamar abin arziki yana komawa tare da kwanciyarsa again yana kallon sama ya lumshe ido iya karfinta tasa hannaye ta riko kafarsa daya tana kokarin jawoshi kasa tana ta kici kici ta kasa,ta lankwasa ta can ta lankwasota nan,kallonta yake yanda take ta fama tare da Surutu tana dariya ai sai ka sakko kasa ba kai ba bacci dama yamma tayi,
Dariya ma take bashi,kawai sai ta maida kafarsa ta koma speaker kamar mawakiya ta kwalla da karfi ba ciki.........ya tafi....ehhhhhhhh......jama'ar Abuja birnin tarayya kowa ya sheda na haihuuuuu........ehhhhhhho........gaba daya su Irfan dasu Mummy tare da duk wanda ke aiki a gidan sai da ya jiyo siririyar muryar Salma me zaki,tunanin kowa aljanunta ne suka tashi,su Mummy suka taho da gudu part din Na'im,Salma najin tafiya ta saki kafar Na'im ta koma can saman Sofa da sauri ta kwanta tayi baccin karya,suna shigowa suka hango Na'im saman Bed idonsa bude sai murmushi yake zubawa,Salma tana can Sofa tana bacci abinta ba Susan baccin karya take ba,
Mummy tace kai ina na ji muryar Salma ko dai aljanunta a gidan suka watsu? Na'im ba karya ba boye boye shi dole sai ya fadi gaskiya da hausar tasa yace Bacci nata na karyane,anan tanayin bacci nata ya nuna kusa Dashi,ciki nata babu yanju,thts why tana murna tana iho now.

Irfan ne kadai ya gane me Na'im yake nufi,yace Momma cikinta ya bace wlh kalli Aljani ya doka abu nasa shima Irfan hausar sai a slow.
Murna suka dinga taya Salma amma yarinyar taki bude Ido a dole bacci takeyi.fita sukayi suka kyaleta,suna fita ta bude idonta kar tacewa Na'im kai wato ba sirri da kai sai ka fadi gaskiya ko,baki ya tabe tare da cewa Sirri munafuka ne yakeyi ni bana haka( sirri munafunci ne shi baya yi haka yake so yace)

Salma tace ya dace ka koyi Sirri,gulma gulma ne Bana sonsa,ina Babynka?ur girlfriend?Harara ya zuba mata yace kin sa mini Badmood ne,to wai da me kake so kayi mata? Harara ya zuba mata yace ur father zanyi mata,bayan kana duka nata ya tafi u make me Sad, dariya tayi ta yi tace sabo da wannan na dawo dakin nan da Zama na koma me gadinka,gate ne ni da zaki koma gatewoman? Ka daina iskanci da mata Allah ba kyau tam,
Rufe baki naka like Duck wai irin ba'a yayi mata,yayi mika tare da mikewa tsaye yace ina feeling iskanci wlh,hhhh dariya Salma tayi tace Wai kai ance a hausance ma mutum baya kiran kansa dan iska,baka ganewa zagine, Na'im yace kene baki ji na hausa tunda ba Allah yace anayin wannan ba mene name nashi?Salma ta bashi amsa iskanci,ok kice ba dai dai na fadi maka ba,Ni dan iska ne yes ina so iskanci ya tsuke baki yana baka ji na hausa da yawa kina cewa zakina koya min hausa,me kika sane a hausa? Surutu Surutu cacacacaca....me Shan noanoa na shaniyoyi kazamiya.(shifa nan ya zagin Salma me Shan Nonon saniya kazama bata Jin hausa shi zata koyawa hausa duk abinda ba Allah ne yace ayi shi ba to iskanci sunansa shi kuma bashi da aure amma yana Romancing mata dan haka shi fa Bai yarda ba dan iska ne shi kuma yana son Iskanci.)

