← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 80

Sashe 63

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainura suna mota yana driving yace Mummy ta bani aiki ni ban san me za ayi miki a gidan matar da tace sai na kaiki,Zainura tace zai wuce gyaran jiki ne,wannan gyaran jiki bazai kare ba kullum gyaran jiki wai me akewa fatar ne haka? Zainura tace ina zan sani nima wani daki ake cewa mu shiga yana fitar da tiririn Zafi sai kaga skin yayi smooth shike nan fa,Irfan yayi dariya Allah Zubaida ni zaki rainawa hankali bafa Audu me kifi bane,au dama ka sani kake tambayata Ashe? Na sani mana zanji dadi gaskiya,Zainura taji kunya harda rufe fuska Auzubillahi,bayan ya kaita saida ya jira ta gama sannan ta fito suka tafi a hanyarsu ta dawowa ya siya musu kaji, ice cream da snacks ta bawa su Jamila kawayenta,taji dadi sosai sai godiya take masa,tana shiga ta zube musu ledoji tace gashi nan Baby yace a baku,Rahina matar Abubakar itace ta bude ledar tare da lekawa tace Wai cakwala dadi sai ko suka taso suna ci suna Santi,Jamila tace kai Zainura kinyi dace,Zahrau ta yagi kaza tace Wai cikinsu wa yafi wani kirki ne,Rahmatu tace ai mijin Salma da ya kaimu Makkah shine na farko,Sai Hunaif kullum da muka zo shi yake kawo mana kayan dadi,kalli dunkuna ma duk shi ya siya mana ya biya kudin dinki emergency,Zainura ta bata rai tace ae wato Irfan din nawa ne tsinanne,Rahmatu tace shi Irfan shine yasa aka kaimu Saloon ya biya kudin ko wacce aka yi mata na yan gayu,yasa aka dauko mana me lalle tayi mana,ga kudin liki duk ya bamu,gashi yanzu ya mana siyayya,Zainab tace kin manta har takalma ya bada kudi Salma ta siyo mana masu kyau na birgewa sabo da mu fito Shar muma,cikinsu kowa yana da kirki ba baya,Zainura tace to dai Irfan dina yafi kirki,sannu sarkin Son kai ai wlh mijina yafi na kowa kirki da komai Salma ta furta da shigowarta kenan,suna Zaune sai ga Hunaif tare da balarabiyarsa Afrah sai fara'a take bata Jin Hausa sai dai suyi turanci,wai kawota yayi su saba da Salma da Zainura sannan ta shiga Hausawa yan mata itama,sai dai tayi ta dariya tana kallonsu bata San me suke cewa ba,Salma da Zainura kadai ke mata turanci duk da cewa Zainura bata gama gogewa ba a turancin amma tana kokari,sai dai idan wata Kalmar ta gagareta tace ke ni ban sani ba.

