← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 80

Sashe 26

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mummy abin nata harda rashin tawakali ma domin yanzu har sambatu takeyi kala kala,yau tana kwance ta rame tayi baki kamar ba Mummy ba kowa ya ganta sai ya tausaya kamar Na'im ne kadai danta,Su Irfan har basa son ganinta Sabo da zuciyarsu karyewa takeyi,duk wanda ya shigo sai dai ta dinga Na'im kaine? Na'im dina ya dawo?Na'im zo na shafaka naji,abin gwanin tausayi surutu iri iri.
Dada ta dawo gidan da zama tana kula da yarta,haka dangi ana zuwa musu jaje da duba Mummy, yau Dada ta shigo dakin sai ko Mummy tana daga kwance Hawaye na sintiri a idonta ta fara Na'im kaine?ka dawo? Zo ga Mummy naka,Salma kake so?zan aura ma ita,duk inda ta shige za a nemota,Dada tayi tsalle gefe tare da cewa yau na shigesu da wannan yarinya ni yau me zan gani haka?kashe kanki zakiyi Sabo da rashin karbar kaddara,sabo da rashin tawakali,da mutuwa yayi fa sai kema ki bishi,yara nawa gareki baza ki godewa Allah ba sai shashanci,Mummy ita dai ba ruwanta tana ji ance ma da mutuwa yayi fa ta saka kuka wiwi harda gunji tana ni gwara na mutu na huta,gwara na shiga daji,Irfan duk sun tsaya can gefe ransu ya jagule,Aisha kuwa kuka itama take taya Mummy,tana tausayin Uwarsu,yanzu Aisha babu jin dadin rayuwar da za tafi shaye shaye,an daina lez ma gaba daya ta daina komai yanzu to gida ba lfy,dama komai jin dadi ke sawa ayi,Irfan kuwa shi ke komai duk business na Na'im shi yake rike komai bashi da time ko kadan,Hunaif ma ya zage a wani part din,kullum Irfan idan yaje Office companies na Na'im sai ya zubar da Hawaye,haka sauran ma,Hunaif kuwa Hospital din shike kula dashi na Na'im idan yaji ana neman Doctor Me Imani sai zuciyarsa ta karye ya zubar da Hawaye,ace sai dai kaninsa,nan ya tambayi me Na'im kewa patients ne suke damuwa dashi haka ana Jimamin rashinsa?Suka ce ai kaf patients indai shi ya dubaka to komai girman cuta kyauta za ayi maka aiki,nan Shima Hunaif duk Ranar da ya shiga asibitin shi ba Doctor ba amma Idan wasu Doctors sun duba zai zabi da yawa a musu komai kyauta yanda Na'im keyi yace idan ya mutu Allah haskaka kabarinsa,idan kuma yana raye anyi Sadaka Allah bayyana shi da gaggawa.

Aisha kuwa Watarana tana zuwa Embassy ta sanar musu duk halin da ake ciki fa ba a ganshi ba,wayoyin Na'im da System nasa duk Irfan ke Amfani dasu wajen Aikinsu.

Dada dai taga Mummy idan sunyi sake haukacewa zatayi kawai ta fara taimako da adduoi Amma abin kullum ci gaba yake,Irfan yace kawai a kaita asibiti ta zauna acan kar brain nata ya samu matsala.
Nan aka kai Mummy asibiti ana kula da ita ko yaushe,Dada na wajenta su Aisha suna hanya kullum har dare asibiti ya koma kamar gidansu ma.
Mummy tana dan jin sauki yau ma ta mike zatayi Sallah ta kalli kudu,Dada tace hauka kike ne?ga gabas nan,nan ma Mummy a kalli Arewa abinta zata fara Sallah da kyar aka samu ta daidaita abin ba dadi dai.

