← Book details Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 80

Sashe 12

Kamarsu Ce Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wanka tayi ta leko ta jikin kofarta daga ita sai towel duk suna palon,a hankali tace Aisha jeki dakin Bro naku kice ya baki kaya zan sa,ba a ganin Salma sai daí maganarta ta jikin kofa.

Aisha tunda Salma ta tona mata asiri take tsoronta da Sauri taje tayiwa Na'im knocking daga shi sai singlet da 3qtr yasha kyau yace lfy?Salmanka tace ka bata kayan da zata Sa wai,
Sai lokacin ya tuna kayanta suna part nasa maimakon ya bata akwatunanta sai ya bude ya dauko Inner bra da pant,da riga da skert na jar Atamfa Holand yar gaske,kayan kwalliya ma budewa yayi ya ebo wasu ya Bada ungo kai mata,ka bayar a kai mata kayanta mana gaba daya me zakayi dasu?
Ina ne ruwanki? ina da reason ki daina shiga cikin lamarina banza shashasha dan Iska.
Allah baka hakuri cewar Aisha,yace Ameen.

Tana bawa Salma itama bata ce a kawo mata kayanta ba kawai wanda ya bata da su tayi amfani,zama tayi ta tsara kwalliya kamar zataje Dinner.
Kamar a saceta,yayinda Na'im tuni yana palo ya gama bawa Mummy da yan uwansa labarin abinda ya faru kaf, kitchen Mummy ta shiga tace bari nazo, cikin gwarancinsa yace wa Irfan cikin Rada kar wani yaji ya furta suna so suna she min ina cinye mashe,Salma fa wai na shinye ta ni na bata kato kato Wannan Baby, shi kanshi Irfan ba wata hausar ce ta ratsashi ba amma yafi Na'im yace kyale su ba Ilmi jahilceni suke ma(wai Jahiltarka sukayi yake nufi Irfan) sunji tausayin Salma,Mummy tace ta zauna dasu kawai har aga me Allah zaiyi,Aisha kirawota aci abinci,kafin Aisha ta mike wani kamshi ya dakesu ba shiri kowannensu ya dago kai Salma ce kamar yar India atamfar tayi mata kyau Dinkin ma ko yayinsa ba a a fara ba,ba wanda ya taba ganin irinsa ya hadu karshe ya kamata cif cif.
Irfan yaja ajiyar zuciya,Hunaif yace ya salam irin wannan ake nema,Na'im ya Galla masa harara yana hade rai,Aisha tace wow kinyi kyau Salma,Mummy kuwa masha'allah tace Salma tayi murmushi tare da jan kujera daya a dining kamar gidansu ta zauna itama kamar me rayuwa a turai ba ruwanta da wani kara komai normal kamar yar gida.

Kowa yana zaune a dining yayi serving kansa yana ci banda Salma,Mummy tace ke kuma me kike jira?baki ta turo cike da shagwaba tace ni Raheel ne zai zuba min shi nake jira Raheel dina ya saba min kullum shi yake zuba min tun ina kauyenmu yanzu kuma ya shareni, Allah idan bai zuba min ba Bazan taba ci ba.

Kowannensu sakin baki yayi yanda take zuba shagwaba kamar zata narke,
Na'im wani zir zir zir yake ji a Cikin Jininsa,Mummy tace kana ji to Raheel,haushi yaji tare da cewa nifa ba Raheel bane Momma ki daina hadani da wani dan iska can,Salma ta kwalla tafi cike da tsiwa tace wlh ba dan iska bane ehe,kuma sai ka zuba min naci,me zakina iya ci? Na'im ya tambaya, Chips da kifi,shi ya zuba mata tare da tura mata,tana ci tana kallon Na'im sonsa yana kara ratsata,ji take sai yanzu ma take son Raheel,yanzu ta fara sonsa.
Irfan yana gamawa ya mike yace Momma Na fita cinema,Da Sauri Salma tace wlh ba can zai je ba sunyi da wata budurwarsa Hanifa wajenta zaije zasu sheke aya karki barshi Mummy.
Mummy tace Irfan shiga room dinka,nan take Mum tayi waya tace a tsare mata gida kar su bar yaranta su fita ko kofar gida sai gobe.
Irfan ya kalli Salma yace Munafuka ya wuce room dinsa cike da borin kunya,Aisha najin an fara tona musu asiri ta sulale ta bar palon,haka Hunaif ma,Mummy tace Gwara da Allah ya kawoki Salma mutum yana shuka tsiya ki fada min ta mike tare da musu sai da Safe ta haura side nata,daga Salma sai Na'im suka rage suna cin abinci,mikewa yayi ya koma bedroom nasa ba tare da yace komai ba, ya dauko Beer dinsa me tsada zai dan kwankwada a dakinsa Ya bude kenan sai ga Salma ta shugo da Sauri ta kwace kwalabar ta kai toilet ta zubar ta dawo ta jefa kwalba a dustbin.

Yana tsaye yana mamakin karfin hali na Salma,ta gama rainashi,ransa ne ya baci sosai Sabo da Na'im akwai son a girmamashi,cikin wata murya me nuna zallan bacin rai yace get out,lv My room now, kin fita tayi sai ma cewa tayi ba inda zanje sabo da gani take Raheel ne,
Mikewa yayi nan take ya daureta da Mari me matukar zafi da gigita dan Adam,da Sauri ta dafe kumatu yace fitar min a room kar ki kira shiga harkata a gidan nan as from today ko magana karki kara yi min,tsawa ya buga mata Out i said,sum sum tayi waje harda rufe masa room sadaf,salin Alin ta koma room din da aka bata ta shiga kwara amai na laulayi a toilet,rarrafawa tayi ta fada saman Bed kowa yayi sallah banda Salma,haka tayi baccinta shar ba abinda ya dameta.