Yanzu ma Zainura tayi turancin tayi ya kare mata ta manta kuma me zatace ta kalli Afrah tace ke dan Ubanki nima bafa wani kwarewa nayi ba,Afrah ta mata zancen kurame tana dariya me tace? Zainura tace ai wlh bazan kara yin turanci ba yau na gama baza ki wahalar dani ba,Tace what? Tana tambaya Still Zainura tace Wai cewa nayi Ubanki ko bakyaji? Tace I don't understand what do u mean? Zainura ta fara shure shure wayyo ni wlh an takura min sai nayi turanci nima fa ba gama iyawa nayi ni wlh bazan yi ba,
Afrah ta dinga dariya abinda taga Zainura tanayi na yara,Salma tayi dariya taci gaba da hira da Afrah,zainura ta fara masifa ke Salma dalla mene zaku hade min kai ni salon a wareni ko faccalanci zaku nuna min tun ba ayi auren ba,Allah shiryeki Zainura cewar Barira,Jamila ta kalli Balarabiya ta tuno da Islamiya yanda suke cewa malami,tace Sabahul khair ya Afran Hunaif,suka sheke da dariya,Zainab ma tace bisalam sai tace mu'assalam ya mu'allim ko ba haka ba Afrah? Afrah dai ta gane Larabci wai suke mata kadan,Kawai ta daga kai tana dariya,Zahrau ma tace nima sai na fadi nawa tace Afrah Ijilis,Jalasna ya sayyadina,Afrah ta dinga sheka dariya ta kara daga kai sannan ta fadawa Salma da turanci cewar Larabcin ai kala kala ne,wannan Bana kasarsu bane Saudiya suna yin irin wannan da suka fada duk da cewa harshensu bai iya fadi dai dai amma Na saudiyya ne,Zainura tace Ashe kunji bayin Allah a larabcinma akwai broken kamar turanci akwai Broken pidgin English,Dariya Sukayi sukace Ashe nasu ma Broken sukeyi ba irin na Saudi bane,cab Ashe ba larabawan kirki bane cewar Zainab gashi tun ba a je ko ina ba har mun kureta,Zainura tace ke Afrah mene Habbibty? Habibi ta fada musu ai kuwa Zainura tace yanzu Irfan zata dinga fadawa Habibty kar taji a bakin Afrah tana fadawa Hunaif shi ta rigata,Afrah ta dinga dariya harda kwalla tunda da turanci Zainura ta fada mata.
Zainab tace yawwa Zainura yama tallan da muke gani a TV din gidan Sale?wannan na madarar?cewar Rahmatu,Zainura tace Labanil mara'i Almara'i bari muji ko suna shanta,Zainab tace Afrah what is a Labanil mara'i Almara'i hhh Zainab anji turanci,Afrah tace ai wata madarace ta wani Company,Sai Jamila ace Al filun,ishajartu,jamalun,kalam,dar,Hazihi,Hazihi dar,Zainura tace kin manta Alburtuqal,Baqaratun cewar Zahrau itama,Sirasil,ankabut haka sukai ta faman jerowa Afrah tana ta fada musu amsa da turanci tana dariya,saida suka gaji sukace to taci jarabawa amma da bata amsa wannan ba koma mece ba Balarabiya bace kawai yar gudun hijirace daga wani yankin cewar Zainura,Salma tasha dariya kamar me,basu da aikin yi sun gama komai har lalle Mummy da safe da wuri tasa akayi musu komai,tace bata son ana biki Amare basa nan ayi ta batawa mutane lokaci wajen gyara,shi yasa komai akayi akan lokaci aka gama ba bata lokaci,Da kyar Na'im yace Mummy ta bari ayi wedding dinner guda daya tal ,haka ta hakura suka shirya komai,Friday gobe kenan za a daura aure da walima,da yamma za ayi Dj a gida kowa ya cashe, Saturday wedding dinner da dare,Sunday sai a kai Amare,Irfan yace shi a kaisu Saturday sai suje Dinner daga gidan mijinsu,Na'im ma yace haka,Mummy tace sai Sunday sabo da su sukace zasuyi Dinner baza su ruda su ba,ga shirin Dinner ga kai Amare kuma har Uku bazai yuwu ba,komai a nutse zasu yi.

Barira taje wajen Mummy tace su dai wlh sai sunyiwa Amare kamunsu na kauye,a bawa Salma turare itace matar yaya tazo ta kama Amare ko a bawa Umma tazo ta fesa,Zainura tace Salma kawarta ce wlh bata isa ta mata Kamu ba sai dai a bawa Umma ko cikin danginta na kauye da suka zo,Iyayen Zainura ma suna nan sunce ba sai anje kauye daurin aure ba su zasuzo Abuja sun hutar dasu Mummy ai suma iyayen Zainura ne,shike nan kuwa har dangi masu zuwa suka zo bikin suna gidan part din Umma da Malam suka sauka,Baba zainura da danginsa Maza duk Malam ya saukesu bangaren maza baki.