Salma da Na'im soyayya sai abinda yaci uban da,kullum Karuwa take a zukatansu kamar su hadiye juna, Malam Magaji ya siyawa Na'im waya me kyau yar dubu ashirin Tecno sabuwa dal,suka siyi sabon layi yasa,nan Salma ta karbo wayar Rahina suka tura hotunansu na Sallar taushe,Kullum sai sun dauki hotuna kamar hauka a wayar nan duk wanka sai sunyi selfie,Umma da Malam tun suna shiga har sun daina ana yin hoton dasu,har video suke daukan kansu idan sun fita yawo a garin,Yauma Umma ta aikesu a siyo mata Kubewa danya da dankalin Hausa,sun fita sai hira sukeyi suna tafka muhawara akan kalmar Soyayya da kauna,Salma tace na fika iya yaren nan fa So shine Love fa,Kauna kuma fa? Yace kauna...kauna ya tafi tunani ya kasa tunawa,Salma tace ahaf shine dai so,sanda kayi min kiss din nan jiya kasan sunansa?to soyayya mukayi fa,Na'im yace hakane soyayya?ke baki santa ba dalla,ai so shine soyayya ake soyawa,Salma ta langabe kai tace ohhh...na gane a kasko ko?yace kwarai ke baki ganewa ne har yau,tace to ai gwara da ka ganar dani kaga yanzu na gane,Ko dai mu tambayi Rahina? Na'im yace nop komai sai mun tambaya tunda muna ganewa mu daina tambayar kowa tace to.
Tunda Na'im yake bai taba zagi ba na ashar amma a kauyen nan ya iyata,daga shi har Salma basu san zagine ko ba zagi bane su Kalmar ma dariya take basu,sai suyi ta narkawa junansu ita suna video a waya,Salma ta daga waya sama yace Dan bura Uba shege suka kyalkyale da dariya,Salma ma ta fada masa,idan Umma ta aikesu har gajiya take da jira Sabo da hira da sukeyi da jarabar daukan hoto da video.
Suna dawowa Umma ta rufesu da fada tace daga yau na daina aikenku tare ba inda Dayanku zaibi daya,ya Isa na gama abinci Amma kuna can kuna daukan hoton Banza da wofi.
Saida suka bawa Umma hakuri ta daina musu masifa.

Tunda Na'im yace Salma zata jirashi a zaure yau kimanin 3days kenan basuyi komai ba akan Malam ya musu aure,waya ta dauke musu hankali sun manta da zancen nasu,Na'im garin danne danne ya gano yanda ake searching abu a Google nan ma Google yaga ta kansa shi da Salma duk kudin Malam suke karbewa suna Sa kati suyi ta searching Words na banza da wofi.
Malam Magaji ne yace ko su daina ko Ya kwace wayar shike nan aka samu salama basa dannawa sai jefi jefi,Malam yaga Sabo da waya ko addininsu yaja baya kawai ya kwace wayar ya kashe tare da boyeta yace su zauna haka tunda ba a musu abin arziki,Yanzu ba waya sai radio FM da Am da suke jarabar ji kowanne shiri ji sukeyi kullum radio sai za ayi bacci ake kashewa nan ma sun damu Malam ko wanne shiri sun san da zamansa musamman shirin soyayya ko karatun Novel har na yaki,Da sunji abin mamaki Salma zatace kai kaji dan Allah Me gidana,shima da yaji zaice kinji yi shuru,yauma ana shirin rai dangin goro sunaji ana karantawa ance Farouq ya mike ya zabga mata mari Salma ta dauki radion ta manna ta a bakinta tace ki rama kema mana Sadiya,ta kara fada da karfi,Na'im ya kwace yace baki iya ba basa Jinki muryarki tayi low,nan ya jijjiga Radion tare da cewa Farouq ka kara mata 1slap me cuta ce,Radio shuru sai karatu akeyi Salma ta doka radio da kasa tare da cewa aikin banza dan wulakanci sunki mana magana,Na'im yace gwara da kikayi haka kin birgeni,Saida Umma ta fito sannan ta musu bayanin mene Radio sukayi Zuru suna ji suna mamaki,Salma tace wai a duniya duk ake da wannan abin haka? oh duniya ina zaki damu cewar Na'im.
Chapter 26 · 0% Book details