Salma dariya take ta Sha tace ni dai Bana iskanci da maza,zaro Ido waje yayi yace ciki naka wane ya baka idan ba an shinye ka ba? Ni Bana shinyewa mata what of u?u r nt a virgin,(batayi iskanci ba ya ta samu ciki,shi fa baya Cinyewa mata)

Salma shuru tayi tasan Na'im bashi da kunya ko ta digo turai ce a jikinsa,bai San kunya ba bare ma baya jin hausa sosai komai kwabowa zaiyi ya fada tunaninsa dai dai ne,wanka ya shiga,ita kuma ta dinga jidar akwatunanta tana kaiwa bedroom dinta har ta kwashe kayanta tas daga Dakin Na'im.
Mummy tace ko fada kukayi da mutumin naki?a'a Mummy kayana na ebo kawai kullum fa sai naje na karbo kinga yanzu suna wajena,yayi kyau hakan ma cewar Mummy,Aisha na ganin Salma ta Mike zata bar palon kar ta tona mata asiri,Da kin daina guduwa ma gaskiyace zan fadawa Mummy yau a gidan kawarki kika yini tun safe,Kunyi shaye shaye kunyi lez dan haka Mummy ki dauki mataki bata daina abinda takeyi ba.

Irfan ne ya shigo yace ki dinga Sallah tukun sai ki fadi laifin wani,mutumin da baya Sallah ai gwara kowa dashi a duniya,Salma ta maka masa harara tace Sallah ce fa kawai kuma ai ni a boye nake tawa,bana yi a idon mutane sabo da ni dan Allah nake tawa,Mummy ma dariya tayi na maganar Salma,Irfan yaci gaba a dai dinga Sallah ko a samu a shiga aljanna,katuwar budurwa bata Sallah ke da Arne baku da banbanci,Kukan shagwaba Salma ta fara,Mummy tace maganinki kenan kunfi kusa ai,kullum ke bakinki baya shuru,kukanta ta karawa Volume,daga nan tace Allah sai na fadawa Raheel dina wai Na'im take nufi,

Sai kuwa ga Na'im yana sakkowa cike da takunsa na isa,sanye yake da kana nan kaya yasha swagg ya gaji da kyau,da gudu taje wajensa tare da riko hannunsa tace kaji wai Wannan yace Bana Sallah kuma Mummy bata ce komai ba, who said so? Na'im ya tambaya da karfi irin serious din nan,ta nuna Irfan gashi nan me kama da kai,Kyale sa zani duka shi na Zane masa jiki,tana Sallah kana cewa batayi ,ko batayi ai zata fara kwanan nan sai ta fika ma yin Sallah,yau yawo zan kaita,yi masa tongue out,aiko ta dinga yiwa Irfan gwalo wulluuuuuu an masa fada,za a Zane wani,kuma baza muje da kai yawo ba,yaushe ma zan biki yawo bata Sallah woooo,Na'im da gaske yanzu harara ya bashi me kyau cikin turanci ya dinga masa fada sosai da masifa,ya daina yin haka,a hankali zata dinga yin Sallah ba sai ana kure mutum ana kunyatashi ba kyau.

Irfan yace mu baka ganin abinda take mana sai ita kawai kace kana sonta zaka dinga raina mana hankali ba wanda ya isa yayiwa yarinya fada ko magana sai ka wani shige ciki kana fada,har Mummy baka kyalewa,ai sangarta ne da lalata mutum, na fada maka dai Allah karna kara ji kana mata gorin bata Sallah,tunda ba nasiha kake mata ba sai dai kawai ka fada mata bakar magana,ok baka ganin rashin kunyar da take mana nawa take Hunaif da Aisha sun girmeta,little kid ce sai kuyi hakuri har ta daina. Shuru Irfan Ya masa saida Na'im ya karaci fadansa sannan yayiwa guards nasa waya zai fita Hospital,kallon Salma yayi duk ta shiga damuwa akan zai fita,ita bata saba da kowa ba sai Na'im,ki shirya Driver zaizo ya dauko min ke ok?cikin farin ciki tace to bye Allah ya kaika lfy,Har Irfan saida ya kalli Salma domin shi baita jin tace Allah ba sai yau.
Chapter 14 · 0% Book details