Salma harda hawaye takeyi ganin dangin kowa ya hadu amma ita babu nata ciki,sai Umma da Malam sai dangin miji,bata da kowa nata,sai ta fashe da Kuka ta koma part din Na'im ta kwanta Saman bed dinsa tana ta kuka,ya shugo bayan ya dawo daga Masallaci Sallar Isha ya Iske Salma tana ta faman Hawaye da shesheka,da sauri ya karasa kusa da ita domin shi baya ganinta sosai ma tunda aka kusa biki,Ba dai kuka kike ba Sweet Baby?lfy? Salma ta kara Volume harda na shagwaba,duk tunaninsa wani abun akayi mata,subhanallahi me akayi miki? My love what's the Matter? Wa ya taba min ke? Fada min wanda ya batawa Amaryata rai,fada min wanda yasa Preetyna kuka take asarar tears haka,Salma cike da shagwaba tace ni...ni....ni...bani da yan Uwa...kowa yana da Uwa da Uba..da...danginsa...ni...bani..da ..ko..daya,Hawaye sukaci gaba da sintiri.
Na'im yaji tausayinta har cikin bargonsa am so sorry Wifey da ina da yanda zanyi wlh da yau sai na kawo miki yan uwanki gidan nan,kiyi hakuri kinji watarana sai labari,zasu zo ne kuma Insha'allah ko ba su zo ba zan je na basu hakuri nan gaba mu lallashesu ko? Salma ta daga gai yes,yace yawwa yan matana yana share mata hawaye da hannunsa,kar na kara gani kinmin asarar hawaye akan wannan ya wuce za ayi maganin abin trust me ok,tace tam tana ajiyar zuciya,kin min abincin? Salma tace ae dazu na gama,Mummy tace akwai a kitchen kar na dafa wani nace mata baka cin abun gidan biki,Na'im yace yes hannu yayi yawa,duk mata sai ayi jagwalgwalo,Salma tace to ai ba a gidan nan akayi ba restaurant aka kai suka yi ake biyansu,i knew Sweet Baby Bana cin nasu ne kema kin sani abincin restaurant sai dole nake ci,sabo da ko nama ne sai suje wajen siya baza su siyo me kyau ba sai marar kyau,Salma tace wasu ma sai suce idan an yanka akuya,tinkiya,ko Saniya masu ciki sai suce dan cikin suke so shi zasu siya yafi laushi da dadi,idan suka kawo sai sharp sharp a zabga farfesu ko girki dashi,kana ci kaji laushi da zaki limis kana ai sun iya girki shi kanshi naman daban ne Ashe ba a sani ba dan jaririn dake cikin Akuyarne ko Saniya,hhhh Na'im ya dinga dariya yace to kingani anci kazanta,Salma tace ko sai sunga naman da aka tare waje guda baida kyau za a zubar sai su siya a araha su kawo restaurant,haka kayan miya irin su tomatoes ma idan kaje layin marasa kyau gwalagwaje shi suke siyowa a gyarashi a Markade kaji ance rice and stew hhhh nan ma Na'im yace wai gwalagwaje banda Sharri Sweet wife,Salma tace Allah ba sharri bane a Nigeria da yawa haka akeyi,kaje mayanka wajen da dabbobi kawai ake yankawa ka gani,sai kaga Hajiya tasha kaya tazo a mota da Leda katuwa suna ta siyan jariran saniya ko Akuya ko marar kyau,haka kayan miya ma kagansu ana ta sa musu a leda suna figar motarsu,hhhh Na'im ya kara dariya yace gwara da kika kara gaya min gaskiya amma suna cutar da alumma a Nigeria shi yasa ba a ci gaba kowa zalunci da cuta yasa a ransa,Salma tace ga son Banza.
Na'im yace yanzu da ke ana abin kirki dake da kin dan jiyar dani dadi,Salma ta turo baki ka bari ni dai Allah sai jibi an kawo Amare,na hakura ai Allah ya kaimu,kuma ki tabbatar ranar kisa nayi suman Dadi ko nayi kuka sosai idan ba haka ba to Kin San sauran kema.
Dariya tayi tare da yi masa rada a kunne ta fece da gudu ta bar dakin,yana zuba murmushinsa me kyau.
Chapter 63 · 0% Book details