Washe gari kuwa bata farka bama sai 10am ba abinda ya dameta da sallah,hakan ma Mummy ce ta shigo ta tashe ta tare da cewa hope dai kinyi sallah?tace ai tun asuba bana makara.brush kawai tayi kanta ba dankwali rigar baccin da Aisha ta kawo mata iya gwiwa me siririn Hannu itace kadai a jikinta sai pant,rigar silk ce me santsi haka tana tahamma ta fito har main Palo tana tangadin bacci kamar yar maye,idonta kuma a rufe haka ta karasa wajen dining kowa yana zaune ba wanda ta kula kawai plate ta ja ta ebi duk abinda take so ta juya tayi hanyar Bedroom nata gashi duk ya barbaza ya rufe mata fuska har tsakiyar bayanta,
Na'im dake zaune Ido ya zuba mata ya dauke kai irin fushi yake yi da ita gaba suke da juna.

Irfan Ya Mike da niyyar Binta ya dawo da ita Mummy tace zauna ban son shishigi fa,Hunaif yace da kin bari yaji ko lafiya take,Na'im ya wulla masa Harara,Aisha bata ce musu komai ba abincinta take ci kawai.
Salma na shiga daki ta cinye abincinta tas ta fada wanka ta fito bata canja kaya ba perfume ta shafa kawai ta zura rigar bacccinta tare da dannawa kofarta key, kawai aljanunta suka tashi ta fara chines a dakinta ita daya ba ji ba gani,ana jinta tana ta yi tun suna tunanin zata daina suka ji abu yaci tura,Zumbur Na'im ya Mike shima nasa so suke su tashi muddin yaje wajenta amma da sauri ya kwashi alluran bacci ya haura dakin Salma,gaba daya suka biyo bayansa,zuwansa jikin kofar kenan ya fadi a wajen yayi sharaf dashi idonsa ya juye kamar me suma,Mummy da Irfan suka rude su basu taba Sanin Na'im yana da Aljanu ba sai yau,ashe har tashi suna yi,da Sauri suka rufar masa da karatun Qurani sai gashi ya farfado ya tashi fes yana zare Ido,tare da rike kansa dake Sara masa,Allah Sarki duniya Salma bata da gata ita tuntuni takeyi babu wanda yaje da niyyar yi mata addua ta samu sauki Amma ga Na'im me gata yan Uwa duk sun rude anyi masa yaji sauki,
Na'im ya dan jima yana hutawa sannan ya mike ya murda handle din Salma gam gam a rufe,ya buga bugun duniya taki budewa yanzu ba chines take ba wani gurnani takeyi wanda nan take da Mummy,Aisha,Hunaif suka zura da gudu dakunansu tare da danna key su boye ciki wai tsoro,Irfan da Na'im ne kadai ke kokarin budewa,Spear keys Irfan ya kwaso suka dinga gwadawa har suka samu na kofar Salma suka bude,Allah Sarki Duk taji rauni a hannaye da kafafunta wajen ya kwailaye waje waje duk suna fitar da jini,tana kasan tiles gefen goshinta ya fashe sosai jini na zuba,harshenta ma ya fashe bakinta jini sosai,

Tausayinta ya kama Irfan da Na'im sai lokacin su Mummy suka dawo suka ga yanda Salma ta koma sai da suka firgita ta basu tausayi matuka,nan ma haka Mummy tace to mu hadu muyi mata yanda mukayiwa Na'im haka suka rufar mata har Na'im sannan Allah yasa bacci ya dauketa ta samu lfy,Alluran Na'im yayi mata sannan Masu aiki suka gyara bedroom din fes da gidan gaba daya,Irfan Da Na'im kowannensu ya wuce wurin aiki,Mummy ma ta tafi wajen Dada ita da Aisha,Salma kadai ke bacci cikin gidan sai ma'aikata da matakan tsaro ko ina.
Abuwa me aiki ce ke yawan leka Salma tana duba lafiyarta yayin da Nurse tazo tayi mata dressing ciwon da tajiwa kanta Doctor Me Imani ne ya turota.

Na'im sam kasa aikin yayi yau kuma yana Embassy sharp sharp yayi abinda zai iya 2pm ya dawo gida,bedroom nasa ya shiga wanka yayi ya fito cikin Jallabiya fara me shegen kyau kamar balarabe haka ya fito kamshinsa na watsuwa, masu aiki ya tambaya ko Salma taci abinci?,suka ce ai bata tashi ba ma,
A hankali ya murda kofarta ya shiga ciki da Sallama, karar ruwa yaji a toilet kuma bata saman Bed din alamar wanka takeyi ta tashi,Kwanciya yayi sosai saman Bed din,minti kadan sai gata ta fito sanye da Hijab kato har kasa bata daura komai ba sai hijab ne a jikinta,ko kallonsa bata yi ba ta dauki Bodycream dinta a Cikin hijab ta shafa abinta yana kallonta yana dauke kai kamar munafuki.
Chapter 12 · 0% Book details